20

11 2 0
                                    

BABBAN GIDA

20

Kowa hankalin shi ya koma kofar parlour,zaro ido sukayi.
Nasir ne yake shigo wa da murmushi a fuskar shi,yasa wani gezna fari da hula se fara'a yake.ahankali ya taka har wurin alhaji ya zauna.
Alhaji murmushi yayi sannan aka cigaba da ɗaurin aure.

Majid ne ya shigo da gudu side nasu Anam yana cewa"yaya Nasir ya dawo!!".
Duk tashi sukayi suna mamaki.
Mira kam fashe wa da kuka tayi tana cewa"na shiga uku shikenan yau zan mutu". rarrashinta suka fara amma taki shiru.haka dai suka hakura suka barta.
Chan sumayya ta shigo tana cewa"yanzu aka ɗaura".
Kowa se murna yake banda mira.anam tana zaune a kusa da ita tana kallon ta.
Sallama suka ji se suka amsa.
Su Walid ne da Yasir da Nasir da sauran.
Kowa tashi yayi suka gaisa.
Isa yace"ya kamata kowa ya tsaya kusa da matar shi a ɗauka hoto".
Nasir murmushi yayi yace"gaskiya kam".
Kusa da mira yaje wanda tana ganin shi ta kara rikice wa,baya ta koma se ya riƙe hannun ta yayi murmushi se  yaja ta  kusa dashi yace"smile".mira ta kasa komai har jikin ta karkarwa yake dan tsoro.
Haka aka ɗauke su hoto se su Walid da Raisa suka ɗauka se Yasir da Isha.
Da suka gama se suka fita.
Mira zama tayi hawaye yana zuba a idonta.
Khairat ce tace"haba mira baki ga kaman ya fara son ki bane".
Mira tace"wallahi da gangan yake yi".
Anam sauke nunfashi tayi tace"mira ba abinda ze Miki ki kwantar da hankalin ki".
Mira da karfi tace"ku Dena ce min na kwantar da hankali na bayan kunsan duk karya kuke yi dan nayi shiru!!".
Shiru ne ya biyo baya wasu suka fita wasu kuma suka shiga ɗaki.

Haka dai lokaci yayi ta tafiya har sukayi sallar magriba aka fara shirin kai amare gidan su.
Aka kai su side na Alhaji yayi musu nasiha me shiga jiki sosai sannan sukayi sallama da iyayensu.mira kam dakyar ta sake ummi se kuka take wai ita bazata tafi ba.
Haka dai suka shiga mota aka wuce da kowa side nashi.

Side na Isha komai brown da milk colour,side na Raisa kuma komai green da fari ne se side na mira kuma komai light brown ne.
Anam side na Raisa suka je aka ajiye ta.sannan se taje side na mira inda su hamra da hidaya suke ta rarrashin mira.
Anam zama tayi kusa dasu tace"ku barta bazatayi shiru ba".
Hamra tace"hmm mira kam se a hankali,haka zakiyi ta Mishi kuka".
Ai kuwa mira kara sautin kukan tayi.anam abun ma dariya ya bata se ta tashi tace"mira hakuri zakiyi yaya Nasir dai yanzu mijin kine ko kina so ko bakya so".
Tana faɗan haka ta fita ta wuce side na Jamila.bata samu Jamila ba se Nasir da harun dake zaune a parlour suna nishadi.ai tana ganin su ta rufe kofar da wuri ta bar wurin.

Direct side nasu taje tayi wanka sannan tasa kayan bacci ta fito parlour ta kunna tv tana kallo.chan se ga salis ya shigo da sallama,da sauri tasa hijabin da daman ta fito dashi daga ɗaki.
Shiga yayi se tayi murmushi tace"yaya salis yau ban ganka ba".
Salis yace"ai Ni aka bari da aiki shesa".
Anam tace"ayyah sannu ya gajiya?".
Salis yace"alhamdullilah,ina baby ne?".
Anam tace"suna side na Isha".
Murmushi yayi ya fita.
Kwanciya tayi ta cigaba da kallo.chan se munal ta shigo tana cewa"Anam mira tana neman ki wai kije da wuri".
Anam da sauri ta tashi ta fita.

Direct side na mira taje.ta same ta tana kuka haryanzu.
Anam tsaki taja tace"ke wai me haka ne,naɗau wani abu ne ya same ki".
Mira tace"Anam dan Allah karki tafi ki barni yaya Nasir ze kashe Ni".
Anam sauke nunfashi tayi tace"mira ba abinda ze Miki inshallah".
Mira tace"ki kwana anan".
Anam ɓata fuska tayi tace"ba zeyu na kwana anan ba kema kin sani".
Mira riƙe hannun Anam tayi tace"dan Allah Anam ki rufa min asiri wallahi yaya ze kashe Ni".
Anam zatayi magana se ga hamra ta shigo tana cewa"gashi ango ya zo".
Mira rikice wa tayi tana ƙara damƙe hannun Anam.
Anam tsaya wa tayi tana jira su shigo.
Se ga su Nasir da su harun sun shigo.
Anam duk da tsoron Nasir da take amma se taje gaban shi tace"yaya Nasir ga amanan mira dan Allah karka mata komai".
Nasir murmushi yayi yaje wurin mira ze zauna se ta matsa, murmushi ya kara yi ya zauna yace"se gobe da safen ku".
Su harun dariya sukayi banda Anam data ɓata fuska tana kallon shi.
Abdul yace"toh ango a kula da amarya".
Nasir murmushi yayi ya kalle mira dake a tsorace.
Fita suka fara yi se suka ga Anam tana tsaye,Abdul ne yaja hannun ta suka fita.

Babban gidaWhere stories live. Discover now