BABBAN GIDA
8
"Mira ta gudu!!!".zaro ido Farida da Anam sukayi suka tashi sauran ma suka fito daga ɗaki kowa ya rikice.
Hamra tace"alisha how sure are you that mira ta gudu?".
Alisha dake tagumi tace"ina zaune a side na umma mira ta kirani a waya tace min wai ita ta bar babban gida ta tafi da saurayin ta".
Munal tace"innalilahi wa innailaihi raji un".
Tsaki hidaya tayi tace"amma mira ba ta da hankali yanzu me zamu faɗa wa Alhaji?".
Shiru ne ya biyo baya kafin chan Fatma tace
"Gaskiya ma na".
Halisa tace"kunsan fa akwai matsala".
Anam tashi wa tayi tace"mira tana da wayo nasan bazata gudu ba in bata shirya ba kuzo muje mu faɗa wa Alhaji".Tashi wa dukka sukayi direct side na Alhaji suka je,suka samu kalil da Alhaji suna magana.
Kallon kallo suka fara yi wa juna ba wanda yake so ya faɗa.
Anam ce ta daure tace
"Alhaji daman mun zo mu faɗa maka wani abu ne".
Hankalin shi baya kansu fuskar shi duk damuwa.
Anam zuwa tayi kusa dashi ahankali tace"Alhaji kaima ka sani ne?".
Gwaɗa kai yayi se ta zauna tace
"ka samo ta ne?".
Kalil ne yace"tambayoyin ki yayi yawa ki barmu muyi abun gaban mu".
Shiru tayi se Alhaji yace
"Zamu same ta amma tabar ƙasan".
Zaro ido sukayi sannan Anam ta tashi ta fita sauran ma suka bita a baya.
Sanda suka fita Anam tace
"Daman na sani ai mira bazata tsaya a inda za'a same ta da wuri ba".
Fatma tace"in Alhaji ya same ta kam ta shiga uku"."ai ita da kallon waje kuma se a mafarki".junayya ta faɗa tana barin wurin.
Fiddat tace"wallahi yana samo ta aure ze mata".
Zasu tafi suka ga ummi duk damuwa a fuskar ta tana zuwa bata ma tsaya a wurin su ba ta wuce ciki.
Farida ta bita da kallo tana cewa"ayyah ummi yanzu se ayi blaming nata bayan bata da laifi mira ce bata da hankali".Haka dai gudun mira ya zagaya gidan kowa yana cikin damuwa.
Washe gari aka haɗa family meeting inda kowa ya haɗu a parlour na Alhaji.
Alhaji ne ya gyara murya yace"toh mira dai tana Dubai kuma na tura a ɗauko ta".duk suka ji kwanciyar hankali tun Bama ummi ba da ta kasa bacci jiya ba dan tunanin er ta.
Wayar kalil ya fara ringing ya tashi ya fita bayan minti kaɗan ya dawo da damuwa a fuskar shi yace
"Alhaji sun bar Dubai amma za'a cigaba da tracking nasu".
Shiru ne ya biyo baya chan Alhaji yace"na sallame kowa".
Duk suka tashi da sanyin jiki suka fita.BAYAN SATI DAYA
Su Farida da Ammi da mommy sun tafi sayayya a Dubai.Yau su aunty fatee sun kawo wa babban gida ziyara.
Suna zaune a parlour babba na gidan.
"Yaya salis ka bani abu na bana so".
Anam ta faɗa tana tura baki.
Murmushi salis yayi yace"bakin ki zeyi dogo ai".
Hararar wasa tayi mishi sannan tace
"Toh ai baki nane ba naka ba".
"Oho dai bazan ba ki ba".
Salis ya faɗa yana sa diary nata a aljuhun shi.murguɗa baki tayi ta tashi zata tafi ya riƙe hannun ta yace
"Dawo ki zauna ga abunki kafin yanzu kisa nayi mafarki dake".
Sake hannun ta yayi se ta zauna ya mika mata diary ɗin.
Baby dake kallon su tace"yaya salis kaidai akwai son tsokanan Anam wallahi".
Murmushi yayi se Anam tace"gaskiya kam ki faɗa wa yayan ki nima na ƙware a tsokana wallahi".dariya sukayi se ayban yace
"Gaskiya kam salis kayi hankali dan fa kana tsokanan Sarkin tsokana ne".
Anam tayi murmushi tace
"Yawwa yaya ka faɗa Mishi kam".sukayi dariya daidai lokacin muffik ya shigo ya wuce wurin Alhaji ya zauna sannan yace"mira tana Egypt".kowa yasha mamaki dan mira kullum chanja ƙasa take yi ana sanin inda take se ta kara chanja wani.Alhaji yace"ka tura su Egypt ɗin kuma su tabbatar sun same ta da ɗan iskan saurayin nata".
Muffik tashi yayi ya fita sannan kowa ya koma harkar shi.Kauthar ne tace"gaskiya mira batayi tunani me kyau ba".
Junayya tace"hmm ai kuwa,da ma ita kaɗai ta tafi ne yafi amma se tabi saurayi".
Jamila dake kwance tace"hmm bakusan me soyayya yake sa mutum bane shesa kuke faɗan haka".
Baby tace"kai Jamila ko ma mene ke da mira dai naku soyayyar rashin hankali ne".
Mama ne tace"ya isa haka".
Shiru sukayi sannan Anam ta juya ta kalle salis dake danna waya ta kobce wayar tana cewa
"Yaya salis tunda bani da waya ai kaima se ka hakura dashi".
Salis murmushi yayi yace"haba Anam kiyi hakuri dai ki bani nawa ke kuma ki rungume ƙaddara ".
Tura baki tayi shi kuma yayi dariya se ta mika mishi wayar dan ana kiran shi, karɓa yayi sannan ya fita daga parlour.suka cigaba da hira har su aunty fatee suka tafi gidan su sannan suma suka wuce side nasu.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.