BABBAN GIDA
12
Kneel down and apologize".
A zuciyar ta tace tabɗijam ai gwanda ka kashe Ni,a fili kuma tace
"Yaya harun ai ba se nayi kneeling ba zan iya bada hakuri duk da banyi laifi bama".
Nasir ne ya tashi yayi mata wani azabebben marin da yasa ta faɗi bakin ta yayi jini.
Tsuguna wa yayi ahankali yanda ita kaɗai zata ji yace"na gudun ɗazu ne wannan".
Harun murmushi yake Anam kuma hawaye ne ke zuba a idonta har hannun shi ya kwanta a fuskar ta abinka da jan fata.
Nasir ya tashi sannan yace"ba kiji me aka ce Miki bane?".
Anam ba karamin nadaman zama er gidan Jaffa take yi ba amma ya ta iya.Ahankali tace"kuyi hakuri".
Muffik gwaɗa kai yayi.
Ahankali ta tashi ta fita ta koma side nasu tana ta kuka har magriba yayi sannan tayi sallah tayi wanka se ta wuce side na Farida inda suna ta hirar su suna farin ciki.Zama tayi a kusa da alisha.
Alisha kallon ta tayi tace"ina kika je ne tunɗazu ban ganki ba?".
Anam jiki a sanyaye tace"ina bacci ne".
Alisha ta gwaɗa kai su Raisa kuwa hirar su suke.
Raisa tace"amma Alhaji bai mana adalci ba ai indai ze sa ranan aure na to ya kamata a haɗa da nasu Anam ma".
Farida tace"gaskiya kam tunda duk kuna part 1 ba".
Fatma ne taja tsaki tace"ke da aka ce wa Alhaji iskanci kike yi shesa ai ya haɗa ki aure da wuri".
Raisa ma hararar ta tayi tace"ai more rayuwa ta nake kafin na shiga daga ciki".
Khairat tace"ai yanzu zaki more me kyau kuma da yaya Walid".
Hamra tace"hmm ai yaya Walid ma yana more rayuwar shi se ku more tare".
Raisa tace"Allah ya soni muna shiri da yaya Walid sosai da na shiga uku".
Anam wani tsaki taja sannan tace
"Ki faɗa wa wanda bai sani ba,ai gaya Miki bamu san iskancin da kuke yi tare da yaya Walid ɗin bane".
Wasu sunyi mamaki wasu kuma basu yiba.
Raisa ba kunya tace"so what Dan kun sani ai daman ban taɓa ɓoye wa ba".
Alisha tace"shi Alhaji yana ganin kamar munfi kowa tarbiyya bai san me akeyi a bayan idonshi ba".
Fatma tace"wasu ba,mudai muna da tarbiyya".
Haka dai suka fara musu sosai ya koma chachan baki Anam da Farida kuwa kallon su suke kamar tv.Mustapha ne ya shigo yana cewa"lafiya kuna ta surutu haka?".
Farida ce tace"musu suke yi fa".
Mustapha yace"kuyi hakuri ku Dena kunji?".
Gwaɗa kai sukayi se ya kira Farida suka fita.
Anam tace"hmm Kuna da aiki".
Tashi tayi ta fita direct side nasu ta wuce ta ƙura wa tv ido.
Umma ce ta shigo tana cewa"Anam tunɗazu ina ta neman ki,kizo ki rakani side na Alhaji".
Anam murmushi tayi ta tashi suka fita da umma suna hira har suka je side na Alhaji.Zama sukayi suna jiran shi dan ba kowa a parlour.
Anam tace"ko ya tafi masallaci ne?".
Umma tace"shi yace nazo bayan magriba".
Chan se ga Alhaji ya shigo ya zauna suka gaisa,ya kalle Anam sannan yace"Anam jeki zamuyi magana na maman ki".
Tura baki tayi ta tashi ta fita.
Tana hanyar koma wa side nasu ta kalle Nasir da Walid suna magana da sauri ta ɓuya a gefe dan karsu ganta.Sanda ta jira suka bar wurin sannan ta fito.tana fita taga Nasir a gaban ta yana murmushi.zata gudu ya riƙe hannun ta yana cewa"kin ɗau ban gan ki bane?".
Shiru tayi tana tuno marin da yamata ɗazu dan taɗau alwashin se ta rama.
Jan hannun ta ta fara yi shi kuwa ya kara damƙe hannun ta har ya fara mata zafi.
Kaman tayi kuka tace"yaya akwai zafi ka sake Ni".
Murmushi yayi yace"chizon da kikamin ɗazu ma akwai zafi".
Ahankali tace"kayi hakuri bazan kara ba".
Janta yayi suka fara tafiya tana kokarin ya sake ta se kawai ga mommy tazo wuce wa ta kalle su se ta tsaya tace"Nasir ya ka damke hannun ta haka?".
Nasir ya sake hannun Anam yace"laifi tamin shesa".
Mommy murmushi tayi tace"ayi hakuri babban yaya kasan Anam akwai rashin ji".
Shima murmushi yayi ya kalle Anam yace"toh shikenan je ki".
Kamar daman jira take yi yace ta tafi da sauri ta bar wurin ta wuce side nasu ta buɗe fridge ta ɗauke slice na cake taci dan yunwa take ji kuma tana tsoro karta fita su haɗu da Nasir a hanya.Bayan ta gama tayi sallah sannan ta kwanta.Yau tun safe Anam take jinta garau ba abinda yake damun ta, tayi wanka suka wuce dining aka fara cin abinci.
Abu ne ya fara cewa
"Alhaji haryanzu ba maganan kalil da mura ne?".
Alhaji kallon abu yayi sannan yace
"wayan kalil ya Dena shiga gaba ɗaya amma zan tura wani ko gobe ya duba me yake faruwa".
Daddy yace"gaskiya kam in bai same ta ba kawai ya dawo dan sun kusan tafiya".
Alhaji yace"ehh ya kamata ya dawo ya shirya".
Anam tace"ba se ya dawo ba ai kawai ya wuce daga chan".
Ammi ne tace"haba Anam ai gwanda ya dawo ya shirya tukunnan".
Ta gwaɗa kai tana wani abu da fuskar ta,bayan sun gama cin abinci Kowa ya wuce side nashi.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.