29

14 2 0
                                    

BABBAN GIDA

29


"Anam mijin ki yana kiran ki".

Anam sanda zuciyan ta yayi dum amma se ta tashi ta tambaya"a ina yake?".

"Yana parlourn shi".munal ta faɗa tana zama.

"Yana da parlour ne?".Anam ta tambaya da mamaki.

Zaro ido sukayi suna mata kallon mamaki.

"Haba ke kuma ai daman ko wani side parlour uku ne".Isha ta faɗa tana dariya.

"Ya rabb wallahi ban sani ba".ta faɗa tana fita daga ɗakin.a hall way ɗin akwai wani kofa shi kuma tasan balcony ni ne so bata je ba.

Wani kofa ta gani wanda yake facing  kofan ɗakin ta.
Ahankali ta buɗe da sallama.

Parlourn ba wani babba bane Abba yana da kyau sosai, komai na parlourn fari ne se wani paint me kyau ta bayan kujerar baƙi,se tv stand shima black da tv se kuma fridge ta gefe.

Zaune yake yana danna laptop nashi hankalin shi ma bayan kanta.
Ahankali taje ta zauna a kujeran dake facing nashi sannan tace"yaya ganinan".

"Mesa kika fita jiya?".ya tambaye ta idonshi na kan laptop nashi.

"Babu".ta faɗa tana wasa da hannun ta.

Wani kallon da yayi mata ne yasata amsawa"ina jin tso-ro ne".ta faɗa zuciyan ta yana buga wa sosai.

"Tsoro".ya faɗa yana kallon laptop nashi.

Shiru tayi shima bai kara magana ba.sun kusan minti biyar a haka.

Data gaji ta tashi zata tafi taji yana cewa
"Na baki izinin tafiya ne".

Da sauri ta zauna tana cewa"ohh".abun nashi ya fara ƙular da ita duk da tana tsoron shi amma ai baze hana ta raina shi kaɗan ba.

Shi kuwa ko kula ta bayyi ba ya cigaba da abinda yake yi.

Da taga dagaske fa ba magana zeyi ba tace"yaya ina da abun yi".

Shiru yayi,abun ya bata haushi ba kaɗan ba.

"Malam dak--". knocking na kofar da aka fara yi ne yasa ta katse maganar ta kuma ta gode wa Allah dan da ta faɗa yau se kalil ya kashe ta.

"Come in".kalil ya faɗa.

Khairat ce ta buɗe kofan tana cewa"yaya bari muyi borrowing nata na minti kaɗan".

"Ok".shine abinda ya faɗa.

Anam tashi tayi tana yamutsa fuska sannan suka fita da Khairat.

"Allah yayi Miki albarka khairat".Anam ta faɗa suna kan shiga parlour.

Dariya tayi tace"Ameen ya Allah".

"Ya rabb nikam gaskiya barin gidan nan zan yi".hamra ta faɗa tana wuce wa ɗakin anam.

Dariya sukayi sannan suka fita waje wurin su mazan,hira suka zauna suna tayi.

Se dare kowa ya koma side nashi.

Nasir da mira.

"Ke kawo shi da wuri".Nasir ya faɗa wa mira dake riƙe da Hisham yana kuka.

Miƙa Mishi tayi sannan ya fara rarrashin shi.mira murmushi tayi tana ganin yanda Nasir yake son Hisham,tun ranan data haihu Nasir yake nuna kauna sosai wa yaron shi.

"Me kin tsaya anan kije ki kawo wani kayan shi".

"Toh yaya bari na ɗauko".ta faɗa tana wuce wa upstairs.

Malik da sadiya.

"Sady zo mana".Malik ya faɗa yana kwance akan gadon shi.

Sadiya dake closet nashi tana gyaran kayan shi ne tace"yaya one minute ina zuwa".

Babban gidaWhere stories live. Discover now