9

17 2 0
                                    

BABBAN GIDA

9

"Adda ja--mila ta faɗi a to--ilet,ji-- jini a jikin ta".
Duka a tsorace suka tashi da sauri suka wuce side nasu anam.suna shiga toilet ɗin Jamila a sume da jini a ƙafan ta,da sauri su mommy suka ɗan wanke jikin ta suka canja mata kaya sannan aka wuce asibiti da ita.

Duk suna asibiti wasu a tsaye wasu a zauna sunyi tagumi.
Mami ne da kawu suka shigo ,mami tana kuka tana ihun me ya same jamila.dakyar suka rarrashe ta sannan tayi shiru.
Doctor lawan ne ya fito duk suka tashi se ya fara cewa
"Alhamdullilah bata ji ciwo ba amma cikin ta ya zube".
Salati suka fara yi.haka dai likita ya basu hakuri sannan yace zasu iya shiga ɗakin.
Da sanyin jiki suka shiga suka samu haryanzu bata farka ba.

Mami ta zauna kusa da ita tana cewa"yanzu me zamu ce wa Jamila, cikin ta ya zube ko me?".
Ummi dafa kafaɗan mami tayi tace"mami hakuri za'ayi a faɗa mata".
Mami shiru tayi.
Haka dai lokaci ya tafi Alhaji yace su tafi gida abar mami da Ammi su zauna da Jamila.
Haka kuwa akayi suka koma gida kowa jiki a sanyaye suka kwanta bacci.

Da safe kuwa suna breakfast suka wuce asibiti a nan suka samu Jamila ta farka se kuka take yi wai a dawo mata da cikin ta.doctor lawan ya mata alluran bacci tukunnan suka samu kwanciyar hankali.
Bayan kwana biyu aka sallame ta mami ma ta dawo babban gida dan ta kula da jamila.kawai se Alhaji yace su dawo gaba ɗaya kuma haka akayi suka dawo da kawu aka basu wani side ɗin dan akwai daya wa wanda ba kowa.alhaji ya gina wani kamar estate a cikin babban gida wanda duk wanda zeyi aure a wurin ze zauna.

Duk suna zaune a parlour suka ji sallamar harun.suka gaisa sannan ya zauna.
Harun ya kalle Jamila dake kwance a cinyar mami yace"Jamila ya jiki?".
Jamila bata juya ta ma kalle shi ba tace"da sauki alhamdullilah".
Harun ya kalle Alhaji yace
"Alhaji nazo ne daman akan maganan auren mu da Jamila,ka ga daman dan cikin ta ne aka ɗaga yanzu tunda ba cikin inaso a haɗa auren rana ɗaya da na Mustapha".
Jamila tashi tayi ta zauna ta Mishi wani kallo sannan tace
"Kai yaya harun baka da tausayi ne yaushe ma na warware da zaka ce ayi auren".
Kawu yayi mata wani kallo yace"Jamila ina tarbiyyar ki ana magana da Alhaji kina sa baki".
Mami zatayi magana Alhaji ya dakatar da ita da hannu sannan ya kalle harun yace
"Wannan ma ai yayi kyau daman nima tunanin da nake yi kenan,tunda ka faɗa toh ai shikenan se a haɗa da nasu Farida".
Duk kallon mamaki suka wa Alhaji balle ma Jamila wanda baƙin cikin harun ya ishe ta.
Alhaji yace"yawwa kuma mira tana dawowa zan mata aure dan naga rashin auren ne yake sata wannan iskan cin ke kuma hamra, haidar ya nema Miki wani makaranta saura kuma wannan ma ki musu raini". gwaɗa kai hamra tayi.
Ummi kuwa baƙin cikin mira ne yake matukar damin ta.
Harun yace"bana so ayi komai a bikin nan se ɗaurin aure".
Anam zatayi magana Ammi ta riga ta cewa"haba dai harun mesa baka so ayi komai?".
Harun murmushi yayi se yace"Ammi ina ganin ai kawai ɓata lokaci ne amma tunda kuna so se ayi walima".
Jamila tashi tayi ta fita daga parlour se Anam ta bita.

"Jamila Jamila ki jira Ni!!".Anam ta faɗa tana bin Jamila a baya,sanda tabar compound na Alhaji kafin ta tsaya ta juya ta kalle Anam kamar zata yi kuka tace
"mesa yaya harun yake min haka tun kafin muyi aure ya fara controlling na rayuwa na me ze faru kuma bayan munyi aure".
Anam dafa kafaɗan Jamila tayi tace
"Karki damu kinji komai ze wuce".
Muryar harun sukaji yana cewa
"Jamila zo nan".
Anam ta juya ta kalle shi sannan tace"bazata zo ba ai ko kawu dai daya haife ta baze ce tazo nan ba balle kai da ko ɗaura auren ku ba'ayi ba".
Harun yayi mata wani kallo sannan yace"ahhh haka ne Anam kin girma,har Ni zaki tsaya kina faɗa wa maganganun nan ko kin manta nine harun?".
Yana gama faɗan haka ya matso kusa da ita se ta ja baya ya kara matsa wa se ta ɗan tura shi sannan a fusace tace
"Kai da yaya Nasir ma bansan wa ye gwanda ba duk halin ku ɗaya shesa ai Kuka fi shiri ba abinda kuka iya se mugunta da baƙin hali kuma wallahi Allah ze saka mana".
Murmushin gefen baki yayi sannan yace
"Ai ba laifin mu bane muma gado muka yi".
Yana faɗan haka yaja hannun Jamila suka tafi Anam kuwa tana tsaye a wurin kamar wanda ta daskare.
Fiddat ce tazo ta taɓata, Anam sannan ta dawo hankalin ta.
Fiddat ta taɓe baki tace"lafiya dai ko?".Anam gwaɗa kai tayi sannan ta wuce side nasu ta zauna a parlour tayi tagumi tana tunanin abinda harun ya faɗa mata duk da tasan gaskiya ya faɗa amma abin yana ɗan damin ta.

Babban gidaWhere stories live. Discover now