37

11 1 0
                                    

BABBAN GIDA




37

"Alhaji Isma'il ya rasu alhaji kuma ya faɗi,yanzu yana asibiti".

Zaro ido sukayi da sauri duk suka fita side na Alhaji inda suka samu kaku tana ta kuka.

"Kaku addu'a zaki mishi".Alisha ta faɗa tana rungumar kaku.

"Ina suke?".Anam ta tambaya hawaye na cika a idonta.

"Suna asibiti an je ɗauko gawan alhaji Isma'il".munal ta faɗa tana goge hawayen ta.

"Muje".Anam ta faɗa tana share hawayen ta dake suke zuba.

"Anam yanzu zasu dawo".kaku ta faɗa tana riƙe hannun Anam.

"Alhaji fa?".Anam ta tambaya.

"Shima baze daɗe ba".kaku ta faɗa tana share hawayen ta.

"Mesa ya fa ɗi?". Alisha ta tambaya tana kallon kaku.

"Kawai shock ne,ku zauna yanzu zasu dawo".kaku ta faɗa.

Zama sukayi duk hankalin su a tashe.

Se bayan magriba aka dawo da gawan alhaji Isma'il.

Kowa se kuka, gaba ɗaya babban gida ya rikice sun zama abun tausayi bare ma aunty Maryam da Amina.

                           ****
"Yaya ya jikin alhaji?".Anam ta tambaya tana bin bayan shi suna tafiya da Malik a filin babban gida.

Ko kula ta bayyi ba suka wuce.
Haushi taji amma se ta wuce har zata bishi se taji Muryar Raisa.

"Anam kin kalla Akira?".ta faɗa tana matso wa kusa da ita.

"A'a ban ganta ba,fita tayi ne?".Anam ta tambaya da damuwa a fuskar ta.

"Tana wasa ne fa se kuma bamu ganta ba".Raisa ta faɗa tana dube dube.

"Yawwa gatanan".Raisa ta faɗa tana wuce wa wurin ammi dake rike da Akira.

Anam side nata ta wuce ta ɗauko keyn mota sannan ta fita.

Garage taje ta same Nasir da harun suna jingine a motan mansur Lexus Rx silver.

"Sannun ku ya hakuri".Anam ta faɗa tana zuwa kusa dasu.

"Alhamdullilah hakuri se ma'aiki".suka haɗa baki.

"Allah yajiƙan shi".Anam ta faɗa tana barin wurin.

"Ina zaki je?".Nasir ya tambaye ta.

"Zanje asibiti ne".ta faɗa tana Allah Allah su barta.

"Ki koma gobe za'a sallame shi".harun ya faɗa yana ɗaga wayar shi dan ana kiran shi.

"Yaya zanje na duba shi ne".ta faɗa da fuskan tausayi.

"Ki koma gida yanzun nan".Nasir ya faɗa yana mata wani kallo.

Koma wa tayi cikin gida tana ta tura baki har ta iso side na umma.

Tana shiga ta haɗu da mami a kofa tana kan fita.

"Mami ina wuni".Anam ta faɗa tana wuce wa.

"Anam ya na gan ki haka duk kin lalace".mami ta faɗa tana riƙo hannun ta.

"Hmm mami kedai bari wallahi abubuwa dayawa yana damina".Anam ta faɗa tana rungumar mami.

"Ki kwantar da hankalin ki inshallah komai ze wuce kuma kisa a ranki zakiyi farin ciki nan gaba wanda ba wanda ya taɓa irin shi".mami ta faɗa tana shafa kanta.

"Ameen mami naji daɗin abinda kika faɗa".Anam ta faɗa tana sake ta.

"An zo wurin umma ne".mami tayi murmushi.

Babban gidaWhere stories live. Discover now