14

17 2 0
                                    

BABBAN GIDA

14

"Alhaji Ni Anam nake so na aura".
Anam wani tsinke wa gaban ta yayi.mira kam kuka ta fara.
Alhaji da ɓacin rai yace"inna faɗa abu ya zauna kenan ba me chanja wa se Allah".
Nasir tashi yayi yace"ummi ki faɗa wa Alhaji inna aure erki toh wallahi se kunyi  nadaman aura min ita da kuka yi dan se na lalata mata rayuwa".
Ummi kamar tayi kuka tace"dan Allah Alhaji a ƙara duba wannan lamarin tunda yace Anam yake so".
Anam tace"Ni wallahi bana son shi".
Alhaji a fusace yace"in kaga dama ka kashe ta amma ita zaka aura ko kana so ko baka so".
Murmushi Nasir yayi sannan ya fita.

Mira a cikin kuka tace"wallahi Alhaji kasan yaya Nasir inya faɗa abu to se yayi,dan Allah karka aura min shi".
Alhaji tashi yayi yace"na sallame kowa".
Mira kuka take yi haka suka fitar da ita tana ta ihu a waje.
Kalil ne da tsawa yace"ke ki mana shiru, daga kanki ne aka fara auren haɗi ko me!!!".
Tsit tayi tana ta sheshsheka.
Mazan suka bar wurin Anam tazo kusa da ita tace"kiyi hakuri inshallah ba abinda ze faru".mira wani kallo ta mata sannan tace
"Kinfi kowa sanin halin yaya Nasir yanzu kuma kina ce min ba abinda ze faru".tana faɗan haka ta wuce side nasu sauran ma suka bita,Anam kuwa tsaya wa tayi tana tunanin halin da mira zata shiga in ta aure Nasir.

Koma wa tayi side na Alhaji ta wuce ɗakin shi ta same shi a zaune.
Itama Zama tayi a kusa dashi ahankali tace"Alhaji me sa ka haɗa auren mira da yaya Nasir?".
Alhaji yace"ke ma kina so ki ɓata min rai ne?".
Karkaɗa kai tayi tace"Alhaji kawai dai naga duk basu son haɗin ne shesa kuma kaji abinda yaya Nasir ya faɗa".
Alhaji yace"haka kowa zeyi hakuri sauran ma ba son junan su suke ba".
Anam shiru tayi tana kallon Alhaji shi kuwa tashi yayi yace
"Bari zan fita".
Yana faɗan haka ya fita daga ɗakin.
Sauke nunfashi tayi ta kwanta tana tunani iri iri har bacci ya ɗauke ta.

"Anam ki tashi yaya Nasir ze kashe mira!!!".
Halisa ta faɗa a rikice tana buga Anam.
Anam a firgice ta tashi tace"me ya faru?".
Halisa a rikice tace"zuwa side namu yayi yana mira suka je ɗakin yaya ayban ya rufe kofar se dukan ta yake yi".
Anam da sauri ta tashi suka wuce side nasu Majid.
Kowa ya taru a kofa suna roƙan Nasir ya buɗe kofar amma yaki.
Anam da sauri taje wurin kofar tana cewa"yaya Nasir dan Allah karka ji mata ciwo ka buɗe kofan ba abinda ta maka".
Bai kula taba se saukan belt suke ji da ihun mira tana bada hakuri.
Kalil ne ya shigo yana ganin su yaje wurin a fusace ya ɓalle kofar se ya buɗe,ai kuwa mira ta daku jikin ta duk jini.
Da sauri kalil yaje ya chunkume rigar Nasir a fusace yace"mesa ka duke ta haka?".
Nasir murmushi yayi yace"dan in nuna mata mijin da zata aura mugune kuma zan iya kashe ta sannan in nuna wa Alhaji yayi kuskuren haɗa Ni da mira".
Kalil sake shi yayi mira kam har ta suma.
Da sauri muffik ya ɗaga ta suka wuce asibiti.

Alhaji Ismail yace Nasir ya koma gida dan ze iya kashe mira.su Anam kuwa sun zauna a waje kowa yayi tagumi.
Jamila ce ta fito daga side nasu ta je inda su Anam suke zaune.
Anam tana ganin ta ta tashi zata bar wurin Jamila ta riƙe hannun ta tana cewa"haba Anam dan kin ganni ne zaki tafi".
Anam jan hannun ta tayi tace"ba dole na tafi ba kin bari yaya harun yana ta dukan ki se kace jaka,ai in bakya rama wa ze raina ki".
Jamila tace"hmm Anam ba za ki gane bane,ai karfi na da yaya harun daban ne kuma ai shi miji nane ban isa na rama ba".
Anam tsaki taja tace"a wani littafi kika taɓa ji miji ya kamata ya duke matar shi?".
Jamila shiru tayi,hamra ce tace"Anam ya isa haka kinsan dai bazata iya rama wa ba kawai se de tayi ta hakuri".
Anam hararar hamra tayi tace"ai kuwa a haka ze chu ce ta".
Jamila shiru tayi ta zauna.
Sukai ta ta zama har suka gaji suka koma side nasu.

Se bayan sallar magriba aka dawo da mira muffik yace take ta kwanta.haka dai yau kowa yayi bacci jiki a mace.

BAYAN SATI DAYA
Yau su kalil zasu tafi,wasu suna farin ciki wasu kuma suna baƙin ciki.
Anam kam baki har kumatu se farin ciki take.
A kwanakin daya wuce hankalin ta kwance dan Nasir baya gidan sauran ma duk sun tafi gidan su kuma gobe suma zasu buɗe makaranta.

Babban gidaWhere stories live. Discover now