Chapter One

12.7K 531 51
                                    

Akwatina shida ne ke jere gaban wasu mata, suna kallon abubuwan da ke cikin su daya bayan daya. Kowacce cikin su tana tofa albarkacin bakin ta, nay abo ko kuma gates da habaici.

Wata mace fara, mai daure da bakar atamfa ta na zaune a gefen su kan karamar kujerar zama. Ba ta ce wa kowa komai ba, don ita kadai ta san halin da ta shiga a lokacin.

“Tubarkallah!” daya da ga cikin matan da a ke kira da Tambai ta furta a yayin da ta dago wata atamfa wadda da ganinta sabuwar yayi ce.

“Lallai yaro ya yi kokari sosai. Yalwaji ta yi sa’a.”

“Lallai kuwa.” Wata ma mai suna Larai ta amince. “Allah Ya sa gidan zaman ta ne. su ma ‘yan uwan ta na baya, Allah Ya ba su kamar na ta.”

Duka suka ce, “Amin.”

Bayan sun gama kallon kayan auren, sai Tambai ta kalli wacce ke zaune a gefen nan, ta ce, “Wai ni yaya batun Laminde ne kam, Dada? Har yanzu ban ji an ce komai ba. Ko auren ne ba ta samu ba tukunna?”

Dada, wadda asalin sunan ta Amina ce, ta samo lakanin ta ne dalilin yadda kannen ta ke kiranta da shi. Ita ce babba cikin ‘Ya ‘ya ashirin da Allah Ya bai wa mahaifanta, sannan “yar usulin garin Bauchi ce. Lakanin Dadan ya bi ta zuwa dangin mijin ta har ma da ‘ya’yan da ta haifa a cikin ta.

“Na ta lokacin bai yi ba. In maganar ta taso ma ai ku ne ma su fada a ji.”

Tambai ta ce, “Yo kun ji min Dada fa. Ke da kike uwar yara, meye nawa in ba bada shawara ba? Kuma ba lallai ne a dauka ba ma.”

“A matsayin ki na kanwar mahaifin yaran, ba su da uwar da ta wuce ki.”

“Hmm, a bar kaza dai cikin gashin ta. Sau nawa aka yi, sai an ci an cinye tukunna na ke samun sudi?”

Dada ta mike, “Wannan kuma ke ya shafa. Bari na ga ko abincin ya nuna, in ya so na sa a zubo muku.”

Har ta bar dakin, cikin matan nan babu wacce ta tsoma baki cikin maganar su. Kowa ya sani, tsakanin Dada da Tambai, ba kasafai a ke shiri ba. Su na dai kula juna ne don ya zama dole.

Dada dai ta san kara zaman ta a dakin zai kai su ga gutsiri-tsome, wanda kuma bas hi ne ke gabanta ba. Abin da ke gaban ta ya fi karfin ta, ko duk wani tunanin ta. Tun daren jiya ko runtsawa ta gagara yi, ta rasa wurin da za ta jefa kan ta.

Ta iske biyu daga cikin ‘ya’yan ta mata uku da suka rage ma ta a gida a cikin ‘ya’ya shida da Allah Ya ba su ita da mijin ta Malam Sabo. Da ganin ta suka zauna da kyau cikin natsuwa.

Ko kallon su ba ta iya yi, ta ce, “Sai ku fito ku duba abinci, don iyayen ku su na jin yunwa.”

Muryar ta fayau, babu farinciki a cikin ta ko nishadi, ko ma alamar ba su umurni, tamkar yadda idanun ta su ke. Daga nan ta koma wajen sauran matan ta zauna. Wa su ma a lokacin su ke zuwa ganin kayan, don haka ta yi kokarin dauke hankalinta ta mayar zuwa gare su.
Ba ta da ikon yin abin da ya fi hakan.

                               *              *                   *
Tun da asubar farko Asiya ta hura wuta a madafi, sannan ta dora ruwan dama koko. Bayan ta idar da sallar asuba ne ta dama kokon, sannan ta share tsakar gidan su tsaf.

A wannan rana ta na da abubuwa da dama a cikin kan ta, da ma cikin zuciyar ta. A wannan rana ta yanke aiwatar da hukuncin da ta yanke a zuciyar ta, cewar tilas sai ta fuskanci azzalumi, mayaudari kuma macuci.
A wannan rana ta yi alwashin kudirin kawo karshen komai, ko za ta iya warware tarkon da mahaifiyar su ta fada ciki.

Ta na aikin, ta na tunanin zaluncin maza. A sanin ta, mahaifin su bai san ya kula da su ba, don kawai su ‘ya’ya mata mahaifiyar su ta haife su. Bai san cin su ba, balle a ce magani ko sutura. Komai ya rataya a wuyan mahaifiyar su ne.

KudiriWhere stories live. Discover now