Nan take ya farfado daga kaduwar sa. Ta ya ya a ka yi ta san ya na wajen? Ya daure fuskar sa, ba bu alamar annuri ko kadan, ya ce, “Idan Asiya ki ka zo nema, ta na can gidan ku.”
Mariya ta yi murmushi, “Na san da haka, don na ga shigar ta gidan. Wajen ka na zo musamman.”
Ba tare da bata lokaci ba ta zauna. Ganin hakan ya sa Habu ya ficewa don ya ba su wuri.
“Ban tuna lokacin da na ba ki damar zama ba.”
Idan ta ji tsoro ko shakka to ba ta nuna ba. Ba ta kuma yi yunkurin mikewa ba. Ga alama da abin da ta zo da shi, wanda bai kasance alheri ba.
Ya na ganin hannun su Yafendo cikin wannan ziyara na ta dumu-dumu. Lallai akwai matsala. Babba ma kuwa.
“Me ya kawo ki?” Muryar sa sanyi kalau mai kaushi. Ko za ta fahimci sakon sa, na ta fita ta ba shi wuri. Bai san dalili ba, komai na Mariya ba ya tattare da alheri. Bayan haihuwar Amatullah da ta yi, zai iya cewa rayuwar hasara ta ke ciki.
“Zuwa kawai na yi don na nuna ma ka godiya ta, bisa rikon amana da ka yi wa diya ta Mansura. Hakika hakan ya tabo zuciya ta matuka.”
Bai kula ba, jin cewar ta canja wa Amatullah suna zuwa ga Mansura. Ba ya son ya nuna ma ta har yanzu ya damu da rashin ta, ya na kuma bukatar ta zauna a matsayin ‘yar sa. Ko ma yadda kowa a gidan sa ya shiga wani hali don rashin ta.
Mariya ta fadada murmushin ta, “Na gode ma ka kwarai da gaske. Allah Ya ma ka sakayya ma fi girma.
Wani takaici mai hade da kulliti suka tokare ma sa wuya. In ban da wannan lokacin, bai taba zama kusa da Mariya sosai ba. Ranar farkon ganin ta kafin auren ta da ma bayan haihuwar ta duk a takaice ne babu natsuwa.
“A tunanin ki don ke na yi? Ai ke da Khalid ba ku kai na yi abu don ku ba. Na rike Amatullah ne don Allah, don kuma dukkanin ku, a matsayin iyayen ta kun gaza.
Idan kuma godiya ki ke son yi, to wa Asiya ya dace ki yi godiya. Ita ce ta cancanci yabo, domin ta sadaukar da rayuwar ta wajen ganin tabon da Amatullah ta zo da shi duniya bai shafe ta ba. Sannan ba ta guje ma ta ba, alhali uwar da ta haife ta ta yi hakan.”
Tun bayan haduwar su ta farko ya saka ta a jerin wadan da ke da son zuciyar su. Ta tabbatar ma sa da hakan bisa amincewar auren mijin ta na farko da ta yi, ta kuma kara tabbatar ma sa a lokacin da suka neme ta ba su gan ta ba.
Sannan ta dawo daga baya, ba tare da godiya ko nadama ba ta bukaci diyar ta. An ba ta, me ya kawo ta wurin sa kuma?
Ga alama maganar sa ta soki Mariya. Ta turbune fuska, “Eh to, ai don kudi ta yi hakan. Ka na tsammani ba don kudin da ka ke da su ba za ta amince ne?”
Ta soke shi a zuciya da furucin ta, amma bai yadda ta gane a fuskar sa ba. Mariya ce. Komai ta yi ba zai ba shi mamaki ba.
Ya ce, “Ban tuna lokacin da na yi tayin kudi wa Asiya don ta aureni ko ta kula da Amatullah ba. Hasali ma ba ta juya wa diyar ki baya ba. Ta gwammace ta fuskanci fushin mahaifin ku don Amatullah ta samu haske a rayuwar ta. Amma don rashin adalci irin na ki, za ki zo nan wajen ki zarge ta kan abin da ya kamata a ce kin ji kunyar fadar sa.
Idan kuma na yi la’akari da yadda ki ka dauki rayuwar ki, kunyar ce aba ma fi tsada gare ki. Ina son ki san har a nade kasa, ungulu ba za ta rama gayyar zabuwa ba. Abin da Asiya ta yi mi ki, ba za ki taba rama ma ta ba.”
Mariya ta tashi ta nufe shi, ta na ya yake hakoran ta, “Mu bar zancen kanwata.” Ta zauna a kan kujerar da ke gefen sa. Bai motsa ba. Ta ci gaba da cewa, “Na zo ne mu yi magana ta fahimta tsakanin mu.”
Ba ya son yadda sautin muryar ta ke fita. “Tsakanina da ke babu wata magana. Idan akwai abin da ki ke son tattaunawa a kai, ki fada wa Asiya, in ya so sai ta fada min.”
YOU ARE READING
Kudiri
RomanceHausa story of love, commitment and sacrifice. Yusuf and Asiya belong to different classes with nothing in common. Well, except for humanity. An incident had occurred which brought them together. Will their shared sacrifice bring them happiness and...