Assalamu alaikum. Thank you for being with me so far. Your comments and votes get me going. I always wait for them to flow in. You guys are awesome👌👌. Keep them coming. Love and hugs😘😘
“Assalamu alaikum.”
Muhibbat ta yi sallama tare da shiga tsakar gidan su Asiya. Ta tsuguna ta gaida Dadan.
“Oh, ‘yar halak kin yi Ambato. Yanzu na ke shirin tura Laminde gidan ku ta kira min ke. Sai ga ki da kan ki ma.”Muhibbat tayi murmushi, “Ni ma tun jiya na ke son zuwa amma Allah bai yi ba sai yanzu.”
“Allah Sarki. Yaya Iya? Sauran mutanen gida lafiya?”
“Lafiya kalau Dada. Su na ce na gaishe ki.” Ta ja kujerar da ke gefen Dadar sannan ta zauna a kan ta, ta ci gaba da cewa, “Da ma tun jiya da dare mu ka yi waya da Maree, ta ce don Allah na gaishe ku, in kuma ce da ku ta na nan lafiya.”
Jin hakan ya fiddo Asiya daga cikin dakin su, wurin da ta shiga yin sallar la’asar. Tun kwanaki take yawan damun Muhibbat, kan ta yi waya don su gaisa da Mareen amma ba ta samu dama ba.
Dada ta yi murmushi mai fadi, “Allah Sarki. Dalilin kiran da zan miki ke nan. Da ma gani na yi tun da suka koma gidan sun a Bauchi, babu wanda ya je ya dubo su. Shine na ke shirin tura Laminde. Amma na san kin fi ta sanin wajen na ta. Ko za ki iya yi ma ta kwatancen?”
Asiya ta saki murmushin jin dadi. Tun bayan dawowar ta daga Bauchi, Dada ba ta yarda ta yi nesa da ita ba, musamman ma da ta ji sun koma Bauchi.
Komawar ta su ma ya kasance ba a sani ba a gidan su. Ta shi ne ya tashi, kamar yadda Mareen ta fada, cewa mahaifyar mijin ta ta bukaci ya mayar da ita can, don ta na son su zauna tare.
A ranar Maree ta samu watanni biyar ke nan da aure, sannan watan ta uku a Bauchin. Shi yasa ma Dada ta yi tanadin garin kuka, kubaiwa busasshiya, daddawa, manshanu galan guda da sauran wasu tarkacen da Asiya ba ta san kan su ba.
“Ai kuwa ni ma ina ta son na je Bauchin don karbar wasu kayyayakin da aka sayo min daga ta Habuja. Gobe ne amma tafiyar in Allah Ya kai mu.”
“Kin ga faduwa ta zo daidai da zama ke nan. Ita ma Laminden sai ta shirya ku je tare goben idan Allah Ya kai mu.”
Bayan tafiyar Muhibbat, Asiya ta rika jin hankoron son ganin ‘yar uwar ta. Ta kagara gari yaw aye. Da, a tunanin ta wani abin zai faru, amma ko da ta ga har a yanzu babu komai, sai ta kwantar da hankalin ta. Ai lafiya c eke buya, ko kuwa?
Da sassafe suka shiga motar Sani kwatambe ya kais u har tashar mota da ke kasuwar central a Bauchi. Kasancewar sa mai kaunar Muhibbat, bai karbi kudin su ba. su ka yi ma sa godiya.
“Muhi, yaushe ne za ki kira mu, mu sha bikin ki da Sani?”
Muhibbat ta harare ta, “Jiya.”
Asiya ta fashe da dariya. Ta san Muhibbat ba mai zaben maza ba ce, amma ta fannin Sani kwatambe kam, iska ce ke wahal da mai kayan kara. Ya na ta cusa kan sa, ita kuwa bai dame ta ba, don bay a gaban ta.
“Me da wukar. Daga tambaya?”
Muhibbat ta bude jakar da ta rataye mai launin ruwan kasa, wanda ya shiga sosai da atamfar ta na Diamond. Asiya kuwa doguwar riga ta saka na wani yadin material mai kyaun gaske.
“Ya kamata mu kira Maree, ko za ta sa a turo motar gidan ta a dauke mu. Kin san zuwan ba-zata mu ka yi.”
Ta na magana tana latsa lambar. Da ma tun can ita ke da lambar. Ita kuwa Asiya ko wayar ma ba ta mallaka ba. lokacin da Maree ke gida ne ta kan dauki na ta ta amfani idan ta na bukata. Ko da tayi aure ba ta bar ma ta ba. ta dai yi mata alkawarin aiko ma ta da wannan kwance da zarar Mudassir ya saya mata sabuwa, babba.
أنت تقرأ
Kudiri
عاطفيةHausa story of love, commitment and sacrifice. Yusuf and Asiya belong to different classes with nothing in common. Well, except for humanity. An incident had occurred which brought them together. Will their shared sacrifice bring them happiness and...