Babi Na Sha Takwas

4.5K 331 70
                                    

Finally, it is here. After power failure and ups and downs I will be able to rest, knowing I have fulfilled my promise of a double update to you. Love you all😘






Yusuf ya nufi bangaren da ofishin sa ya ke, mutane ne ke jere a kujeru su na zaune. Kowanne na jiran ya gan shi. Nas nas su ka gaishe shi, ya gyada mu su kai kawai a matsayin amsa, sannan ya shige ciki. Ko ina a tsaftace ne, kamar yadda ya ke so, an kuma jera ma sa fayel fayel na marasa lafiyar da zai gani a ranar. Kafin nan, zai fara nazari kan tiyatar da zai yi da azahar.

Ya zauna a hankali bayan ya duba kalandar kwanan wata kamar yadda ya saba, ya kalli dimbin fayel na marasa lafiya, ya nisa. Akwai aiki sosai a yau. Ya dauko fayel din farko ya bude, amma bai ga komai ba, idannun sa sun rufe.

‘Wa ya san gobe’ fa ta ce ma sa. Manufar ta daya ne, auren ta da shi bai dame ta ba. Nan ya ga wautar sa na ganin cewa kila akwai damar da Asiya ke da shi na maye gurbin Abida. Kwana ya yi bai runtsa ba a kan hakan. Sai ga shi ya ma ta shigar sauri, ya razana ta. A takaice dai, dole ya canja salon sa.
Hadi ya shiga ofis din ba tare da sallama ba. Ko da Yusuf ya dago ya lura da yanayin sa, ya ga tashin hankali da bacin rai ke bayyane cikin idanun sa da ma fukar sa.

“Lafiya Hadi? What is it?” Ya tamabaya cikin kulawa da damuwa. Ya tsayar da ta sa damuwar don fuskantar ta aminin sa. Yanayin Hadi kan canja ne idan wani majiyyacin da yake kulawa da shi ya mutu; ko kuma bai karya da safe ba.

Don kuwa yunwa ta kan daga masa hankali. Amma Yusuf bai taba ganin sa cikin wannan yanayi ba. Ya sha bamban da sauran, shi ya sa ya ba shi hankalin sa gaba daya.

Amsar da ta fito daga bakin Hadi ta girgiza Yusuf daga silin gashin kan sa zuwa yatsun kafar sa. “Na saki Kausar yau da safen nan.’’

Tun da Yusuf ya zaro idanu, sai kyafta su kawai ya ke yi. Hadi ya zauna kan kujerar da ke fuskantar sa. Mamaki ne ya cinye harshen sa.

“Garin ya ya hakan ya faru, Hadi?” Karshe muryar Yusuf ta dawo. “Babu fada ko sabani, sai kawai rabuwa?”

Dole ya girgiza, domin kuwa jiya suna tare da iyalan juna har yamma. Har shi Hadin ya ba shi kwarin gwiwar fuskantar matsalar da ta kunno ma sa a jiyan. Sai ga wannan kuma ya bijiro?

Hadi ya amsa, “Hakika ba mu yi fada ita ba. Ko jiyan bayan mun koma gida mu na tare cikin fara’a. rabuwar mu ta fahimta ce, ba gaba ko fada ba.  Ka san yadda mahaifin ta yake, ka kuma sha shiga tsakanin maganar mu.

To a jiyan kamar kullum, ya ziyarce mu, ya kuma jefa min bukatar sa na neman sakin diyar sa. Ni kuma a gaskiya na ji na kosa, na tsani jin kallaman sa a kullum idan ya tsaya a gaba na; wai tun da babu kira, me zai ci gawayi?”

Yusuf ya ji wani daci wa a wuyan sa. A kullum furucin Baban Kausar ga Hadi ke nan. Sai ka ce mutum shi zai ba wa kan sa haihuwa ba Allah ba. Ba abin boye ba ne, cewa Kausar ce ta so abin ta, amma mahaifin ta bai taba kaunar Hadin ba. Balle kuma da a ka samu wannan jarrabawa shike nan ya gaza hakuri.

A daren jiya, ni da ita mun dauki tsawon lokaci mu na tattaunawa irin ta fahimta da natsuwa. Ta gwada min cewa burin ta ne a duniya; karin karatu da kuma haihuwa.

Ta san zan iya daukar nauyin karatun nata, amma ta na son ta je wani wajen, ko Allah zai sa ta samu haihuwa. Saboda haka da safe nan, cikin tashin hankali da ban taba samun kaina ciki ba, na rubuta ma ta takardar saki daya, na kuma kai ta gidan su da kaina.

“I really don’t know, Yusuf, ban san abin da zan yi ba. Ni likita ne, kuma na bi hanyoyi da dama wajen gwaje-gwaje ni da matana duka, komai ya nuna cewa  muna da lafiyar samun haihuwa, Allah ne bai bayar ba.”

Muryar sa cike da takaici da kunci. A bayyane ne, wannan rabuwar ta girgiza shi fiye da yadda ya ke nunawa. Hadi mutum ne mai saukin kai tare da daaukar rayuwa cikin sauki. Ba karamin abu ba ne ya ke jijjiga shi.

KudiriWhere stories live. Discover now