Babi Na Ashirin Da Bakwai

4K 303 39
                                    

“Wannan bai yi ba.”

Muhibbat ta nisa sosai, “Me ye aibun sa Minde?” Ta tambaya, hannun ta rike da riga dikin atamfa. Ta sha kwalliya kuma ta yi zanzan, dinkin zamani daga likitan kaya, Jibayor da ke kasuwar central da ke Bauchi. Sanin kwarewar say a sa amare da ma wadan da ba amaren ba ke kai ma sa kayan su ya fere mu su dinkuna na gani a fada.

Asiya ta gyara zaman ta, ta na nazarin rigar, “Ba bu. Sai dai kyaun atamfa, in za a kai ki gidan ki ne. Don haka ki daura wancan leshi mai launin shunayya (purple). Zai fi fitar da ke.”

A ranar an saka walimar auren Dokta Hadi da Muhibbat. Auren kan sa sai washe gari za a daura.

Muhibbat ta daga leshin da Asiya ke magana a kai ta duba. Dinki ne fitted, kuma ta gwada ya karbe ta ainun, ta ce, “Kin fa san walima kawai zan yi, ba wani luncheon ba.”

“Ai a na sakawa. After dress kawai za ki dora a kai, ko ki yafa babban laffaya. Abu mai sauki!”

Muhibbat ta zauna a bakin gado, ta na fuskantar Asiya. Ta kai hannun ta ta dora a kan ta, ta na shafawa, “Wayyo Allah! Wannan abu duk ya ishe ni. Rabo na da barci na fi sati, ba na yin sa sosai. Ba na can, ba na nan, kamar zan balle biyu.” Muryar ta cike da gajiya da takaici.

Asiya ta yi dariya tare da tausaya ma ta, don ta san yadda ta ke ji. Shirin aure abu ne gagarumi. Duk da cewar ba ta ji hakan a na ta ba, ta yi na Mariya ta dandana, don kusan komai na shirin tare su ka yi shi.

“Wannan duk mai sauki ne.” In ji Asiya.

Muhibbat ta harare ta, “Ba ki ji abin da na ce ba ne?”

Asiya ta fadada murmushin ta, “Za fa ki auri mutumin da ki ke so ne. Shi ma kuma ya na son ki. Me ya fi hakan dadi?”

Muhibbat ta nisa, ta saki murmushi, “Kin san Allah Minde, ko tunanin sa ma ba na yi a halin yanzu. Don abubuwa sun min yawa. Ni ce karbar dinki, ni ce shirya walima, ni ce yin lalle, ni ce mai taron jama’a. Shi kuwa ya na can, hankalin sa a kwance.”

Asiya ta kyalkyale da dariya, “Amarya ke nan. Ai kowa ke ya ke sha’awar gani. Wa zai damu da sha’anin ango? Balle na tabbata, aikin da ya ke yi a yanzu ya na yi ne don ya samu damar cin amarci da kyau.”

“Dalla ja daga nan!”Muhibbat ta daga hannun ta, ta sauke kamar mai kade sauro, “Sai ka ce wannan ne auren sa na farko?”

“Hhmm, amma ke auren ki ne farko, ko da ba ke ce matar sa ta fari ko ma ke ce kadai ba. Dole ya yi yadda zai yi don ya tabbatar kin samu natsuwa da kwanciyar hankali. Balle ma in dai namiji ne ko kara mata sau dari zai na aure sai ya yi karkarwa nan da rawan jiki.”

Muhibbat ta kalle ta, fuska cike da zolaya, “Iye! Su Laminde manya. An yi kwas.Yanzu na zama dalibar ki ko?”

Asiya ta yi ‘yar dariya, “Ke dai bar wannan. In dai zaman gidan Dokta Hadi ne nice gaba zan dawo dalibar ki.”

Ta yi yunkurin tashi. Muhibbat ta dakatar da ita, “Me ki ke shirin yi?”

“Tashi zan yi mu gama zaben kayan, in ya so sai na duba wajen zaman walimar da a ka shirya a waje.”

“Don Allah rufa min asiri. Da wannan tukeken cikin naki ki je wani abu ya same ki mijin ki yakama ni. Da ma da ya ya ya bar ki zuwa bikin nan?”  

Asiya ta ce, “Ai shi ya ce na rika motsa jiki na, ina dan juya wa.”

“Hakan da kyau. Amma ki motsa a gidan sa, ba a nan ba. Ke kin ga mutum kamar zai hadiye ki? Tabdi! Wace ni?”

Asiya ta yi dariya. Sanin kan ta ne irin kulawar da Yusuf ke gwada ma ta tare da kauna, mata da yawa sai dai su yi mafarkin sa. Ba ya bari ta rika aiki sosai.

KudiriWhere stories live. Discover now