Babi Na Talatin Da Uku

3.3K 271 71
                                    

Asiya ta ci gaba da kuka kamar ranta zai fita. Ba ta iya jin kowane hakurin da su Umma ke ba ta. Su kan su hankulan su a tashe ya ke. Yusuf dai ya bar ta dakin ta ne don ba zai iya jure ganin hawayen na ta ba. Don kuwa hankalinsa kara tashi ya ke yi, kwakwalwar sa ta gagara yin tunani.

Lokacin da Asiya ta fara gaya ma sa cewa Mariya ce ta shiga gidan ta fitar da Nurain, ya sandare, mamaki ya toshe kwakwalwar sa a yayin da kalaman Asiya ke nutsewa cikin ta.

Mariya? Ta dauki dan sa? A fadin duniya idan akwai wadda ya tsani jin sunan ta, ya kuma tsani ganin ta, to bai wuce Mariyar ba.  Ko da kuwa ‘yar uwar matar ta sa ce. Ta ja ma sa matsalolin da har ya mutu ba zai manta ba. ba sai ta kara da wannan ba.

A lokacin ya bi sawun ta da kafa, Bature ya same sh Gudu ya diba ya na ci da zuci tare da kwafa. Idan har Allah Ya sa ya same ta da dan sa, Allah Ya gani, zai mance da dangantakar ta da matar sa, kuma uwar ‘ya’yan sa.

Zai mance da cewa ita uwa ce ga Amatullah. Don ta wuce gona da iri a wannan karon. Ta wuce kan su iyaye ta zarce kan dan su. Ba zai juri hakan ba.

Ya karade gewayen su kaf, tun ya na yi da kafa har Bature same shi da mota. Ba su ga Mariya ba. Shi kuwa bai zame ko ina ba sai gidan su Yafendo.

Kan sa tsaye ya shige gidan, zuciyar sa na tafarfasa don takaici. Ya san duk yadda a ka yi, su na da masaniya ko nasaba game da abin da Mariya ta yi a wannan dare.

Ya san cewar tun haihuwar Asiya, Yafendo ba ta taka kafar ta zuwa yin barka gidan sa ba, sannan ba ta je sunan ba. Ta fi kowa adawa da wannan haihuwa don ta tsani Umma, ta kuma ji haushin cewar ta tsatson ta a ka fara samun jikokin gidan, wandanda shari’a ta amince da su.

Ko da ganin sa cikin gidan su, fuskar ta ba ta nuna alamar jin mamaki ba.  Sai ma kallon sa ta yi cikin gatse, sannan ta ce, “Yau kuma Dan auta an yi batar hanya ne a ka zo nan?”

“Ina da na Yafendo?” bai bata lokaci ba. kowane dakika daya ya na kara nisantar da Nurain gare su.

Ta saki dariya busasshiya, ta ce, “Yau na ga ikon Allah, wai na kwance ya fadi! Ina ruwan maza da wankan jego? Ina ruwan kwado da rigar ruwa? Me ya hada ni da gidan ka ballantana danka? Kai kuma waye, wai kiyashi a jirgi! An gaya maka ni hankaka ce kamar ka, wanda ke mayar da dan wani na sa?”

Kokari yake ya danne zuciyar sa, amma ba don haka ba da ya aikata abin da zai yi nadamar sa daga baya. Ya ce da ita, “Duk in da mai aro ya je, da sanin mai riga. Mariya ba zata taba aikata abin da tayi min ba tare da hadin kan ku ba. Na san kun san wurin da ta ke. Ki fada min na karbo da na, mu wuce wurin. In kuwa ba haka ba, za ku yaba wa aya zaki, gaba dayan ku.”

Yafendo ta kalle shi sama zuwa kasa a lokacin da ta mike tsaye, ta ce, “Iye, sannu Dan auta. Wato uwar taka ce ta turo ka ta ce ka zo nan ka ci min mutunci ko? To wallahi ka bar ganin girman kuka, bagaruwa ce babba. Kuma ka da ingarma ya raina gudun kura. Kudin ka da matsayi ba za su yi tasiri a kan mu ba. Je ka yi duk abin da zaka iya yi, yadda ka gan mu, haka zaka bar mu. Sai dai kaska ta mutu da haushin kifi a ruwa!”

Yusuf ya ce, “Ni dan zamani ne Yafendo. Kuma idan zamani ya riski manshanu ko an soya shi baya kamshi. Zan fice zuwa gida, na ba da nan da awa daya, ya kasance na samu da na a kwance a gida.” Da wannan ya juya zai yi yunkurin ficewa daga gidan.

“Ban dauki danka ba, Dan-auta.” Ta tsayar da shi a takaice.
“Wannan shirin Mariya ce, babu hannu na ko na Khalid a ciki.”

Bai san dalili ba, amma ya tsinkayi sautin gaskiya a cikin kalaman ta. Duk da haka, ya ce, “Idan shege ya bata, shege a ke sawa ya nemo shi. Kin fi kowa sanin wurin da za a samu Mariya, don haka ki yi gaggawar aika sakona gare ta.” Ya sake kallon agogon sa na hannu, ya dora da “Awa daya tak!”

KudiriWhere stories live. Discover now