Ya furta hakan, amma bai motsa ba, bai kuma bar kallon ta. Tsawon say a kara bayyana a yadda yake tsaye a gaban ta. Rudani da kasala su ka yi barazanar jefar da ita, a yayin da wata kunya ta nemi nutsar da ita cikin kasa. Karar bugun zuciyar ta kuwa, ta yi yakinin yana iya jin sa…du-dum! Du-dum!! Du-dum!!!
Haushin karnukan gidan da hayaniyar mutane ta ke ji a kofar shiga, amma ta gagara motsawa. Amatullah na gefen ta amma ta gagara kallon ta.
Karshe dai shi ne ya sakar mata murmushin da ya jefa mata karin rudani cikin kwakwalwa sannan ya juya ya nufi kofar fita waje. Ta kura wa bayan sa idanu ya na tafe cikin kasaita don ya tarbi bakin su, tamkar ba wani abin da ya kusan faruwa a tsakanin su a yanzun nan.
A tsawon rayuwar ta, ba ta taba tsayawa kusa da namiji ba kamar hakan. To amma idan ta duba, ba ta taba yin aure ba sai yanzu. Kuma wannan din mijin ta ne, halal, na sunnah.
Ta yi sauri ta danne duk wasu abubuwa da suka taso cikin zuciyar ta. Baki ne a gidan na su, baki na musamman. Duk yadda ta daure da ma yadda Dokta ya nuna mata karfin halin ta, sai da ta ji shakkar haduwar su.
Ba ta san yadda za su dauke ta ba, ko kuma yadda suke dukan su. A jiya ne da suke wajen gyaran gashi Sara ke mata bayanin su.
“Sunan matar Dokta Sadi Amina, ‘yar cikin garin Bauchi ce, unguwar Makera. Ta na da son kwalliya a fuskar ta caba-caba, ta yadda duk ranar da ba ta yi ba, za ki ga ta canja, har ma ki yi zaton ba ta da lafiya ne. mayyar son taliya ce…” Saran ta kara sauke murya tare da kare bakinta da hannun ta na dama, “…don bata iya dafa komai ba sai ita.”
Asiya ta dan yi dariya, “Kai Sara.”
“Ina gaya miki. Da safe da rana da dare duk taliya. Aminar taliya a ke ce mata, shi kuma mijin nata kamar noodles. Hahaha.”
Dole Asiya ta dara, “’Ya’yan su kuma fa?”
Sara ta gyara hannun ta don mai zana mata lallen hannun ta ji dadin cancara wa. Ba ta fara sol, lallen ya ba da kala. Ta amsa, “Babu ko daya. Sau biyu ta na haihuwa amma bas a fitowa da rai. Sun ce dai wai jinin ta ne ya fi karfin na yaron ne ko ya na hawa na yaron ne? Wai dai abin a tsatson wato genetical.”
Asiya ta tausaya mata kwarai da gaske. Sannan ta sa ran haduwa da ita, don ta na ganin alakar su za ta yi kyau.
“Sai kuma Fatima, matar Dokta Kabir.” Sara ta ci gaba da sharhin ta, sai ka ce wata mai aikin gidan rediyo. “’Yar Kaduna ce. Mace ce mai son nuna aji da isa don kawai ita ‘yar birni ce. Dole ai, don ta na ganin ya tsallake kogi goma sha biyar kafin ya kai gare ta, irin ita ta fi kowa a nan Arewan nan.”
Asiya ta girgiza kan ta, “Ba ki da dama.”
“Ina gaya mi ki, yadda take ji da mijin nan na ta. Sun haifi da daya ne, ya na kuma wajen mahaifiyar Doktan.”
“Masha Allah. Abu yayi kyau.”
“Hmm, sai fa a hankali. Ai da suka kai shin ba wai yaye aka ma sa ba. Sai don dai kawai it aba mai yawan son fitina b ace da hayaniya. Renon yaro kuma akwai wahala shi ya sa suka kai wa kakar sa ta rike mu su.”
“To?”
“Ah, ki na mamaki ne? To ko da za ta haihu ma tiyata aka mata, wai idan ta yarda ta haihu da kanta to za ta lalata ni’imar ta.”
Asiya ba ta taba jin hakan ba, abin kuma y aba ta mamaki. A zaton ta, haihuwa baiwar Allah ce da kowace mace ke burin sam, sannan zafin nakudar ma kan ta ibada ne, don duk wadda ta mutu ta wannan hanyar ta yi shahada. To ita me ta sani, tun da ‘yar kauye ce ita.
“Sai nag aba, matan dokta Hadi guda biyu, Suhaima uwargida, Kausar amarya. Suhaima irin matan nan ne da suka kasance sari-ka-noke, wato Musa a baki, Firauna a zuci. Kausar kuwa ‘yar ba ruwan ta ce. Mijin su kuwa, shine babban aminin naki mijin, sannan kuma mayen tuwo miyar kuka ne.
YOU ARE READING
Kudiri
RomanceHausa story of love, commitment and sacrifice. Yusuf and Asiya belong to different classes with nothing in common. Well, except for humanity. An incident had occurred which brought them together. Will their shared sacrifice bring them happiness and...