First of all, I apologize🙏🙏 for the late update. I hate breaking promises but it was unavoidable. Well, here it is, your first long update😀. It is the longest chapter yet and I hope it will meet your expectations.
Mariya ta kalle su cikin mamaki, sannan kunya ta biyo baya. Maimakon ta yi musu maraba da murnar ganin su, sai ta yake hakoranta.
Ta na daure da zani kodadden gaske, kan ta da hula amma gashin kan ta a tsettsefe, ya na nunawa ta kasan hular. Ta riko buta a hannun ta na hagu, ga alama daga bandaki ta fito. Ga ciki rusheshe, ya fito fili.
“Muhi, Laminde, sannun ku da zuwa.” Ta na magana muryar ta na kadawa. “Ku zo mu je daki.”
Gidan irin na gadon nan ne, mai sassa daban daban. Suna wucewa kowa sai kallon su yak e yi. Mata ne da yara cike tab, fututu da su. Wasu yaran suna warwaso kan faten tsaki, uwayen su kuwa suna ihun ce musu idan ba su ci a hankali ba to ba za su samu kari ba. Ba wai ba su taba ganin irin gidan ba ne.
Irin sa ma a Dagauda akwai. Amma ganin Maree a ciki ya jijjiga su. Ita da ko gidan mahafin su ma mitar zama cikin sa ta rika yi kafin auren ta.
Mudassir ya gabatar da su ga matan gidan, su kuma suka rika yi mu su maraba lale. A hakan ne har suka isa sashen da suka hangi Mareen da shigar su. Asiya ta tsaya ta kalli sashen. Duk da cewar a birni ne, jinkar ciyawa ce a saman dakin Mareen…idan an kira shi daki ke nan.
Cikin sanyin jiki Maree ta canja zuwa wata doguwar riga mai kamar buhu, sannan ta dan yi mu su murmushi, alamar ba ta so su gan ta cikin yanayin da suka yi ba.
Dakin babu girma, in an bar Asiya, za ta ce akurkin kaji ne. Akwai tabarma guda da ke shimfide kan tsohon kafet din da ke baje, a gefe guda wata ‘yar katifar da ba ta wuce waya goma ba ke shimfide. Dakin a hargitse ya ke kamar ba mutane ke kwana a cikin sa ba. Hakika ya yi na sabani da wanda suka bar ta cikin sa a Azare.
Asiya ta gagara magana, kuka kawai ta ke son yi amma ya ki zuwa ma ta. Wannan wacce irin masifa ce haka? Ina aljannar duniyar da ta samu? Wallahi, da wannan ukuba gwara ma da auren Buba saurayinta na farko ta yi, da ya fi mata.
Buba ya so Maree tun sun a saurayi da budurwa, amma karatun da ta saka a gaba ya hana ya aure ta da farko. Kaddara ta saka ya auri Rumana.
Amma duk da hakan bayan ta kamala sakandare ya koma. Sai dai ita Maree ta hani kanta da auren talaka. Sai ga shi an ki kare wajen tsuguno an dauko biri.
Zafin yanayi ya rufe su. Watakila don tafiyar da suka sha ne kuma dakin babu fanka. Ko kuma tsananin kaduwar da suka yi. A ganin Asiya dukkan su ne. don kuwa ta san ba za ta taba mancewaa da wannan rana ba, har mutuwar ta.
* * *
Asiya ta yi zugum kamar yadda Muhibbat ta yi, suna sauraron Maree kawai, wacce ke bayanin halin da ta shiga ciki. Bayani ne ta rika yi babu boye boye. Ga alama ta dade tana neman wurin da zata amayar da cikin nata ko zata ji sanyi.
Ciki. Hankalin Asiya ya tsaya kan cikin Maree, da yadda ya fito sosai. A gaskiya, fiye da rabin bayanin na ta,ba saurare ta ke yi ba. Tausaya wa ‘yar uwar tata kawai ta ke yi.
Ta na jin Muhibbat ta tambaye ta, “Haba Maree, me zai sa ki zauna cikin yanayin yaudarar na da wulakanci hade da zalunci? Ki duba ki ga irin karyar da ya rika cika ki da su a can garinmu? Wannan zai iya kashe ki ya boye wukar.”
Maree ta yi wata dariyar da babu armashi, ta ce, “Na bar komai a hannun Allah.”
Asiya ta sake kallon tumbin Maree. Ita ma ta kasance mai yaudarar mijin nata ne tare da munafurtar sa. Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa ta yi shiru. Shi da kuma gudun kar a mata dariya, ta sha kunya idan asirin ta ya tonu. Don kuwa a Dagauda, zata zama abar kwatance.
YOU ARE READING
Kudiri
RomanceHausa story of love, commitment and sacrifice. Yusuf and Asiya belong to different classes with nothing in common. Well, except for humanity. An incident had occurred which brought them together. Will their shared sacrifice bring them happiness and...