Assalamu alaikum. It's the twentieth chapter already? I can't believe it. We have reached this far and your support has not wavered.
That is more proof that you're all awesome 😍😘. Thank you for your time and support. Keep voting and commenting.
Love you 😘😘
Dokta Yusuf Haruna ya shiga gidansa cikin sauri, zuciyar sa da idanun sa sun kagu da son ganin matar sa. Da ma Amatullah, diyar da kotun da ta mallaka ma sa; ko kuma ta mallaka wa Asiya.
Yusuf bai zauna ba kwana daya rak, bayan hukuncin da Malam Dalhatu ya yanke a zauren su, har sai da ya ja hankalin iyayen sa a kan raba ta da Amatullah. Ya yi nuni da yadda addini musulunci ya tsara a kan cewar idan babu mahaifiyar jaririya, to za a samu ma fi kusa da ita, wato ko mahaifiyar uwar ta, wato kakar wajen uwa, ko kanwa ko yayar ta ta jini. Idan an duba babu, to shine sai a koma kan kakar wajen uba.
Yafendo ta ja da hakan, ta na nuna cewa ai tun da shayar da ita nono a ke yi ba, to ita ma za ta iya ba ta. Sai da kotu ta binciki yadda za su rike ta, ma’ana wajen suturar ta, wajen kwana da kuma sayen irin abincin da ya kamata su rika ba ta idan sun karbe ta.Da farko dai Khalid ba ya da sana’a ko aikin yi. Don haka ba zai iya kulawa da jaririya ba. A karshe dai bias dole, a ka bar wa Asiya rikon diyar ta. A yanzu komai yayi dai dai a tsakanin su. A kalla, kusan komai……
Ko da shigar sa, kai tsaye ya wuce dankin ta, wajen da ya same ta zaune bakin gadon ta.Shigar ta ta doguwar rigar atamfa (fitted gown) ta karbe ta. Kan ta babu dankwali, sumar kan ta a daure ya ke, baki wuluk sai sheki ya ke yi. Fatar jikin ta ta kara haske, sannan fararen idanun ta sun inganta kyaun ta. Ba kwalliyar tashin hankali ta ke yi ba, amma wadda ta ke yi, ba karamin fidda kyaunta ya ke yi ba.
Ta mike tsaye, a kunyace ta ce,“Sannu da dawowa.”
Sai da ya hadiye yawu da kyar, jin muryar ta sassanya da kuma ganin surar ta mai shagaltar da shi. Ya matsa kusa da ita, ya lura ta shiga rudani, kamar ranar da ta fara shiga dakin sa. Sai da ya tsaya a gaban ta ya tuno da yadda numfashin ta ya rika hawa da sauka a kirjin ta a rannan, da yadda kamshin ta ke ratsawa cikin kwanyar sa. Ta sauke idanun ta cikin jin kunya. Hakan ba karamin tsima shi ya ke yi ba.
“Yau sati guda ke nan rabon da na tsaya mu gaisa da ke sosai. Ko ma dai na san halin da ki ke ciki.”
Ta dan dago kadan ta kalle shi, sannan ta saki murmushi, hakoran ta su na burge shi, ta ce, “Yanayin aikin ka ne ya sa hakan. Kuma har ga Allah b aka bar mu cikin kunci ko matsala ba. Haka ma Amatullah.” Ta dan kara sunkuyar da kan ta, ta dora da, “Kuma ta yi kewar ka.”
Muryar ta da kadan ta fi rada. Ya tabbata ba ta san yadda hakan ke s aka shi ji ba. Ya saki ‘yar murmushi shi ma, wanda ya tabbatar zai iya aika ma ta kadan daga cikin halin da zuciyar sa ke ciki, “You have no idea, ba ki san yadda na yi kewa ba…” Ya dan kara matsawa dab da ita, sannan ya sauke muryar sa sosai, “Kewar dukan ku biyu.
Ya lura ta kara sunkuyar da kan ta. Shauki ya kara kama shi. Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na dawo yau da wuri, na samu off na sauran yau gaba daya.”
A lokacin karfe uku ne, da ya kalli agogon san a hannu. “So, dama ina ta son kewaya cikin gari, and I was wondering, ko zan samu ‘yar rakiya?”
Ta dan kalle shi kadan, “Kewaya? Yanzu? Na ga yanzu ka dawo.” Ta tambaya.
Ya yi murmushi, “Na sani. “Na yi la’akari ne da cewar tun da ki ka shigo nan gidan ban taba kai ki ko ina ba. Ki shirya kawai bayan sallar la’asar sai mu je.”
Ita ma ta yi murmushi, “Bari na shirya Amatullah, in ya so sai mu same ka a falo.” Muryar ta da zumudi.
“Actually, wannan fitar ba tare da Amatullah za mu yi ba. Daga ni ne kawai sai ke. More like, kamar fita date ne, tsakanin abokai biyu. Hakan zai kara ba mu damar fahimtar juna a matsayin haka.”
YOU ARE READING
Kudiri
RomanceHausa story of love, commitment and sacrifice. Yusuf and Asiya belong to different classes with nothing in common. Well, except for humanity. An incident had occurred which brought them together. Will their shared sacrifice bring them happiness and...