Babi Na Talatin Da Hudu

3.5K 328 63
                                    

Daki ne cike da duhu kamar yadda yake a waje. Ba a iya ganin ko da tafin hannu ne. asiya ta dafe kirjin ta cikin tsananin tsoro da fargaba, ta shiga addu’ar Allah Ya raba mu da duhun kabari.

Kuka take ji mai shiga jiki, amma ba ta iya ganin komai. A yayin da kukan ya tsananta, zuciyar ta ta shiga tsere, ta na matsawa cikin duhun. Ta fahimci kukan dan ta ne Nurain, wanda ke yin sa cikin tsananin bukatar dauki.

Ta fara gudu, ta mance da dukkan wani duhu ko tsoro, zuciyar ta na tsalle. Nurain! Nurain ya na bukatar ta, za ta je gare shi cikin gaggawa. Da wannan zummar ta nufi wurin da ta hangi wani haske kadan, wurin da ta lura da wata mace tsaye a wajen, ta na rike da jariri.

Ko da ta matsa kusa, ta ga Maree ce, ta na kuma rike da Nurain. Amma maimakon ta mika ma ta, sai ta yi miskilin murmushi sannan ta daga shi sama.

Asiya ta shiga rokon ta da ta ba ta dan ta, amma idanun ta a soye, suna  cike da muradin son su kuntata ma ta. Ta na ji ta na gani, Mariya ta jefar da Nurain ta taga..…

Nurain! Asiya ta farka daga gyangyadin da ya sace ta, cikin zufa da haki. Karo na uku ke nan a wannan dare irin wannan mummunar mafarkin ke faruwa da ita.

Yusuf ya dafa ta daga kan sallayar da yake zaune, idanun sa cike da tausayi irin na ta. Tsawon dare biyu ke nan suna cikin fargaba da zullumin rashin dan su. Babu abin da suke yi sai salloli da adu’o’i.

Umma ta sa an bayar da sanarwa masallatai don a taimaka mu su da addu’ar Allah Ya bayyana Nurain, sannan ya tona asirin wadan da suka sace shi.

Cikin kwanaki biyun nan ba ta cikin hayyacin ta. Numfashi kawai take iya yi, amma ba ta san yadda a ka yi ta ke yi din ba. Ta zama kamar fatalwa.

Ba ta sanin lokaci sai idan Dada ta sanar da ita lokacin sallah ya yi tukunna take tashi. Abinci kuwa ya kaurace wa makoshin ta, sai fa a dole take shan ruwan dumi don kar ta cutar da Aslam.

Kukan Aslam ya na kara tayar ma ta da hankali, musamman idan za ta shayar da shi. Karshe ma madara ya koma sha dindindin, a maimakon farkon rayuwar sa da yake hadawa da ruwan nono.

Yusuf ya ci gaba da kallon ta, yana du’a’i. Ba sa iya ce wa junan su komai don sun kai ga ganin kalamai bas a isar su wajen kwantar da zukatan su. Sun dagara ne kan idanun su wajen isar da kowane sako.

Asiya ta mike ta koma bandaki don sabonta alwalar ta. A kowane dakika kukan Nurain take iya ji, ta na tunanin abin da a ka shayar da shi, in har an shayar da shi din. Hakika, Maree ta kai kololowa kan zalunci.

Tsawon kwanaki biyun nan sun yi waya daban daban da Yusuf, kan maganar kudaden da suka bukata. Yusuf miliyan goma ya iya hada wa don karancin kwanakin da su ka ba shi ya hada mu su ya ba su.

Suna hakan kuma ‘yan sanda suke binciken su game da wannan al’amari, a yayin da fitilar su ta haska Larai da maigadin gidan. ASP Hashiru, cikin kwarewar aiki da sanin halayyar dan Adam, ya sanar da su cewa akasarin sata irin wannan, a kan yi nasara ne idan akwai hannun na gida a ciki.

Wai hausawa sun ce da dan gari a ke cin gari. Bugu da kari kuma ita ce mutum ta karshe da ta gan shi, kuma ma itace ta mika shi wa Mariyar.

Larai ta ci kuka kamar ran ta zai fita, har ta ba wa Asiya tausayi. A ranar da a ka fita da ita da sunan kai ta cibiyar bincike na ‘yansandan ciki, wato CID, Yusuf kau da kan sa yayi, ya sunkuyar ba tare da ya kalle ta ko ya kula kukan da take yi ba.

“Yallabai, ka yi min rai. Na dade da ku ina aiki, a nan na ke ci da sha tare da rufa wa kaina asiri. Na rufa asirin gidan nan, kar ku tozarta ni. Wallahi yallabai ban san komai ba.” ta juya ga Umma, “Hajiya Umma, kar ki bari su tafi da ni don a wulakanta ni.”

KudiriWhere stories live. Discover now