“Aure ya kunshi abubuwa guda uku; abota, aminci/yarda, sannan so da kauna. Su ne ginshikin aure, ma su saka shi yayi inganci da karko, wadanda babu ko daya a tsakaninmu. Anya, b aka ganin kuskuren aure idan babu su?”
A lokacin tana fuskantar tagar dakin, wajen da hasken alfijir ya fara bayyana. A ka fara kiraye kirayen assalatu. Ya matsa kusa da ita, y ace, “Kuskuren da zamu yin a jefar da yarinyar nan zai fi na auren mu. Kamar yadda na ce ne, auren wucin-gadi ne. Ba zan matsa miki wajen zama da ni ba. A duk lokacin da ki ka yanke shawarar rabuwar mu, ina baki tabbacin sawwake miki, ki yi tafiyar ki.”
Wucin-gadi. Ko da dai ba ta damuwa da Kalmar aure, amma ta tabbata wannan kalma ba ta cikin lissafi. A tunanin ta, aure idan aka yi shi, to na har mutu-ka-raba ne. Karewa ma, ba ta taba tunanin wani zai nemi auren ta a dakin asibiti wajen karfe hudu na asubahi ba. Abin kamar a mafarki.
Ta dan kale shi, “Ka fada min abin da Umma ta ce game da wanna shirin.”
Bai kalleta ba, “Ban fada mat aba tukunna. A tunani na, bayan mun daidaita sai na fada mata.”
Duk da cewa Umma ta matsa ma sa kan yayi aure, yanke wannan shawarar da yayi ba tare da neman shawarar ta ba gaganci ne. amma shi a gaban sa jaririyar nan ce.
Ya ji ta ce, “A duk aikin da ake so yayi kyau ya na da muhimmancin a samu hannun manya. Duk da na san mahaifana ba lallai sub a da goyon baya gare ni ba, zan so a ce Ummarka ta san shawarar da ka yanke.”
Dokta ya ce, “Fair enough. Yanzu zan je na yi sallah. Kafin azahar zan dawo nan, a lokacin zan so jin amsar ta ki.”
Da wannan ya dan tsaya a gefen jaririyar, wacce ke barcinta a tsanake, sabanin asubahin jiya. Ya sa hannun sa duka biyu ya dauke ta, ba tare da karin magana ba, ya kai kunnuwan ta dab bakin sa……
* * *
Asiya ta tsaya kallon Dokta Yusuf, wanda ga alama, huduba yak e yi wa Baby A. hakan ya matukar sosa mata zuciya. Idan a da ta na shakkar son da yake yi wa yarinyar, a yanzu ta cire.
Ya ajiye ta a kan gadon ta sannan ya ci gaba da kallon ta, “Na rada mata suna Amatullah. Ina mai mata addu’ar Allah Ya raya ta cikin addinin musulunci, Ya kuma daukaka ta duniya da lahira.”
Kwalla suka ciko idanun Asiya, ta ce, “Amin.”
Har ya bude kofar zai fita, ya tsaya ya sake kallon Asiya, “Kar ki matsa wa kan ki. Idan har zuwa lokacin da na dawo amsar ki a’a ne, ina baki tabbacin komai zai zauna tsakaninmu a matsayin sirri. Zan ba da mota a mayar da ke har gida cikin aminci. Ina son ki sa abin cikin addu’a. allah Ya mana jagora.”
Daga nan ya fice, ya bar ta da neman wuri ta zauna don kar kafafuwanta su jefar da ita. Sai a lokacin komai ya zo mata gaba daya.
Da farko ta dauka ko zagin kunne ne, ko ma zolaya da rainin hankali. Daga baya ta ke tabbatar da cewa kudiri ne, wanda ko da ita ko babu, yayi niyyar cimmawa.Ta kowane bangare Yusuf ya na ba ta mamaki, da ma fargaba ko tsoro. Kalaman sa sun jijjiga ta, sannan suka yi majajjawa da ita zuwa wata duniya daban- wurin da komai ke faruwa cikin mafarki. Ba ta san ko hakan abu ne mai kyau ba.
Kai tsaye ta samu kwarin gwiwar shiga bandaki ta yiwo alwala sannan ta dawo dakin ta bada farali. Ta na zikiri baby A…. Amatullah, ta motsa daga kwance.
Ta mike cikin sauri ta daga ta tun kafin ta bude bakin ta ta rera mu su wakar da babu kida. Ta bata ruwan dumi kadan ta sha. A zuciyar ta, ta so ta bata ruwan zam-zam ne. amma babu abin da ke tafiya daidai game da rayuwar Amatullah.
Amatullah, baiwar Allah. Sunan ya dace da ita matuka. Ta rungume ta, zuciyar ta na nazari. Kamshin Dokta Yusuf da ke jikin shawul din daukar ta ya kara shige mata kwanya. Ta kara tuna da kudirin san a rike Amatullah ko da ita ko babu.
![](https://img.wattpad.com/cover/97770052-288-k325894.jpg)
YOU ARE READING
Kudiri
RomanceHausa story of love, commitment and sacrifice. Yusuf and Asiya belong to different classes with nothing in common. Well, except for humanity. An incident had occurred which brought them together. Will their shared sacrifice bring them happiness and...