Babi Na Ashirin Da Biyu

4.6K 338 93
                                    

Assalamu alaikum. 😯😯😯🏃🏃 double today, God's promise🙏.  Thank you for your patience. Love you all 😘😘😍





A falo ta same shi, ya na zaune gaban talabijin, amma ya na dauke da komfutar sa bisa cinyar sa, ya dannawa.

“Assalamu Alaikum.” Ta yi ma sa sallama.

Ya amsa, “Wa alaikis salam.”

Ya kalle ta a hankali cikin natsuwa daga sama har kasa, sannan fuskar ta. Ta ji idanun sa na shiga jikin ta tamkar askar wanzami. Idanun sa na dauke da abin da zuciyar ta ce kadai ke iya fahimta, amma ba za ta iya fassara shi da harshe ba.

Bai taba ganin shigar ta irin wannan ba. Ta yi ma sa kyau gaskiya, kamar ne a ce mutum ya rika kallon hudowar rana daga sararin samaniya. Akwai haske mai watsa launin gwal tare da dimbin alkawarin haskaka wannan rana. Dukkan furanni da ma mai rai ya dogara ne da wannan fitar ranar.

“Na kai abincin ne tebur.” Ta furta, kan ta a sunkuye.

Ya lura da jin kunyar ta. Ba zai iya misalta yadda hakan ke kara burge shi ba game da ita. Taraddadin ta tsima shi ya ke yi.

“To Bismillah.” Ya ce da ita.

Ta koma teburin, har ta zauna idanun sa ba su kau daga kan ta ba. Shi ma ya taso zuwa teburin ya ja kujerar sa da ke kusa da na ta ya zauna. Ya canza kayan jikin sa zuwa doguwar jallabiya mai gajeren hannu. Kamshi biyu ke tashi daga gare shi; na sabulun wankan sa da kuma turare.

“What’s for dinner? Me ye abincin daren yau?”

Ta dan kalle shi, shi kuwa ya tsare ta da idanu. Da gangan ya sauke muryar sa, ya na murmushi a lokacin da yak e ganin tasirin hakan. Ta kasa tabaka komai.

Ta bude kwanukan a matsayin amsar ta. Kamshin ferfesun kaji mai kayan kamshi tare da tafarnuwa ya naushi hancin sa. Taliyar Penne ta dafa tun kafin fitar su da yamma, don haka ta hada da kajin da suka sayo, wanda ta sake gasawa cikin oven cikin gaggawa. Ta kara cika kayan kamshi da albasa da yaji.

Bai san lokacin da cikin say a rika yi ma sa kugi ba. Kafin ta fito yayi zaton a koshe yak e, kawai dai zai dan taba ne. amma a yanzu ji yake kamar zai ci giwa.

“Na san zaa iya neman ka zuwa aiki a ko da yaushe, shi ne na yi maka abinci marar nauyi.” Ta furta cikin murmushi mai garwaye da jin kunya.

Ya yi murmushi. Ya ji dadin kulawar ta. A dan zamantakewar su, ta fara kiyaye abubuwan sa da dama. Bai san ko duk ta na hakan ba ne don Amatullah. Shi ya sa ya ke son su zauna su dan tattauna a kan hakan. 

Ita ma ta yi murmushi sannan ta kara sunkuyar da kan ta cikin kunya. Bai san wanne ne ya fi tsima shi ba; abincin da ke gaban sa ne, ko kuma ita. Ta ma fi abincin da ke gaban sa.

“Well, ina jira, ki zuba min da hannayen ki.”

Ta dago ta kalle shi. Bai san ko zai iya jurewa ba, amma idan ta kara yi ma sa wannan kallo to zai mance da yunwar abincin da ke gaban sa ya ja ta zuwa jikin sa. Ko ma me za ta dauke shi sai ta dauka, zai mance da alkawarin da ya dauka ma ta kafin auren su.

Bayan ta zuba a filet, har ya fara ci, ya ce da ita, “Bismillah mana, ina kwarya.”

Ta ce, “Ba na jin yunwa. Na ci abinci da Muhibbat dazu.”

Ya dan bata ransa tare da ajiye cokalin sa, “Ni kadai za ki bari ina ci yanzu? Gaskiya ban ji dadi ba. Ko albarka ki saka min.”

Ya lura da damuwa cike da idanun ta hade da nadama. Abin da ya ke son gani ke nan. Ta dauki wani filet zata saka na ta. Yayi sauri ya dakatar da ita, “Me ye amfanin nawa filet din?”

KudiriDove le storie prendono vita. Scoprilo ora