Babi Na Ashirin Uku

3.8K 344 47
                                    

Hannayen ta rike da saman kujera, ta kalli mijin ta, bai ce komai ba, kallon su kawai ya ke yi. Ta ce, “Tooo?! A waje na? Allah Ya ba ni ikon cika ma ka kokon ka.”

Yusuf ya kalle ta, ya ce da ita, “Gwara ki zauna.”

Ba ta yi dogon tunani ba, ta zauna. Hadi ya ce, “Game da kawar nan taki ce.”

Mamaki ya bayyana a fuskar ta, “Muhi? Me ta yi kuma?”

“Kwantar da hankalin ki. Za ta yin dai.”

Ya ture shayin da burodin sa gefe, ya tsayar da hankalin sa kan Asiya, “Gaskiya, amarya babu boye-boye, ko kwane-kwane; na gani ne ina so. Auren ta kuma na ke son yi, amma fa in an ba ni dama.”

Yusuf ya lura da fuskar Asiya. Tsoro ne zalla, sannan mamaki. Da kyar ta yi magani, “Don Allah zolaya ta ka ke yi?”

Hadi ya tsuke fuskar sa, “Babu wasa a cikin wannan magana. Na fa zo ne na ji in zan samu shiga. Don kuwa na san kamar ta, ba za ta rasa masoya tari guda ba.”

Nan fuskar Asiya ta nuna matukar kaduwa, “Haba kai kuwa? Ya ya ka ke son na kalli Suhaima? Gaskiya, ba zai yiwu ba.”

“Amarya, ki taimaka na samu shiga a wajen ta.” Ya ci gaba da naci. “Da alheri na zo, babu sharri. Na fada mi ki, son ta na ke da aure.”

“Amma ba ku san juna ba. Ya ya za ka fara zancen aure?”

“Aure gamon jini ne. Kuma sau da dama za a so juna, a san komai game da juna, amma a zo ba a yi auren ba. Komai ai nufin Allah ne.”

A lokacin Yusuf ya sa baki, “He is right. Aure nufin Allah ne. Ke dai in babu matsala ta fannin Muhibbat, kawai ki ma sa jagora. Sauran zai ci gaba daga nan.”

Ta dage da a kan kin maganar, “Ku maza ba ku da matsala ta wannan fanni. Amma mu mata mu na da ita. Ya ya Suhaima za ta dauke ni?”

“Ai ba wai wannan ne karon da za ta zauna da kishiya ba.” Shi ma ba hakuran zai yi bag a alama.

Yusuf ya ja tafin hannun ta, wanda ya yi sanyi kalau, ya rungume cikin na sa, a yunkurin kara mata kwarin gwiwa, “My dear, me zai hana ki tuntubi Muhibbat da maganar don jin ra’ayin ta. In ta ce ba ta amince ba kin ga sai ya hakura. Idan kuwa ta karbi wannan tayin na sa, sai ya fara ziyartar ta a can gida, a hankali su kuma sai su tsayar da magana. Idan Allah ya sa rabon sa ne, sai ya aure ta. In kuma Allah bai yi ba, shi ke nan.”

Asiya ta nisa, ta kalle shi sosai. Idanun ta na bayyana jin dadin kalaman sa, ta ce, “To, bari na je na ji ra’ayin nata.” Ta san Muhibbat za ta ki shi a take kuwa.

Ta mike za ta tafi, Hadi ya ce, “Yauwa amarya. Baki ce Allah Ya bani sa’a ba.”

Ta kalle shi kadan, “Allah Ya ba da sa’a.”

Ya nuna jin dadin sa, “Allah, Amin. Ina sauraron fitowar ki.”

Asiya ta iske Muhibbat tare da Amatullah, su na kwance kan gado. Muhibbat na tsakurin ta, ita kuma ta na kyalkyatar dariya, har da makaki. Dama a ce ita ke da damar yin wannan dariya a wannan lokacin?

Zuciyar ta dauke da nauyin dutsen dala ta nufe su. Ko da Muhibbat ta gan ta, ta ce, “Duba Minde, yadda yarinyar nan ke dariya. Tun dazu abin da mu ke yi ke nan. Da zarar na tsaya, sai ta fara kuka.” Ta ci gaba da yi mata wasa.

Asiya ta nisa. Za ta so a ce ta shiga layin su, amma abu ke gaban ta, wanda ya fi karfin ta. Me ya sa ne maza ba sa da kwakwalwar tunani ne? Kawai abin da zuciyar su ta so shi ke nan sai su aiwatar? Ga shi Hadi ya na neman jefa ta cikin matsala. Da ma yaya, balle sarki ya aiko?

“Dokta Hadi ne yazo...”

Muhibbat ya kalle ta sosai, “Likitan jiyan nan? Me ya faru kuma?”

KudiriWhere stories live. Discover now