Babi Na Talatin Da Biyu

3.6K 288 122
                                    

Ranar suna an yi taron walimar suna. Kusan kowa ya halarci wannan taro. Maza a waje, mata ta ciki. A nan ne aka yi wa’azi kan ladubban aure da zamantakewar sa, daukar ciki da goyon sa, sannan hakkokin iyaye da ‘ya’ya a kan kowannen su.

An ci, an sha, sannan an rarraba abin tsaraba kamar littafan addini, zannuwa wa mata da kuma turmin shadda wa maza. Akwai CD da a ka tsara, kan tarihin annabawan da a ka saka sunayen su wa yaran nan.

Cikin CDn, an nuna Harun, sannan a ka zayyana tarihin Annabi Haruna wanda ya yi rayuwa tare da dan uwansa Annabi Musa, sannan a ka nuna Harun karami da yadda a ke shirya shi, a ke ba shi abinci, a na mai ma sa fatan ya taimaka wa dan uwan sa kamar yadda wancan Harun din ya yi.
    Haka ma Annabi Yusuf.

Daga bisani a ka yi intabiyu da mahaifan yara da kakkanin su. Yusuf ya ba da tarihin kan sa da kuma yadda su ka hadu da matar sa Asiya. Ita ma Asiyar haka. Gaba daya kuma suka yi mu su addu’a da fatan alheri a rayuwar su. Kowane bako sai da a ka ba shi wannan CD don tunawa da su.

Hakan ya burge Muhibbat, wacce ta halarci sunan tun da sassafe. Ta rika shiga da fita, jikin ta na kamshi na musamman, yanayin fuskar ta na nuna hasken amarci. Dole ne ai, idan a ka yi la’akari da cewa kwanakin ta bakwai ne kacal a gidan miji.

“Mama Minde, ummin Aslam da Nurain. Jego fa ya karbe ki.”

Asiya ta yi dariya, ta na sanye cikin leshi ne mai tsadar gaske mai ruwan hoda da ratsin fari. Ga daham nan a makale a wuyan ta. “Ke fa Muhi ba ki da dama. Har yanzu ba za ki sassauta min ba?”

“Me na yi ma tukunna? Hmmm Allah Ya sa mu a danshin ku ke dai.”

Asiya ta kara dariya, “Cewa nake za kid an ci amarci tukunna kafin ‘ya’ya su zo?”

Ta harari Asiya, “An ce mi ki kowa irin ki ne? Ai ki jira ki gani.”

“Muhi, babu ko kunya?”

“Kunyar wa zan ji? Ke dai Allah Ya gyara rimi, cediya ta bar fushi.”

Hankalin Asiya ya tsaya sosai kan Muhibbat, ba bu barkwanci, “Me ya faru Muhi?”

Tabbas akwai matsala in a ka yi la’akari da yanayin muryar Muhibbat da fuskar ta, duk da dai murmushi ta ke kokarin yi,
“Ba bu. Ba abin da zai gagare ni bane.”

“Ki kara min bayani, don ban gane ba.”

Muhibbat ta yi murmushi mai fadi, sannan ta ce, “Ki shiga hankalin ki, kin fa san ni ce yaya babba.”

Muhibbat na kokarin kawar da maganar ne. amma Asiya ta san akwai matsala, wand aba zata yi saurin fada ma ta ba. ta fahimci hakan, ba wai fushi ta yi ba. kawai dai hankalin ta bai kwanta ba ne saboda Suhaima.

“Allah Ya kyauta Muhi. Amma na jiye mi ki tsoron Suhaima ne.”

Muhibbat ta dan yi dariya marar armashi, “Sai ka ce ni ba mace ba ce Minde? Ai na yi likimo ne na zuba ma ta idanu naga takun ta. Ba ta da wayo, don kwanakina uku a gidan ta fara sake makaman yakin ta. Ni kuwa ina kallon iya gudun ruwan ta ne kafin na saki boma-bomai na.”

Dariya Asiya ta ke yi har da kyarkyata. Ta dade ba ta ji dariya irin na lokacin ba. “Ki ce ta tako kulli ba ta sani ba.”

Muhibbat ta wulkita idanun ta, ta ce, “Ai Minde, rufin asirin mai loma kawai kar a yi walkiya. Amma an yi walkiya na gan ta.  Sati na daya ne, amma na riga na raina wa hankalin ta wayo. Ke dai a je zuwa kawai, wata rana za ki sha labari.”

Asiya ta yi murmushi, “Allah Ya kara kare min ke Muhi na, ta Dokta Hadi komai dozin.”

“Ke Minde, ashe kin yi baki ne haka?”

KudiriWhere stories live. Discover now