Babi Na Talatin

3.6K 297 50
                                        


Rayuwar duniya  juyi-juyi, wai kwado ya fada ruwan zafi. A daren jiya idan wani y ace da shi zai shiga wannan hali a yanzu zai musanta. Ko sau daya ma bai kawo hakan ba a rayuwar sa ta aure.

Hakika wannan ziyara da Mariya ta kai ma sa it ace ta haddasa ma sa fitinar da ya ke cikin ta. Ya shiga jin haushin kan sa.

Me ya sa ma bai fafare ta ba sannan ya kulle masaukin na sa bayan hakan? Me yasa bai gaya ma ta kalaman da su ka dace da it aba, wadanda za su hana ta mancewa da shi a tsawon rayuwar ta?

Ya nisa, a yayin da yake ta yawo a harabar gidan sa. Cikin dakin sa ya yi ma sa zafi, gami da kuma halin da Asiya ke ciki a lokacin. Ya san kuka ta ke yi amma ya fi ta bacin rai.

Asiya ba ta yarda da shi ba, hakan ke kona ma sa rai. Ko kafin auren sa ma bai yi abin da kalamanta ke zargin ya aikata ba. shi da yak e ganin ko da a ce a gaban ta ya aikata wani laifi za ta kawar da kanta, sannan ta ki amincewa da laifin?

Ya sake nisawa. Ba laifin ta bane, ban a Mariya b ace. Laifin sa ne, da ya mayar da rauywar sa abar sadaukarwa gare su, hakan y aba su damar juya shi son ran su. Daya ta Haifa ta gudu, dayar kuma ta aure shi amma ga yadda take zargin sa.

Amma zai ba su mamaki dukan su. Zai gwada mu su cewa shi ba kanwar lasa ba ne. Musamman ma Mariya, wadda ke neman raba ma sa aure sannan ta bata ma sa suna tare da lika ma sa babban tabo.

Ya tuno da abin da Asiya ta fitar daga jakar sa. Bireziya ce da kamfai a dunkule hade da kwalin kwaroron roba. Wannan ba bu ko shakka zai ruruta wutar zargi a tsakanin su, kuma babu mai haddasa hakan sai shaidaniya Mariya.

Shi fa da kan say a gama hada kayan sa. Zuwa kawai ya yi ya fitar da su a lokacin tafiyar ta su. Kuma a wurin da ya ajiye jakankunan a nan ya tarar da su.

Karo na fiye da kirgen say a yi nadamar barin Mariya ita kadai a cikin masaukin sa. Bai zaton za ta taba aikata hakan ba, musamman ga ‘yar uwar ta. Ko tausayin halin da take ciki ma ba ta ji ba.

Karar motar da ta tsaya a gaban get din sa ta ja hankalin sa. A sanin motar, ya san ta Hadi ce. Ya duba agogon hannun sa, karfe hudu da rabi na asuba.

Jikin sa ya ba shi, cewa ba bu lafiya. Don duk da cewa Hadi ya sake da shi ainun, ba zai yiwu ya zo gidan sa a wannan lokacin ba, alhalin ma a daren nan a ka kawo ma sa sabuwar amarya.

Bayan ya latsa ham, maigadi ya bude da sauri. Zama da likita, wanda ke fita a lokutan da ya yi bamban da na sauran mutane sun sa shi sabo da budewa da rufe kofar a kowane lokaci.

Hadi ya shigar da motar sa, amma bai fita ba har sai da Yusuf ya shigar da karnukan gidan sa cikin dakin su. Su kuwa sai haushi suke yi kamar za su daga motar ta sa.

“Me kake yi a nan?” Hadi ya nufo wurin da Yusuf din yake, bayan ya fito daga motar ta sa.

Ba tambayar da ya yi tsammani ba ne daga wajen Hadi. Don kuwa a duk ziyarar Hadi gidan sai ya yi ma sa mitar karnukan sa. Amma a ganin sa, kasancewar sa a harabar gidan sa a wannan lokaci ne zai sa Hadi yi ma sa wannan tambayar.

“Ina fata dai komai lafiya. Don ban yi tsammanin ka a yanzu ba.”

Bai tuna ko sun yi maganar zuwa aiki cikin dare ba, ko ma yin wa ta tafiya. Balle ma tun da ya zama CMD ba ya cika shiga hidimar tiyata sosai don ayyuka sun ma sa yawa.

“Na kira wayoyin ka kamar sau talatin ko ma fiye, amma ba ka dauka ba. Seriously, ba ka kai tsada har hakan ba.”

Yusuf ya kalle shi sosai, a yayin da ya ke la’akari da cewar ya bar wayar sa guda cikin dakin sa, kusa da gadon sa, wurin da jakar sa ke zaune. Daya wayar kuma ta na wata duniyar daban, a hannun Mariya.

KudiriOnde histórias criam vida. Descubra agora