Babi Na Ashirin Da Shida

4.2K 308 36
                                    

Yusuf ya na manne da kan waya a kunnen sa, ya ba da matukar hankalin sa a jiki. Bai dade ba da komai a rayuwar sa ke tafiya sumul. Amma a yanzu komai ya birkice.

Mariya ta dauki Amatullah, Yafendo ta tabbatar ma sa da sakon nasarar takun sakar farko. Don ta yi alwashin mallakar dukiyar jikar ta!

“Na fahimce ka.”Yusuf ya furta wa wanda su ke maganar ta waya. “Babu gudu. Zan aiwatar da duk abin da na yi kudiri, ba gudu ba ja da baya.”

Ya dan kara saurare, sannan ya gyada kan sa, “Kar ka damu da wannan. Na san yadda zan yi da al’amarin. Na gode.”

Daga nan ya ajjiye kan wayar, ya kalli Hadi, wanda ke zaune tun farkon wayar ta sa, ya na fuskantar sa cikin ofis din sa. “Mun gama.” Kawai ya sanar da shi.

Hadi ya ce, “Are you sure, ka tabbata kan kudirin ka?”

“Its the only way, abin da ya fi dacewa ke nan na yi. Ka fi kowa sanin ba damuwa da Amatullah dukan su su ka yi ba. Dukiyar ce ke jan su. Duk da ina son tsirar da mutuncin mahaifina, ba zan bari wasu su hau kan dukiya ta don su lalata rayuwa yarinyar ba. So, tilas na janye duk wa ta yarjejeniyar da mu ka yi, wanda na amince kan biyan kudin wasiyyar sa domin na cika ma sa.

Na amince da shawarar lauyan Alhaji da ma manajan bankin da ke rike da dukiyar tuntuni, kan a sayar don a karasa biyan basussukan da ya karba. Sauran abin da ya rage sai a raba gado wa magada. Zancen wasiyya kuma, mun warware ta gaba daya. So su na iya kai wa duk wurin da su ke da niyya. Ba bu yadda suka iya.

“Ita kuma Amatullah sai na bude sabon account da sunan ta, na zuba ma ta wasu kudade a ciki na boye. Duk da ba ni na haife ta ba, zan iya yi ma ta wannan kyauta, don kuwa na san ko yau na mutu, ba ta da gadona.”

Hadi ya nisa, “Shin ka yi shawara da Ummah da Asiya game da niyyar ka?”

“Me ka ke gani? Tun jiya na tara su duk na kuma sanar mu su da komai.”

“Ka na ganin shawarar nan ba zai shafi Amatullah ba ta hanya marar kyau?”

Wannan karon Yusuf ne ya nisa, “Mu na fatan kila in sun ga abin ba yadda su ke zato ba ne, za su mallaka ma na Amatullah a karshe.”

Hadi ya gyara zaman sa, “Kar ka rudi kan ka. Ka fi kowa sanin Yafendo. Idan har ba ta samu abin da ran ta ke so ba, to kai ma lallai ba za ta ba ka abin da ka ke so ba. A karshe Amatullah ce za ta sha wahala.”

Yusuf ya fi kowa sanin haka.Ya kuma san cewa samun kudin ba shi zai kare Amatullah daga shan wahala ba. Duk daya ne wajen su Yafendo. Don ba su san da kowa ba, sai kan su.

“Ba su kudin da rashin ba su duk daya ne, Hadi. Amatullah dole ta sha wahala wajen su. Shi yasa na yi kudirin hana mu su komai, don na tabbata gaba za a zo babu kudi, babu kaunar Ama. Ban san gaibu ba, amma ina fatan Allah ya kawo ma na saukin kawai.”

Hadi ya nisa, “Amin.” Sannan ya tambaya, “To, ya ya Asiya ta ke ji a yanzu?”

Sake ambaton matar sa ya sa shi jan numfashin sa cikin huhun sa, ya fitar a hankali. Yau kwana uku ke nan rabuwar su da Amatullah, amma har yanzu ba ta sake ba. Ba ta ci ko sha, har sai an tilasta ma ta. Ya yi kokarin danne na sa zuciyar don ya kwantar ma ta da na ta. Amma abin ya ci tura.

“Asiya na iya kokarin ta na shanye abin. Amma yadda ta ke ji ne ba zan iya fassarawa ba. Zafi ne da uwa ce kadai ke iya jin sa, in an raba ta da diyar ta.”

Tunanin Asiya ya kara mamaye shi. Ba ya son sake komawa gida ya tarar da ita cikin halin da ya bar ta kafin fitowar sa. Ya ma ta magana, kuma ta yi ma sa alkawarin za ta ci abinci. Dazu ma waya ta ma sa, ta sanar da shi ta ci abinci, don kawai hankalin sa ya kwanta.

KudiriWhere stories live. Discover now