Babi Na Biyu

5.5K 362 55
                                    

Da wannan ta tura daya daga cikin manyan gilas na kofar shiga, wadda ta kai ta zuwa ga wata farfajiya babba mai dauke da kujerun zama ma su tarin yawa masu fuskantar gabashin dakin. Cikin da sanyi amma ba sosai ba.

Wata kila don tiles din da ke baibaye da kasan ne ko kuma iyakwandishan din da ke kunne. Kamshin Dettol ya riski hancin ta.
Akwai wani kabet babba, wanda da gani takardun fayel fayel ne dankare cikin sa, sannan ta lura da wata ma'aikaciyar da ke zaune a bayan wani makeken ginin da aka baibaye saman sa da duwatsu masu sheik na marbles launin ruwan kasa. Ta nufi wajen ta, ta lura da silin din da ke wajen na zamani ne wato POP.

Ta dan tsaya muhawarar yin sallama wa nas din nan, wadda da ganin kalar ta ba bahaushiya ba ce. Karshe dai ta yi ma ta sallamar. Ganin ba ta dago kan ta ta kalle ta ba, ya sa ta ci gaba da cewa, "Ina son ganin Dokta Yusuf ne."

"Ki na da appointment ne?" Nas din ta tambaye ta cikin murya kasa-kasar da sai da ta dan duka sannan ta ke iya jin ta.

Ta amsa, "A'a. Daga Dagauda na zo ganin sa."

Nas din, wadda sunan da ke sakale a gaban aljihun ta ya nuna Bridget, ta ce, "Kawo takardar da a ka turo ki da ita daga can asibitin garin naku."

Asiya ta ji zuciyar ta ta zo bakin ta. Ba ta yi tsammanin samun matsala ba. Don haka dai ta amsa da cewa, "Ba daga wani asibiti na zo ba. Zuwa na yi don na gan shi."

Bridget dai ba ta daga kai ta kalli Asiya ba har a lokacin, rubutun ta kawai ta ke yi, "To za ki bude fayel a nan. Za ki biya kudin a wancan dakin da ke kallon nan."

Da yatsar ta ta nuna wa Asiya wata taga, wato window wadda wani namiji ke zaune kan tebur a ta cikin sa. Ta lura an rubuta 'Cashier' a saman sa. Ta tsaya yin muhawara cikin zuciyar ta. Shin ta sayi katin da zai ba ta damar ganin sa ne ko kuwa? Ita dai lafiyar ta kalau, magana ce kawai ta je ma sa da ita mai karfi. Ba ta kuma da lokaci a tare da ita. Sayen katin ba zai bata ma ta lokaci ba?

Ta yanke shawarar fadin gaskiya wa Bridget, "Ni ba na da wata cuta. Ina son ganin sa ne kawai."

A lokacin ne Bridget ta dago ta kalle ta, "Sorry, marasa lafiya ne kadai ke iya ganin sa a nan. Ko ki bude fayel, ko ki neme shi ta wani waje." Muryar ta dauke da umurni, fuskar ta a daure.

Asiya ta shiga roko, "Don Allah na roke ki. Wallahi wata muhimmiyar magana na zo da ita. Ba zan dade a ciki ba, na yi miki alkawari."

Bridget ta sake kallon ta, wannan karon sama zuwa kasa, sannan ta koma fuskar ta. Ta lura da yadda ta tsuke fuskar ta, "Duba malama, nan tun safe mutane ne ke zaune sun a jiran ganin sa. Ta yaya zan bar ki ki gan shi haka kawai? Balle ma ba ya nan asibitin. Ya fita."

Ta na gama furta hakan ta dan ja tsaki sannan ta ci gaba da rubutun ta, ko kallo ma Asiya ba ta ishe ta ba. Da farko dai kamar ba zata yarda da maganar ba, amma Asiya ta san ba ta da wata madafa illa ta yi hakan.

Ta shiga tunanin yadda za ta yi. Ga alama hanyar da ta biyo ba za ta bille ma ta ba. Sai fa idan za ta koma gida can garin su, ya kasance ta yi zuwan banza kawai.

Gida. Dakata. Idan an hana ta ganin sa a nan asibitin ai ba za a hana ta ganin sa a gidan sa ba. Nan take ta ji wani abu ya tokare ta mai kama da tsoro, amma ta matse. Ba tare da wani tunani ba ta sake neman taimakon Bridget, kan ta yi ma ta kwatancen gidan na sa.

Wannan karo kam hararar ta tayi, ta sake yi mata kallon biyu-taro uku sisi. Kai tsaye ta ba ta amsa, "Ban san gidan ba, amma na san a Kandahar ya ke."

Muryar Bridget na nuna kyama, idanun ta dauke da kallon raini. Amma Asiya ba ta ji haushin ta ba. Ba za ta ga laifin na ta ba, don wata kila an sha zuwa neman na sa kamar yadda ta ke yi. Ta dai yi godiya sannan ta yi ficewar ta.

KudiriWhere stories live. Discover now