Babi Na Sha Bakwai

4.6K 349 88
                                    

Assalamu alaikum. Afwaan! I promised to give an update since yesterday, but I couldn't. So today, I will give a double.😀

Yes, I know. It is because you all are awesome. And I love you loads. 😘😘💗



Yusuf yayi kasake tambayar ta na shigar sa a hankali. Hakika, ta fi shi shiga tashin hankalin rabuwa da Ama. Don haka ne ma tun dazu take zaune cikin fargabar rabuwar su. Ba wai don tana tsoron fuskantar duniya ba ne, sai don rabuwar za ta zame mata tashin hankali.

Sai ga shi ya zo ma ta da zancen tsohuwar soyayyar sa, wacce ya nuna alamar ta na da matukar mahimmanci a rayuwar sa har a lokacin. Watakila shi ya sa shi ya furta auren su na wucin gadi, tare da bata damar rabuwa a lokacin da take so. Yanzu ne damar ta, na ganin ko zai cika alkawarin sa ko zai saba?

Amatullah ta yi motsi a lokacin, gaba daya suka mayar da hankalin su zuwa gare ta. Motsin mika kawai ta yi, ta koma ta ci gaba da barcin ta. Kowannen su da abin da ke ran sa. Allah sarki! Ga ta dai ba diyar su ba ce, amma ta hada su zaman aure kuma a dalilin rashin ta, auren su zai iya fuskar ta barazana, wadda a yanzu ba ta shirya wa ba.

Bayan kamar zamani mai tsawo, ya ce da ita, “Ina ganin ya dace mu yi abu daya bayan daya. Farko, mu gama da matsalar da ta same mu a yanzu, kafin mu yi tunanin wata.”

Daga nan, ya tsaya jikin Amatullah tare da shafa ma ta kumatun ta, sannan ya sake kallon Asiya, “Idan kina bukatar wani abu a ko yaushe sai ki sanar da ni. Sai da safe.” Daga nan ya yi ficewar sa.

Ta zuba wa bayan sa idanu. Ba ta san ta rike numfashin ta ba, sai da ya rufe kofar bayan ya fice daga dakin na ta. Ta nisa. Ya ce idan ta na bukatar wani abu ta sanar da shi. Ga amsar da tafi bukata, amma ya zille ya ki badawa.

Ita ma kan ta, idan ba karya za ta yi wa kan ta ba, zuciyar ta ba son jin amsar take ba. Amma dole ta yi wannan tambayar. Ta san dole ne rabuwar su ta yi kusa, idan har a ka raba su da wadda ta yi dalilin auren na su. Tabbas, Yusuf ba zai bukaci komai daga gare ta ba.

Yusuf ya bata zabi, cewa idan ta na so, ta yanke alakar su. Don haka, da zarar ta furta hakan, to fa ba makawa, a tsammanin ta, zai cika alkawarin da ya dauka.

Ta sake nisawa, tare da kallon Amatullah. Kan ta a daure ya ke. Ta na fatan da a ce ita ce wannan jaririyar, wacce ke kwance abin ta, ba ta san me duniya ke ciki ba.

A lokuta irin wannan, ta kan mike ne ta yi sallolin dare, ta fada wa Allah damuwar ta, ta kuma yi fatan samun alheri bisa jagorancin Sa. A wannan dare ma ba ta yi barci ba. Ta yi kusan kwana ta na raya daren da nafilfili da karatun Al-kur’ani. Lokaci-lokaci Amatullah kan katse mata idan ta farka. Bayan ta ba ta madara ko kuma ta rarrashe ta, sai ta koma abin ta. Ita kuma ta koma abin da ta ke yi, har a ka kira sallar asuba.

Bayan ta idar da sallah ne ta yi zikirin ta, idon ta na kan Amatullah. Son ta kara bulbula ya ke cikin zuciyar ta, abin har ba ta tsoro ya ke yi. Ga rabuwa ta zo, ga shi kuma sai son ta ke karuwa. Wata kila hakan alheri ne?

Ta nisa. Ta bar komai a hannun Allah, don Shi ne Buwayi, Gagara misali. Shi Ya nufe ta da shiga rayuwar Ama, don haka idan rawar da za ta taka cikin rayuwar ta ta ta zo karshe, babu yadda ta iya. Da wannan ta mike zuwa kicin, don hada wa Amatullah madarar ta. Wanda ta hada sun kare, kuma za ta iya bukatar sha da zarar ta tashi. Hakan ma zai bata damar rage tunani da radadi daga cikin zuciyar ta.

Motsin da ta ji a kicin ya sa ta kalli agogon falon, karfe shida saura kwata. Duk da cewa Larai ta kan tashi da wuri, ba ta shiga madafi kamar yanzu. Ita kan ta dai ba karyawa da wuri ta ke ba.

Wasu lokutan ma ta kan ci abincin safe a matsayin na rana ne. Shi kuma Dokta Yusuf bai cika zama da safe ba, yawanci a asibiti ya ke. Umma kuma ba ta nan. Don haka Larai ta kan yi kaye-kayen ta ne na wasu bangaren gidan, sai kamar hantsi ta fita su gaisa.

KudiriWhere stories live. Discover now