Babi Na Ashirin Da Daya

4.2K 320 75
                                    

Hello dearies 😘😘. I am very sorry for the late update. I lazy around on weekdays but weekends are usually busiest for me. I would love to give double updates today, although I am still thinking about it.  But I hope you like this. Love all of you😘😍😘





Da nauyin zuciya Asiya ta fita, don ba ta son haduwar ta da Suhaima ko kadan, musamman ma a yanzu da ta kasance ita kadai ce wajen Dokta Hadi.

Ba wai sun taba sabani ba ne. Kawai kaunar matar ce kawai ba ta yi. Ta san ita din ma ba son ta ta ke yi ba, duk da kokarin nuna hakan da ta ke yi.

Ilay! Ko da kofar gaba ta bude, ba Suhaimar ta gani ba. Muhibbat ta gani. Ta fito cikin sauri ta je ta rungume ta. Zuciyar ta ta yi kaaal don ganin ta. Oh! Yaushe rabon da ganin ta? Tun fa bayan auren ta.

“Muhi, ashe zan sake ganin ki?” Kwalla su ka ciko wa Asiya idanu. Ji ta ke tamkar ta ga Dadar ta. Ko ma Mariya. Nan take ta ji raas! Ko dai mariya c eta bayyana a gida?

“Ai ke ba kya da kirki. Ko ki dan waiga gida sau daya?” Ta kalli Yusuf wanda ya gama musabaha da Hadi, ta ce, “Mhmmm, ka samu amarya ka wani makale ta a gefen ka, ka hana ta zuwa kauye... to yau na zo ma ka da tuhuma ce, dole ka amsa.”

Yusuf ya yi murmushi, “Ba dole na ba. A ce ta hannun damar amarya ta zo da kan ta, ai dole ne.”

Duka suka kyalkyale da dariya. Asiya ta kalle shi cikin mamaki. Ashe a wancan ranar sayen bakin nan ya saurare su. Ta yi zaton bai damu da abin da abokan na sa ke yi bane. Ko kuma auren bai dame shi kamar yadda yake nuna ma ta a yanzu ba.

Bayan ta gaida Dokta Hadi, sai ya ce, “To, ta hannun damar amarya, ni zan koma. Tun da na danka ki hannun mutanen gidan nan, na sauke nauyi.”

Ta yi dariya, “Gaskiya, ka fita. Na gode sosai. Sai wata rana.”

Hadi ya kalle sosai, “Sai wata rana kuma? Ta ya ya haka? Ina ‘yar malelen da a ka kwadaita min a biki na?”

Muhibbat ta sake fashewa da dariya, “’Yan Bauchi kauyawa ne. Dan-malele a ke fadi, ba ‘yar malele ba.”

Asiya ta shiga maganar, “Haba, Muhi. Ki na magana kamar wani dan-malelen wani kayan gabas ne.”

Hadi ya ce, “Kyale ta amarya. Na ga alamar ta raina wa mutanen Bauchin ne. Kuma ga shi ‘yar Bauchin ce ita, gaba da baya. Ba ta da wurin da ya wuce nan nan din idan Kanawa koro ta.”

Muhibbat ta ce, “Duk da dai ni ‘yar jihar Bauchin ce, babu abin da zai kawo ni nan, idan ba dole ba.”

Hadi ya ce, “To, tun da dole ne ya saka hakan, an kara zama daya ke nan. Gobe in Allah Ya kai mu, zan dawo na ci dan-malele na ke nan.”

“Tab, ai gobe da yamma ko kura ta ba za ka samu ba. Na yi nisa.”

Ya kalli Asiya, “Amarya, ban san mutanen garin ku su na da rowa ba.”

Asiya ta yi dariya, “A’a, ba ma da rowa.” Ba ta san abin da zaata ce masa ba, don ga alama, sun dan yi jayayya ne tun a motar sa.

“To in dai haka ne, ya kamata na ci dan-malele.”

Muhibbat ta girgiza kan ta, tana ‘yar dariya. Ba ta sake cewa komai ba, kawai shigewa ciki ta yi. Asiya ma ta bi bayan ta. Bature direban gidan ya bi bayan su da jibgegen buhun da ta zo da shi.

Nan suka yi sallar maghrib, Yusuf da Hadi kuwa masjid suka koma suka yi na su. Ta san daga can Hadi zai wuce ke nan.

“Ina ki ka samu Dokta Hadi, Muhi?” Asiya ta tambaye ta, bayan sun idar da sallah. Tun ganin su tare ta ke kaikayin yi mata wannan tambayar.

KudiriWhere stories live. Discover now