Babi Na Sha Hudu

4.4K 342 126
                                    

Asiya ta zuba wa bayan sa idanu har ya bace. Ta rufe kofar dakin ta sannan ta jingina da jiki, ta dafe kirjin nata da hannun ta. A lokacin zuciyar ta ta kumbura cikin kirjinta ta yi mata nauyi, sannan ta shiga bugu da sauri. ‘Asiya’ fa ya ce….karo na farko ke nan da ya kira sunan ta.

Tun bayan auren su, bai taba yi ma ta magana tsawo ba kamar na wannan lokacin. Har ma ya kira sunan ta. Ba wai hakan ne ya mata dadi ba, yadda ya ambata ne ya ruda ta. Sannan kuma ya bukaci nan gaba ta kai ma sa abinci da kan ta. Nan gaba….ta shiga jin dadi saboda ya yabi girkin ta, sannan ya bukaci ta ci gaba da yi, kamar dai matar sa.

Nan ne kuma ta dakatar da zuciyar ta, ta lalumo zahiri kan ta ya bar shawagi cikin sararin samaniya. Ita matar sa ce, amma ta wucin-gadi. Ya aure ta ne don ta kula ma sa da Amatullah.

Me ya same ta ne? Dan abin da ya faru ne zai sa ta shiga wannan hali? Girki ta yi ma sa, irin wanda ran sa ke so. Idan bai nuna farin cikin sa ba, me zai yi?

Ai ba wani abu ba ne, kawai ya yi kokarin nuna jin dadin sa ne game da wahalar da ta dauka na yi ma sa abincin. Kamar yadda take zaton shi ma yake nuna mata jin dadi game da kula ma sa da Amatullah da take yi.
Ta yi sauri ta matse zuciyar ta, lokacin da ta tuna da yadda ya kalle ta kafin ya bar kofar dakin na ta.

Ta sake matse idanun ta a kokarin ta na cire yadda shigar sa ta yi ma sa kyau matuka. Yadda rigar sa ta bayyana faffadar kafadun sa da cikar hallitar sa, da yadda gashin bakin sa da ya fito ya bayyana tsarin fuskar sa, zuwa ga yadda gashin kan say a ke taje fes…..

Kai! Ta bude idanun ta cikin sauri. Da gaske ne, ta na bukatar a duba kanta. Ta yaya ma a ka soma hakan? A ce wai duk ta lura da wannan a dan tsayuwar da yayi ba da dadewar nan ba?

A’a ba zai yiwu ba, tilas ta canja akala. Yadda shi bai saka rauni a zuciyar sa ba, ita ma ya dace ta fitar da wannan shirmen daga kan ta. Idan bah aka ba, to za ta iya fadawa wata masifar ta daban. Babbar masifa!

Da wannan kudiri ta jera tsawon ta na ma sa girke-girke kala kala. Tun ta na neman taimakon Sara har ta gwanance a kai. Sara ta mallaka mata littafan kirke-kirke irin na gida da na waje, har da My Kitchen Essentials na Azizah Idris Gombe. Tun daga lokacin ta ji Azizah ta fara burge ta don tsantsenin ta da basira.

A kullum Dokta zai ci abincin ta. Ko da rana ko dare, a duk lokacin da ya samu damar hakan. Sai dai bayan gaisuwa ba ya tambayar ta komai bayan lafiyar Amatullah.

“Gobe idan Allah Ya kai mu za ki kai Amatullah asibiti don allurar riga-kafin sati shida.”

Asiya ta daga kai daga zuba ma sa ruwan sanyin da take yi cikin kofi bayan ta jera masa abincin sa. burabusko ne da miyar danyen kifi.

A kwana a tashi ba wuya. Wai har sun yi arba’in. Ikon Allah!

“Allah Ya kai mu.” Kawai ta ce da shi.

Har ta juya za ta tafi ta ji furta, “Zauna mana.”

Ta kalle shi sosai, “Na’am?”

Ya dan kalle ta, “Please, ki zauna, akwai wata muhimmiyar maganar da na ke son mu yi.”

Ta zauna a hankali tare da hadiye yawu da kyar. Zuciyar ta bugu take yi ta na tsalle. So ta ke ya yi yagama fadin abin da yayi niyya tun kafin ta suma. Duk da cewar tana kokarin kauce ma sa, ta kan sa ran ganin sa kullum tare da ba shi abinci. Ta tsinci kan ta a cikin jiran lokacin da za ta ga ya saka lomar farko cikin bakin sa, da yadda zai nuna godiyar sa ko da ta kwayar idanu ne.

“Abokanai na kuma aminai na, Hadi da Sadi, sannan kuma abokin aikina Dokta Kabir suna son su gabatar da matan su don ku gana sosai. Kamar dai ziyarar suna su ke nufi. Sannan hakan zai sa Sadi ya kyale ni na huta.”

KudiriDonde viven las historias. Descúbrelo ahora