Tun da karfe shida Asiya ta gama shirin ta, ta zauna cikin dakin da ta kwana jiya. Ita da ma tun can ba mai barcin safe ba ce, sannan ta saba da kaye-kaye.
Sai dai a wannan lokacin ta zauna ne jiran aiwatar da hukuncin da Umma ta yanke game da maganar da ta zo mu su da ita.
A yanzu da ta fuskanci Dokta, tambayoyi ne cike da tunanin ta fiye da amsoshi. Shin zai yarda da laifin da ya aikata, ko zai ci gaba da musantawa?
Me zai faru daga yanzu: tsakanin Dokta da Maree; tsakanin ita kan ta Asiyar da Dada; tsakanin mahaifin su da su; tsakanin Mudassir da Maree; tsakanin gidan su da mutanen garin su?
Ba zata iya cewa akwai nasara tattare da tafiyar nan da ta yi ba. Amma ko da hakan ma, shi ma Dokta Yusuf zai yin a sa irin hasarar, ba su kadai ba.
A kalla hakan ta so ya faru tun farko. Ta yi hakan ne don koya ma sa darasi, ya san nan gaba cewar su ba kanwar lasa ne bane, ba zai mayar da Maree gangar da zai ci moriyarta ya jefar da kwauren ba. Kuma ko da nan gaba ne, ba zai kara yin hakan wa wasu abin da ya aikata wa Maree ba.
Ta nisa. A can cikin zuciyar ta, za ta so a samu maslaha game da wannan matsalar. Za ta so a ce likitan nan ya amince da wannan ciki a matsayin tsautsayi, ya tausaya mu su gaba daya, ya auri Maree da zarar ta haife abin da ke ciki. In ya so sai a tsara cewa ta koma Jos da zama har zuwa lokacin da za ta haihun, shi kuma Mudassir a ba shi hakuri, a mayar da kayan sa.
Mafarki ne da ta san zai yi wuyar faruwa. Amma ai ba a hana ganin sa ai ko? Sai dai ganin mafarki alhali ba barci a ke ba bata lokaci ne, kamar yadda ta ke ganin wannan kudirin na ta. Amma it aba mai saurin karaya ba ce. Za ta tsaya ta ga abin da zai faru.
Tare da sallama mahaifiyar Dokta ta shiga dakin da take, ta na daure da atamfa mai launin ruwan toka da ratsin ja. Da shigar ta kamshin ta ya mamaye dakin.
Ta kalli Asiya, fuska a yatsine, ta tambaye ta, “Me ya sa ba ki kwanta kan gadon ba? Ai kuwa ba ki huce gajiyar jiyan ba.”
Asiya ta durkusa cikin ladabi ta gaishe ta, sannan ta amsa, “Nan din ma ya wadatar.”
Hakika, kasan kilishin da ked akin akwai taushin gaske. Da ma ita tun can kan tabarma ta saba kwana, don haka gado ya sha zaman sa. Ya ma fi karfin ta. Ita dai alla-alla take yi ta ji abin da Umma ke tafe da shi.
“Na ga kamar kin shirya, ko?”
Asiya ta gyada kan ta, “Eh, na shirya Hajiya.”
Umma ta yi murmushi, “Umma za ki kirani. Larai za ta kawo miki kalaci. Ni kuma zan je na yi shiri, don zamu je tare da ke har can garin naku, domin mu taru mu samo maslahaa baki daya. Ko yaya kika ce?”Zuciyar Asiya sai bugawa take yi da sauri. Za a so hakan, amma ba za ta so ba. Saboda zuwa hakan da Umma kwatsam zai iya haddasa babban damuwa tsakanin ta da Dada. Amma idan ta ki kuma za a ga rashin gaskiyar ta. Don haka ta amince. Komai zai faru kam sai dai ya faru, don ta riga ta shiga har wuya, babu halin fita ko ja da baya.
Larai ta kai mata lafiyayyen sinasir da miyar naman rago zako-zako, hade da ruwan shayi. Shayin kawai ta kurba, don du’a’i sun cika mata cikin ta dam. Roko ta ke yi, tare da cikakken fatan komai zai zo cikin sauki.
Karfe bakwai da kwata Umma ta sa Larai ta kira ta, kan ta fito su tafi. Ta fito ta iske ta canja kayan jikin ta zuwa ga wani leshi mai kyaun gaske launin ja da zaren gwal. Ga daham nan a wuyan ta wandaa ke zikirin nera.
Ta rufe jikin ta da gyale babba amma na yayi. Hannun ta da munduwa guda biyu manya. Ta tabbata su ma gwal din ne. shi yasa shekarun ta bas a nuna wa. Ga dai Asiya ce yarinya, amma sai ta ga kanta kamar ta saka ganye ne a jikin ta ba sutura ba.
Da suka fita waje, daya daga cikin jerin motocin da ta gani a jere jiya ne ta gani dab da bakin kofar fita daga gidan. Motar a kunne take, ga alama direban ya shirya ne ya na jiran su.
YOU ARE READING
Kudiri
RomanceHausa story of love, commitment and sacrifice. Yusuf and Asiya belong to different classes with nothing in common. Well, except for humanity. An incident had occurred which brought them together. Will their shared sacrifice bring them happiness and...