* * *
Yusuf ya kalli Larai wacce fuskar ta ke nuna zakuwar ta na son ta je ta huta. Idan an duba ta na da gaskiyar ta. Ta ce da shi, “Ina ga ta kwanta ne fa. Don na dade ina bugawa amma ba ta amsa ba.”Yusuf ya gyada kan sa, ba don ya amince da hasashen Larai ba ne, sai don ya kyale ta ta je ta huta ita din. “Shi ke nan, je ki yi aikin. Zan dauka daga nan.”
Ta yi ma sa godiya sannan ta koma bangaren da a ka ware mata daki cikin sa, ta lume shiru. Ya kura wa kofar dakin Asiya idanu wanda ke rufe gam. Kwanaki biyu ke nan da dawowa daga taron su. Shi da ita ba su zauna na minti biyar tare ba. Hasali ma tun daren jiya, rabon sa da ganin ta.
Ya mike tsaye ya shige dakin sa. Ya san abin da ya dace ya yi. Dole a yau ya gana da ita, don kuwa ya san ba kwanciya barci ta yi ba. Wane irin barci ne za ta fara da karfe takwas na dare?
Ya shiga dakin sa ya nufi kofofi biyun da ke hannun riga da juna. Guda daya na shiga bandakin sa ne, guda kuwa, kai tsaye zai shiga bangaren saka kaya na dakin Asiya, wato closet. Bai taba amfani da kofar ba, don kuwa damar yin hakan ba ta samu gare shi ba. Ya tuno da irin jayayyar da ya yi da Sadi a lokacin da ya bayar da shawarar fasa kofa a wajen.
A cewar Sadi, kyaunta shi da matar sa su rika shiga da fita ba tare da sun fito falo ba. Wai hakan ‘Romantic’ ne. Yusuf bai ga romantic a nan ba. Ya dai amince ne a wancan lokaci don Sadi ya kyale shi. Har a yanzun ma bai gani ba. Tukunna.
A kasa ya iske Asiya, bayan ya shiga dakin ta. Ya yi mata sallama. Ta dago fuskar ta wanda ke manne da gwiwar ta, idanun cike da tsoro da fargaba, da mamaki. Ta na kallon sa tamkar kunnuwar sa sun yi girma fiye da tsawon sa, ya tsiro da kaho da fuka fukai.
Cikin tsananin kaduwa, ta tambaye shi, “Ta ina ka shigo?!”
Ya dan yi murmushi sannan ya zauna a gaban ta, a kasan, ya amsa, “Ta kofa.”
“Ta ya ya a ka yi hakan bayan na kulle kofar?” Ta kura wa kofar dakin idanu, sannan shi.
Ganin fargaban ta ya sa shi neman hanyar da zai kawo ma ta sassauci, ya ce, “Idan Allah Ya sa a ka rufe ma ka kofa, sai Ya bude maka wata kofar daban.”
Ta sake kallon kofar dakin ta, har lokacin makullin sa ya na sakale da shi. Ya gyara muryar sa ya ce, “Kwantar da hankalin ki, akwai kofar da ta hada daki na da naki ta closet. Ta nan na shigo, don kuwa na turo Larai ta kira ki har sau hudu, amma kin ki amsawa balle ki fito. Shin a ganin ki, hakan ne zai kawo mana masalaha ko me?”
A wannan lokaci ne ya ga rudani da kaduwa sun gushe daga idanun ta, kunci da bacin rai suka mai da gurbin su. Ta kife fuskar ta sannan ta nisa, “Ban amsa ba ne…” ta dago ta kalle shi, “…don ban san abin da zance ba. Kwakwalwa ta a birkice take, zuciya ta a cikin rudani. Ban san ta yadda zan fara ba.”
Ya kara tausaya mata ganin irin kuncin dake cikin su da rauni. Kiris ya rage ya ja ta zuwa jikin sa har sai wannan kunci ya gushe. Amma yin hakan ba zai taimake su a ba a lokacin. Ya ce, “Shi ne ki ka boye kan ki? A ganin ki yin hakan ya fi?”
“Addu’a na ke yi domin neman Jagoraci da Yardar Allah na. Duk abin da Ya zaba min zan karba da hanu bi-biyu.”
Ya sauke muryar sa sosai, “Amatullah ba mutuwa ta yi ba.”
Ta kawar da kan ta daga fuskar sa, ta ce, “Na sani. Amma gobe za ta tafi wajen kakar ta.”
Ya hadiye yawu amma makogwaron sa a bushe ya ke. Tun da Mariya ta haifi Amatullah bai taba rabuwa da ita ba, ko da na awa guda ne. Nan ma sai ko in aiki ne ya nisantar da shi daga gare ta.
Ya tuna ranar da ya mata huduba, da irin sadaukarwar da ya yi domin ta. Amma a ce wai za a raba shi da ita? Ya san dai tilas Asiya ta ji zafin rabuwar su, amma bai kamata ta ga kamar rabuwar ba zata dame shi ba.
YOU ARE READING
Kudiri
RomanceHausa story of love, commitment and sacrifice. Yusuf and Asiya belong to different classes with nothing in common. Well, except for humanity. An incident had occurred which brought them together. Will their shared sacrifice bring them happiness and...