🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 02. 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆
K A *2* Ya dan daga kafadanshi alamar ko oho, ya ajiye a kujerar gefenshi sanan ya kunna mota ya dau hanya. Yana yin horn maigadi ya wangala mishi gate kasancewar horn dinshi mai sanyi shiyasa maigadi ke saurin ganewa ba tare da ya bude ya leka ba, ya samu waje a harabar gidan yayi parkin,ya sauko da littafin a hannun shi. Ball aka jefo shi dashi yayi saurin cafkowa kan ya dokeshi, dukkansu biyar suka taho wajenshi a guje suna bashi hakuri farida tace "yaya please ka bamu ball din wasa muke Ahmad ne ya wurgo maka wai ko zaka iya chafewa" yayi murmushi, dukkansu sanye suke da jerseys iri daya mara sa hannu da wandunan su sai fararen t shirts da suka saka a ta ciki masu guntun hannu, farida da hanifa duk akwai huluna akansu wanda kashedin yayansu ne akan kada su kuskura koda wasa ya dawo ya tarar da kan kowaccensu a bude. Yace "zan baku amma nima sai nayi one round kun yarda?" yuzarsif yace "ah ah yaya bamu so yanzu kana shiga sai ka gwasale mu don ka fimu iyawa" hanifa tace "yes yaya kayi, ai kana grup dinmu neko" yace "idan bana grup din auta ai bazan ma joining din kowanne grup ba" mu'azzam yace "muje zuwa ai mai gudun mutuwa shine gawa ta fari" takalmanshi ya cire a wajen suka runtuma cikin basket ball court din. Kasancewar shi mai tsayi da kakkarfar jiki shiyasa yake mugun son basketball, its his hobby a sanadiyyar shi ma baban su yasa akayi musu wajen bugawa a gidan har ya kawo kowa ya soma son game din. Cikin kiftawa da bismilla har ya musu zillo ya sakala ball din a cikin ragar sa, yan matan duk suka dau sowa "sai yaya! Sai yaya!" yuzarsif yace "kagani ko mu'azzam ai shiyasa naki amincewa" umar yace "yuzarsif zo nan, ni ba ta game nake ba. Gashi mukullin motana ka kaishi wanki naga dan ladi baya nan kuma bazan iya jiran shi ba, akwai kudade a cikin hand rest a motan wanda zasu ishe ka amfani ka dawo mun dashi kana gamawa don akwai inda zani, hope u get me" ya gyada kai ya nufi cikin gida. A falo ya tarar da mami a zaune tana kallon sunna tv ya baje a kan kujera yana nishi sanan ya gaida ta, ta amsa a ciki ciki yayi saurin kallonta "mami me kuma nayi ne" "ai kafi kowa sani what the use of asking" ya hannayen shi biyu alamar roko "mami wlh ban sani ba, naga lafiya lau muka rabu dake da safe" "umar kanaso a kodayaushe mu dinga batawa da kai akan magana daya ko? Kai kenan kullum sai an maka fada akan abinci sai kace ahmad? Inafa sane da kai rabonka da abinci tun jiya sanan nasan fitan nan dakayi baka ci komi ba don halinka na tsantsani baka son abincin restaurant to gaya mun me kaci?" yayi murmushi "mami na kenan, to yi hakuri kinji yanzu ma kuwa zanci, mami ai zaki zubo mun ko" ta harare shi "bazan zubon ba kar kaje ka deba ka jirani" ya rike cikinshi kaman yana ciwo ya soma "wash mami cikina,mami yunwa mami abinci,mami zan mutu " da sauri ta mike tana kwalawa farida kira ...............
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.