🎆🎆🎆🎆🎆🎆 20. 🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Tana isowa suka gaisa tace "har na soma tunanin bazan sake ganinka ba" yace "koh? Dalili" "saboda na soma tunanin ko kai aljani ne. Na dade ina neman littafina ban samu ba amma lokaci daya ka daga hannaye kayi adu'a sai gashi kana tafiya manager ya kirani wai an gani, nayita murna na fito ko zan ganka amma baka nan. Dazu dana ganka ban zata kai bane shiyasa na kira sunanka domin na tabbatar kaine" dariya ya dingayi tsakanin shi da Allah don bai zata haka zata kalle shi ba "au dariya ma na baka?" saida ya natsu yace "aljanin lafiya, bama mala'ika ba. Haba kar kisa na soma jin tsoron kaina ba mana" tayi dariya itama tace "to shikenan yanzu ai na tabbatar kai dan Adam ne so wanchan zargin na soke shi" wayar shi ya soma ringing yaja gefe ya amsa, ya gama ya dawo "sorry ana neman a gida, mu hadu wani lokaci" "ko baka fada ba ai dole na roka, ni duk abunda aka mun ina yawan bada tukwici saboda haka tukwicin abunda ka mun shine ka zabi rana da kake free a lunch time sai na bada place mu hadu amma before then bani lambar ka" ya karanto mata ta saving sanan suka tsaida lokaci a washe gari, anan sukayi sallama ya kwashe su suka wuce gida. Washe gari karfe daya daidai ya baro office ya dawo gida, yayi wanka ya fesa turare yana saukowa duk ya bulaye su da kamshi a falo, rumaisa da hanifa suna jeren abinci akan dinnin sukayi turus suna kallon shi, rumaisa tace "umar wanan kamshin haka sai kace ka barar da kwalban turare duka" "budurwata zanje gani ai gwara nayi ta baza kamshi ko zanyi saurin siyan zuciyarta kinsan mata da son kamshi" mami ta bude baki "tofa! Lallai za'ayi ruwan sama da kankara a watan zafi,ko wacece haka oho?, yau wacce rana umar na maganar budurwa. Ni har na soma tunanin na hada ka da duk wacce zuciyata ta raya mun" ya wani bata rai "haba mami, umar dinki guda?" rumaisa tace "ai gwanda ayi maka haka domin akwai alamun hatta farida sai ta rigaka aure" yayi hanyar kofa saida ya kai daidai kofa sanan yace "kunata magana na ni kadai bayan yaya adnan ko soma lissafi bai yi ba" adnan ya tashi ya bishi a guje yana fadin "don ni ka raina ko? Idan ana maganar aure kana kirana sai na targada ka a gidan nan" shi kam tuni ya gudu har ya tayar da mota ya fice, dukkansu dariya sukeyi mishi a falon adnan din kuwa ya hada rai tamau ya wuce dinning, wa yaga su baban yaya. Mami tace "ai nikam na rasa matsalar dukkan su biyu, gwanda ma adnan din ma akan umar tunda shi yanada budurwa lokaci ne kawai ba'a tsayar ba amma shi umar duk wacce aka kawo sai yace bayayi, mardiyyan gidan baffan ku har tayi ta gaji tayi aurenta shi kowa kawai baya so" Adnan ya deba abincinshi salin alin ya wuce dakin shi don tun ana yabonshi har a soma kawo sukin shi.. Dama ta kirashi a waya tana tunanatar mishi kada yayi latti bata son african time saboda da hakan yasa yana isowa ya kirata tace har ta iso ta daga mishi hannu ya iso ya zauna, suka gaisa sanan sukayo odar abunda suke bukata, yaci rabi ya tura plate din yasha ruwa ya share baki, itakuma ci take tsakaninta da Allah tayi mishi wani kallon tuhuma yace "lafiya?" "lafiya mana da akayi mene" "naga kina mun wani irin kallo ne dana kasa fahimta" "ai dole nayi maka kallon tuhuma, kaci abinci rabi ka ture. U know mu mata bamu son almubazaranci kuma as a business woman nasan muhimmanci kowanne one naira dina so tell me why" ya danyi murmushi "dats my nature ban cika cin abinci ba,baya cikin agenda dina" ta daga kafada alamun ko oho tace "shikenan, suite uralf". Saida ta gama sanan yace "tell me about urslf" ta dan mishi bayani sama sama akan ita business woman ne kuma tana zama ne da mamanta da danta daya ja'afar shikuma fa shima haka. Sukayi hira sama sama sanan yace tasan me tace mene yace "ni mutum ne da bai iya kwana kwana ba saboda haka zanje straight to the point, tun ranar dana fara arba dake naji ina kaunarki, kauna me tsanani daya hanani runtsawa saida na dawo na dinga cizon yatsa abunda ya hanani karban no dinki watakila gigicewar ganinki ne kokuma ganin halin rashin natsuwar da kike ciki ne dunno. So a takaice ina sonki kuma i wont take a no for an answer". Sororo taketa kallonshi yana ta fayyace mata abunda ke ranshi bata katse shi ba saida yaga aya, tayi murmushi "haba malam umar, wanan karfin hali har ina? daga ganin sarkin fawa sai miya yayi zaki? Baka ma sanni bafa haka kawai har kana batun u wnt take no for an answer" ya daga kafada "ni ba wanan bane matsalata, burina ki amsa tayina kice kina sona simple sauran tunanin sai ki bar mun nayi shi" ta ma rasa abun fada. Tayi nisa tace "bazan ce na ki ka ba don iyakacin sanin dana maka na gane kanada kirki amma a gaskiya akwai ababen dake bibiyar rayuwata wanda nasan dole ya kawo mana cikas muddin muka ce zamuyi soyayya" "nace miki ki bar wadanan hasashen dukkansu i can handle them ni kawai kice kina sona kawai. Nasan kina tunanin ke bazawra ce nikuma saurayi, kinada yaro da dai sauran su to nidai babu ruwana da hakan muddin kika amince dani shikenan" a zuciyarta tace "yau na gamu da gamona " a sarari tace "shikenan ka bani lokacin zanyi shawara nan da sati daya zakaji feed back amma ka shirya jin abubuwan da kunnuwanka zasu kasa ji" "ba amin ba. In shaa Allah babu komi face alkhairi" tayi dariya kawai tana jijjiga kai, a haka suka rabu.
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.