🎆🎆🎆🎆🎆🎆. 21. 🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Suna kwance akan wani doguwar kujerun roba suna shan iska a cikin wani gidan gonan habib dake dan wajen gari, suna hutawa. Dukkansu biyu idan sunada karancin aiki sukan je gidan gonan bayan sun zagaya sanan su samu karkashi bushiya su zazzauna saboda basu son a damesu hatta girki saidai su aika ma'aikatan su siya musu abinci su kawo musu wajen. Suna kan hira wayar umar ya dau kara, kasancewar busy line dinshi ne shiyasa ya buga wata uwar tsaki ya soma mita "kai! Kai! Kai! Saboda Allah mutum bai isa ya huta ba, daga litinin har asabar mutum na faman zirga zirga yau lahadin ma baza'a barshi ya huta ba, ni kashe wayar kawai zan soma yi ..........." ai ganin sunan dake kan wayar shi ya sakashi hadiyar sauran mitar a makoshinshi yayi saurin sallama ta gaishe shi ya amsa ta tambayeshi yana ina ne ya kwatanta mata inda yake tace mishi nan da awa daya zata iso. Habib na kallonshi har ya ajiye wayan yana murmushi yace "wato ya kamata masu basirar waya su soma yin yanda mutum zai ji abunda mutum yake fada kafin ya amsa saboda a dinga kama irin ku. Yanda ka dinga bala'i kamar zaka cije mutum kafin ka daga wayar amma kana dannawa najika kus harda faman ladabi, wani abun sai mata" sukayi dariya dukkansu suna ta faman hira har ta iso ta kira tana shaida mishi isowarta yayi mata kwatancen inda take. Tunda habib ya hangota kwalkwalarshi ta dau chaji domin ya zata gizo idanunshi suke mishi saida ta kusan karasowa inda suke yayi saurin dafa shi "kai man a ina kuma ka samo budurwa mai kama da matata?" "ah ah ka mance, matar takan ce ba kamanni ba, ni dalla ka natsu kafun ta zo tace muna maganarta kasan mata wasu lokutan da birkicewa mutum" haka ya hadiya kalamanshi har ta iso suka gaisa yace "bari na baku wuri na dan zagaya idan ka gama sai ka sanar dani koh" ya tafi yanata faman waiwayarta domin kammanin nasu har ya baci. Wajen da habib ya tashi ta zauna sanan ya gabatar mata da fresh milk da glass cup ta kurba ta ajiye tace "nayi nazarin daya kamata kuma na kasa dauko mafita saidai na yanke shawaran zan gaya maka ko ni wacece watakila idan ka saurara zaka hakura dani kowanne yayi hanyansa" a nan dai ta soma bashi labarin rayuwarta tiryan tiryan kamar yanda nima ba baku watakila ma harda kari (wink). Ya natsu yana sauraranta tamkar baisan komi ba a game da ita ba saida ta gama bashi labarin sanan ya soma mata jimami tace "yanzu dai da fatan ka gamsu da kashedin dana maka akan takun mu bazai taba zuwa daya ba, mun banbanta a fanni dayawa sanan ban baka labarina ba domin na tona wa kaina asiri kokuma don kaji tausayina ah ah na fada ne saboda koda Allah zai kaddara aure tsakanina da kai ya zamto munyi shi ba tare da sirri ba ko daya don bana son mai karya kuma bana kaunar na kasance daya a cikin su" "kinsan Allah? To wlh labarin nan dakika bani ko kadan bai bani tsoro ba instead ya kara karfafa mun gwiwa na don na jajirce akan sonki saboda haka tambayan dana miki tun ranar ban sauya shi ba har yanzu, kina sona kuma zaki aureni? Kokuma akwai wani abune banda wanan?" kallonshi kawai take ganin yanda ya dage shi tsakani da Allah ga bukatar shi ita kuma tana hango musu matsaloli tuli tuli saboda akasarin lokuta ba daga kan samarin ake samun matsala ba daga iyayen su ne tace "ka cika taurin kai umar wlh da ka natsu ka fahimceni ka nemi wata zai fiye mana duka kwanciyar hankali" "ai wlh tunda kika ga nace kece nake so to ko sama da kasa zasu hadu tofa lalle sai ke din saidai idan buda baki kikayi kika furta umar bana sonka to sai na rabu dake tunda ba'a soyayar dole don bazan taba auren wacce bata sona" tayi ajiyar zuciya "ban kika ba umar amma bazan taba furtawa ina sonka ba sai kaje ka sanar da iyayenka ko ni wacece sun amince da auren mu sanan mu dasa kakkarfar alaka da kai saboda yanda kowa keda weak point a rayuwarshi nima inada shi kuma shine zuciya, muddin naso mutum na karamin jinya nakeyi ba kafin na rabu dashi. Banaso na dasa soyayya dakai a zo daga baya bayan na saba da soyayyarka a hanamu aure nakega wanan karon kila mutuwa zanyi don haka kaje kayi shawara da iyayenka duka yanda suka fada sai ka sanar dani, ina mai marrhaba da amsarka komi munin shi na tabbata naji worst ones" tana magana tana hawaye ta mutukar bashi tausayi ga kuma kaunarta dayayi dare dare a birnin zuciyarshi "na dau alwashi komi runtsi sai na shawo kansu kuma komi zai zo mana a saukake insha Allah" a lokacin ta danyi murmushi mai ciwo "mudiin haka ta faru ina mai marhaba da soyayyarka" ta mike "na barka lafiya watakila shine sallamar mu na karshe da zamuyi a dadin rai" "yauma nace ba amin ba tunda baki iya kyakyawar adu'a ba" tayi dariya,suna hira har bakin motarta ya bude mata ta shiga sanan ta fice yana mai daga mata hannu har ta kule ya dawo wajen zamanshi.
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.