🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 05 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Idan na duba halin da muke ciki sau tari sai nace Alhmdlh! Nafi wasu kuma wasu sun fini dama hakan shine rayuwa. Nakan fada mata "mama idan nayi kudi zan siye miki tangamemen gida kaman wanan, na sai miki mota mai kyau bama sai kinyi tuki ba zan nemo miki direba da masu aiki wa'inda zasu miki bauta kamar yanda kika bauta ma wasu kema sai kin dandana wanan jindadin rayuwa" takanyi dariya tace "sodari(ma'ana wacce ake so don bata kiran sunana)ki ma daina ire iren wadanan tunanin tun wuri ki natsu, a zuri'ar mu karankap babu mai arziki saboda haka kima bar wanan mafarkin. Ke a ganinki yanda zamani ta lalace talaka haka kawai yake zama mai kudi tashi daya? To stop dreaming, kiyi ki karasa karatun ki kiyi aure ki soma aikin mai aiki kema a gidan wasu don haka rayuwar mu zata kare a matsayin masu aiki" sai nayi murmushi na girgiza kai bazata taba ganewa ba inada babban buri wanda nasan Allah zai cika munshi inshaa Allah. KADDARA TA ta kokuma ince matsalolina tunda kaddara ta hau kaina tun a ranar da aka haifeni babu uba, sun fara ne a lokacin dana gama zana jssce dina na fito da sakamako mai kyau don kwakwalwata na ja babu laifi kamar yanda mama take yawan fada mun cewa na dau kwakwalwar babana ne don shima ya kasance mai ilimi ba kadan ba. Ina zaune a gida ranar baban yar uwargida na mai suna rukkaiya ta kawo wa mahaifiyarta ziyara daga katsina ta ga yanda nake bauta wa mahaifiyarta ta nuna son ta tafi da ni saboda fama da laulayi da take babu mai lura mata da gida ga kuma mutukar wahala da take sha. Maman aliyu bata so rabuwa dani ba amma son da take wa yarta yasa ta amince, nikuma ganin tayi alkawarin karatuna bazata katse shi ba shiyasa na amince, nayi kukan rabuwa da kakata da kawuna mai mutukar sona muka wuce garin katsina. Tunda muka iso uwargida ta Rukkaiya tana iyakacin kokarinta wajen sauke hakkina dake kanta dukda ta kasance mai bala'i amma tana ban ci da sha da sutura mai kyau shiyasa tuni nayi clean nayi freshi ruwan birni ta karbeni. Mijinta mubarak shike biya mun kudin makaranta, shima yana gwada mun kulawa ba laifi wanda sai daga baya na soma dana sananin kulawar da yake bani. Bayan ta haihu aka sanya wa yaron sunan babanta amma ana kiran shi da amiir sai na chanja ma dukkansu suna na mayar musu da baban amiir da maman amiir don basu girma kamar yanda na girma na gani anayi a kauyen mu. Na shiga ss3 a lokacin dukk wata sirrin dake tattare a jikin ya mace duk sun bayyana a jikina shiyasa hatta kallon da baban amiir ya soma mun ya sauya salo, girki idan nayi ya dinga danbanzan santi kenan sai kace matar shi bata iya ba, koda bansaka hoda a fuska ba sai yace mun nayi kyau, a matsayina na karamar yarinya marasa expirience din rayuwa a lokacin ban gane manufar shi ba sai daga baya daya fito baro baro ya fada mun nufinsa a kaina. Kunji soko waifa sona yake, tuni na ce mishi ah ah banayi don sau miliyan ba daya na sha jin maman amirr tana jajanta mun yanda bata kaunar kishiya, ko kawarta aka wa kishiya ta dinga takaici tana kumburi kamar zata fashe ballantana ita, to ni mahaukaciyar kasuwa ce da zan amince da bukatar shi kalan ta kar wa mamana da kakata ni suyi asara?..........
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.