🎆🎆🎆🎆🎆🎆 30. 🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Haka yayi saurin bin bayanta saboda tunda safe mama ta sanar mishi da zuwan shi baban amiir din, har tayi nisa ko jin nauyin cikin dake jikinta ma batayi saboda bacin rai ya rufe mata ido, yayi saurin rikota ta kai mishi naushi mai ji da rai a gefen cikin shi, zafi ya ratsa shi ya saketa ta sakeyin gaba wanan karon ta baya ya rungumo ta tun tana turjewa da karfi har ta sarara mishi jikinta nata rawa tana kuka tana fadin ''wlh idan ya rabani da da'na bansan ya zanyi da raina ba, akwai mutukar shakuwa a tsakanina da shi, dukkani wulakancin dana fuskanta a rayuwata saboda shi na samu karfin gwiwan tsallakowa saboda na zamo mishi jigo a rayuwarshi tunda bashi da kowa sai ni sai Allah mahaifinshi ya juya mishi baya. Hrt pls kar ka bari ya rabamu dan Allah hrt'' ya rufe maka bakinta da hannu daya dayan yana gungume da ita yaki sakinta yan daidaikun mutane dake wucewa kowa kallonsu yake mussaman ma ita da babu gyale babu takalmi ga tulelen ciki,ya rikota har mota ya sakata a ciki sanan suka nufi gida a mota ya playin mata karatun alQur'ani ta dinga ajiyar zuciya a hankali. suna isowa ya cirota suka wuce cikin gida, dakinta suka nufa ya rabata da kayan jikinta sanan ya wuce da ita bayan gidata zauna a cikin bathtub ya kunna mata shower a kai sanan ya fita ya barta, kafin ta fito har ya hada mata strawberry n milk ya shigo mata dashi ya zauna jiranta, tana fitowa ya lullubeta da towel dayan kuma ya daura mata a kanta saboda ruwan dake digowa ya zaunar da ita akan cinyar shi tana so tayi magana ya manna hannun shi akan lebben ta yace'' banaso naji komi first listen to me dukkanin abunda kike son fada sai subi bayan nawa'' ya kafa mata kofin a baki sanyin madarar ya ratsa ta bai dire ba saida ta shanye sanan yace ''yanzu sai muyi magana da fatan kina saurara na'' ta gyada kai, '' a rayuwa evry one makes mistake dani dake dama kowa no 1 is perfect amma there's sumtin special about it, duk wanda yayi kuskure amma ya ajiye girman kai da jiji da kansa yazo ya furta kalmar hakuri no a ganina ya gama komi saboda ba kowa ya iya kamar hakuri a wanan zamanin ba saboda haka a matsayina na abokin shawarar ki kuma mai sonki da rahamar ubangiji ina mai baki shawarar ki amshi gafarar shi da hannu bibiyu sanan ki yafe mishi da zuciya daya saboda lalle Allah na tare da masu hakuri da fatan kin fahimce ni'' cikin hawaye tace ''shikenan naji na yafe mishi amma a yanzu matsalata daya shine yaya zanyi idan yace zai rabani da jj'' yana shafar bayanta yace 'karki damu akan wana domin hukuncin a hannun mu yake ba nashi ba don koda munje kotu mune masu upper hand a cikin case din so dont worry babu me rabaki da danmu kinji'' ta saukar da sassanyar ajiyar zuciya tare da fadin nagode hrt, thank u soo mch... Daya ga hankalinta ya soma kwanciya sai yayi saurin riko gefen cikin shi data nausa yace''wash, wayyo cikina'' cikin kidima tace '' hrt menene'' ''dazu inda kika naushe ni ne ke mun ciwo, kai, kinji zafin kuwa harfa na soma tunanin ba ke kadai bace sai mu wuce da ke wajen rukiya, karfi ne haka sai kace wani dan dambe'' tanata dariya tana matsa mishi wajen shi kuma ya hakkince akan wajen na mishi ciwo har ya mantar da ita damuwarta.... Zaman lafiya da farinciki ya wanzu sakanin wadanan family din dukkansu sai abunda ba'a rasa ba domin a rayuwa no1 is perfect sanan ance zo mu zauna zo mu saba, zaleeha ta haifa zukekeiyar yarta mai kama da babanta sak saidai tabon fuskar zaleeha data dauka, bayan kwana bakwai aka rada mata sunan zeenatu, zinariya mai haskaka zuciyaan iyayenta dama danginta duka......... Haka suka kasance har mai rabawa yazo ya raba TAMMATBILLAH!!!!!............ Anan nake mai kawo maku karshen labarina mai sunan KAKKARFAR ALAKA, for those i wronged i say sorry evry one makes mistake, for the mistakes ave wrote i ask Allah swt to forgive me.
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.