Kakkarfar Alaka Part 22

116 10 0
                                    


               🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆. 22. 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆

Washe gari da yamma bayan sun dawo daga massalaci ya samu adnan a daki ya kwankwasa ya shiga, yana danne danne a laptop ya samu guri a gefen gadon ya zauna.

Idanunshi akan allon laptop din yace "ya dai bro?" yace "yaya dan magana zamuyi da kai if ur free" "ban minti goma na compiling abubuwan nan kaji", saida ya gama sanan ya rufe ya dauko ya jona shi a chaji ya ajiye tabarau dinshi a gidansu sanan ya bude fridge dinshi ya dauko chapman biyu ya wurga mishi daya ya dawo gefenshi ya zauna suka kurba tare sanan yace "ya dai?" "wato yaya wata yarinya na samu ina so shine naje na sameta muka daidaita" ya dan doke kafadar shi "ai wanan gud news ne amma ka shigo nan da fuskar damuwa ko tazo daga baya tace ta fasa ne?" ya soma sosa keya "wato..... Umm..... Mnn...... Matsala aka samu amma ba irin wanan daka lisafa ba" ya bashi labarinta tiryan tiryan shima sanan yace "ya adnan so nake ka samu baba kayi mishi bayani" ya jinjina kai "tab! babban magana kenan! Yanzu umar daga ina kakeso na fara, me ma kakeso naje na fada mishi?" ya matso kusa dashi "yaya kai babba ne at least ka girme ni kuma ka fini expirience na kalaman natsuwa watakila ni idan naje wajenshi head on ba lallai ya amince ba amma idan kaine nasan akwai hanyoyin da zakayi amfani dashi wajen shawo kanshi nasan ka yaya, ka taimakeni" yayi nisa sanan yace "shikenan bari kawai naje yanzu domin maganar nan bana bari ya kwana bane duk yanda mukayi dashi zaka ji" yace "ah yaya ka dai bari ayi isha mu ci abinci sai kuyi ko ya?" "shikenan naji Allah ya kaimu" "amin" a nan suka rabu. Bayan sun kammala cin abinci ya wuce dakinshi ya kasa zaune ya kasa tsaye duk fargaban amsar da zaiji duk ya cika shi, mami batada matsala ita kam muddin bai shige addinin musulunci ba tana marrhaba dashi tsoronshi daya baban su, wasu lokacin idan ya birkice akan rasa gane ina ya dosa. Landline din dakinshi yayi kara alamar wani a gidan ke son magana dashi domin anyi connectin dinsu a kotaina hatta kitchen akwai, cikinshi yayi wata irin kugawa yaje ya amsa muryar abbansu yaji yace mishi ya sameshi a falo. Duka adu'ar dayazo bakishi shi yake jerawa har ya iso falon babansu ya tarar da adnan da mami dukkansu tare dashi ya samu gefen mami ya rakube a kasa sanan yace "abba gani" "ba wani dogon magana bane dama zance naji sakonka a wajen adnan a gaskiya banso amincewa ba amma danayi la'akari da hujjojin daya dinga kawo mun sai na gane cewa lamarin na bukatar fahimta saboda haka naji bukatarka kuma naji na yayanka ke mamansu me kike dashi da zaki fada?" ta girgiza kai "banida abun fada. A kodayaushe ka zartar da hukunci ni mai ladabice a gareka saboda baka taba zartarwa an dawo ana Allah tir dashi ba" "shikenan to ni ga tawa hukuncin, zanje nayi bincike akai nabi diddigi akan komai, wlh muddin na samu akasi koda daya ne a ciki to ka tabbata maganar ta watse amma idan har ya tabbata gaskiya ne to babu makawa zaka aureta, ku tashi kuje ku kwanta" dukkansu biyu suka mike sukayi musu saida safe kowa ya wuce dakinsa. A waya ya kira zaleeha yana mai sanar da ita hukuncin da abba ya zarta, tace Allah yasa suji alkhairi wanan karon kam yace amiin saboda tayi adu'a mai kyau. A lokacin daya biyo baya suna cikin jiran hukunci abba a lokacin shakuwa mai tsanani ya shiga tsakaninsu, taso ta yakice shi amma ta kasa saboda ba shikadai ke fama da lalurar so ba harda ita ta fada a rijiyar kokuma ince kogin. Bayan sati biyu umar ya dawo daga wajen aiki kenan abba ya aika kiran shi ya shigo ya zauna a kasa yana sauraran shi da mamin, abba yace "naje nayi bincike kamar yanda na fada kuma Alhmdlh anyi dace da abubuwan data fada hakan ne hakikanin gaskiyan saboda haka ina mai farincikin sanar dakai cewa na yarje maka kaje neman aurenta idan aka bukaci ka turo ka zo ka sanar dani muje mu tambayo maka aurenta", wayyo murna! Bakinshi kasa rufuwa yayi,tsantsar godiya kawai keta faman kwarara daga bakinshi. Yana fitowa ya soma neman layin ta ta amsa a kasalance alamar tana barci ne ya tasheta yace "albishirinki" cikin yanayin magagi tace "goro fari kal" "abba ya amince da auren mu" nan take barcin ya wartsake a idanunta ta mike zaune tace "dan Allah fa hrt".Yace "wlh kuwa" ta fashe da dariyan farinciki "lallai yau ka bani albishirin da ban taba samu ba, har kasa barcina ya wartsake " "kinga dakata ba wanin nan zaki kallameni da dadin baki, tukwici na kawai nake saurara" "hrt kaima kasan dolen dole nema na baka tukwici saboda haka gobe ka saka time kazo gida zan hada maka delicious kuma favourite dinka, tru out gobe dina zan dedicating maka ne kai kadai" "lallai ashe ni dan gata ne " "au dama kana tantama ne? Kanada ni babu kai babu maraici" yayi dariya harda shewa "iyeh! Lallai to Ubangiji Allah ya kaimu gobe da rai da lafiya". Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa cikin tsantsar so da kulawa, an aiko gidansu zaliha kuma an musu tarba mai kyau aka tsai da ranar aure iri daya dana adnan saboda abba yace bai isa umar yayi aure ya barshi mishi a gida ba shima ya san inda dare yayi mishi. 

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now