Kakkarfar Alaka Part 8

137 10 1
                                    


           🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 08 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆


Sai bayan sallar asuba na samu barci ya daukeni bani na tashi ba sai kusan karfe goma sha dayan safe, da rarrafe na kai kaina bayangida na dauraye jikina, dukda bansan yanda na kamata nayi ba i just did what came up in my head nd i felt better. Daga ranar muka soma wasan buya dashi kwatakwata na toshe duk hanyoyin da zamu hadu dashi a haka har maman amiir ta dawo, babban abun tashin hankali shine a lokacin dana gama waec dina ina jiran neco nayi na nema al'adata na rasa, wata uku kenan, cikina kuma da yake nan flat ya soma wani un nececesary girma dana kasa fahimta, a lokacin maman amira itama tana fama da nata laulayin cikin, a wajenta na gane ciki ne kadai ke hana mace ganin al'adarta sai kuma cutan lalura wanda ni nasan banida shi. Kada a ga laifina ace nayi kidahumanci dayawa, na farko ni yar kauyece futuk, na biyu banyi rayuwa da uwata ba hasalima sau shida ko bakwai nake ganinta a shekara, koda naje wajenta bamu da lokacin hira kasancewar bautan da take wa gidan aikinta ya wuce misali so i was ignorant, a makaranta kuma maman amiira ta hanani kawaye a makaranta wai bata son gayyan sodi azo a cika mata gida kalan na kawo wacce zata kwace mata miji. Da kafafuna naje asibiti ranar bayan dukkansu sun fita kasancewar tana dan bani kudin kashewa, gwajin farko likita yace inada juna biyu wai har na wata uku, cikin sassaucin hankali na karbi sakamakon na fito daga asibitin na wuce gida don gudun kada na tara wa kaina mutane a ka. Saida na iso gida na kulle kaina a daki a nan na fasa wata uban kara hannu a kai na soma zagayen dakin ina furta kalmar "innalillahi wa inna ilaihirrajiun, na shiga ukuna", ranar har yamma ina ta aikin kuka ko abincin dare ban girka ba, saida ta dawo ta tambayeni dalili nace mata kaina ne ke ciwo, ta taba jikina sanan ga idanuna sun kumbura sunyi ja sai ta tabbatar da karyar dana narka tace naje na kwanta, ranar dai marcaroni kawai ta dafa shap shap kowa ya ci ya kwanta. Washe gari na bari sai da maman amiir ta fita ita da amiir sanan na taro shi, bayan gaisuwa yaga naja tunga na tsaya dai yace "ya dai zalli baby" babu alamun wasa a fuskana nace "banga al'adata ba yau watanni uku kenan" ya tsura munido "idan bakiga al'adar ki ba ai asibiti zakije a duba lafiyar ki wata kila matsala kika samu a mahaifar kai bawai ki zo kina gaya mun ba" "ai kai likita ne ya kamata ka gane inda na dosa amma tunda kana nuna halin ko'inkula to bari na fito baro baro na gaya maka, ciki ne dani wata uku harda satikkai" ya wani wangale ido da baki a lokaci daya, nace ''munafuki'' a raina "ci mene?" "ki, juna biyu har na wata uku" zufa ya hau keto mishi goshin shi har kyalli ya dinga yi ya yarfar sanan yace"to yanzu me kikeso nayi akai?" "ji wani tambayan da kake mun, da ace na sani da na tambayeka? Ko ni nace maka kayi mun fyade? Mafita shine na haifa ka amshi kayanka sanan muje kauye a daura mana aure" "kutumar uba! ki haifa mun shege a gida? To wlh ba dani ba, tun wuri mu wuce dake asibiti naje nasan yanda zanyi dashi or idan ma bakya so ni nayi miki zamu iya zuwa wani wuri a cire ko nawa ne ni na amince zan biya amma bawai a haife mun ciki a gida ba, nace wa rukkaiya mene". Wato kallonshi na dingayi shekeke sai kace sakarya yana ta faman zuba surutu mara amfani ina ayyana takaicin da' namiji a zuciyata, saida ya kai aya sanan nace "ka gama? To saurareni da kyau, wallahil azeem bazan zubar da cikin nan ba, yanda uwata ta haifoni haka nima sai na haifo cikin saidai duk abunda zai faru ya faru, da kake babatun me zaka gaya wa matarka a lokacin da kake keta mun haddi wani girman Allahn ne ba hadaka dashi ba yanzu zaka kawo mun wani zancen banza. Wallahi sai na haife shi kaikuma ka shirya tunkarar duniya a ranar dana haife jinjiri na ajiye maka kaida matarka, fakat!", ina kaiwa aya na juya abuna nayi daki na barshi tsaye a wajen. Tun daga ranar akalar zaman lafiyata ta chanja a gidan, duk shopping din dayake mun a matsayin kyautatawa kamar yanda ya fada wa matar shi ya tsaya hatta kudin motar zuwa exams maman amiir ita ta soma bani don ata fur ya daina. Idan nayi girki a da sai ya dinga santi sai kace matarshi bata iya ba amma yanzu sai ya furzar yace gishiri ko maggi yayi yawa na karshen ma cewa yayi yaji yayi yawa yanata tari wai an manta yanada ulcer so ake a kasheshi? Abun ya ishe maman amir kawai tace shikenan daga ranar na bar girki ita da kanta zata dinga daurawa....

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now