Kakkarfar Alaka Part 4

177 11 2
                                    


                       🎆🎆🎆🎆🎆🎆. 04 🎆🎆🎆🎆🎆🎆

Rayuwar gidan mu mai sauki ce ma'ana akan bunu muke kwana don bamuda arzikin siyan katifa da dan tsohon bargona wanda da shi da babu dan kadan ne, suturata a kirge ina iya kirge su don ko sha biyu basu kai ba tunda sai sun mutu mama ke turo da sabo kokuma idan yayan gidan da take aiki sunyi watsi da nasu a shara sai ta tattaro ta tanada mun, akasarin su ma sun mun yawa amma haka nake saka su a ganina sun fi mun babu. Naje makaranta na dawo, nida abdallah muje cikin daji mu samo icce dayawa muzo bakin titi mu kasa kafin yamma mun saida duka saboda nida kawuna akwai iya ciniki, da dare bayan isha muje dandali mu kidi, idan ma an saka kallo mu kalla da kudin mu bayan an gama mu sai kifi da rake da kayan kwalam mu koma gida mu kasa sauran chanjin mu saka a cikin asusu mu hau gado to kuma sai washe gari. Wanan shine day to day routine dina, Alla ha halicceni yarinya mai kazar kazar kamar mahaifiyata shiyasa ina gama primary school aka daukeni aiki a gidan wani mai dan kudin kauyen mu, ina mata reno da aikin gida ita kuma sai ta biyani da albashi mai tsoka, da wanan kudin muke samu mu saya kaya harda sabon katifa, rayuwar mu ta soma dadi shiyasa bana sanya da sabon aikina. Maman aliyu tana da mutumci ssai, muna zaune lafiya tsakanina da ita sai kauna da mutuntawa, tsangwamar kalmar "shegiya" da ake bina dashi bai taba kawo mana akasi ba dukda hausawa sunce "shege na gidan ubansa"..... Ina jss 2 na kaiwa mahaifiyata ziyara a birni, wai! zo kuga kauyanci nasan ba saina baku labari ba har kun hango. Gidan bene tangameme, kiris ya rage mai mota ya bugeni a hanya don har yayi horn ya gaji ban ko waiwayeshi ba, dakyar na kwankwasa gate din maigadi ya bude, na nuna mishi takardar hannuna da aka bani adress din gidan na nema idan nazo. Allah yaso na iya boko da kuwa na kwana gidan chajimoshin, mama ta fito ta rungume ni ta shiga dani gidan, wanan shine ranar farko dana taba hawa kan katifa na kwanta, don dadi saida na makara sallar asuba nida a kauye nike tashin su sallah tun assalatun farko. Zuwana ya mutukar taimaka mata da aikin gida, ashe a rayuwa akwai sangartattun yara haka?. Sunan mai gidanta Alh Adamu da matar shi hajiya habiba, yaran su uku, shegun yara masu shegen girman kai Yazid shine dansu na farko sai Hauwa da Rahiina. Tunda safe take aiki har dare don hatta remote control sai an mika musu koda kuwa ga su ga shine a cewarsu meye amfanin biyanta da akeyi, hatta inner wears dinsu da ya kamata ya zama sirri a garesu dukka zaka tarar a cikin kayan wanki Allah yaso akwai washing machine da bansan yanda hannun mamana zai koma ba. Sai kuma wani abun ban haushi wai da maryam suke kiranta, katuwa da ita amma ko kunya basu ji wai maryam bayan a kauyen mu duk lalacin mace muddin ta haihu to ta tashi daga sunanta ta koma maman wance ta inda aka saka wa mamana sunan mero kenan don a bata wanan darajar. Idan ka ganmu sai kace yayata ce idan ban mance ba akace tana da shekaru goma sha shida ta haifeni, karatun da bata karasa ba kenan har yau.......

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now