🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆. 24 🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Dukkansu a falon saida suka firgita banda hajara data san dawar garin, zaleeha tayi dan murmushin karfin hali tace "haba baba, haka kawai sai kace kaine babana? A ina ka sanni kuma ta yaya ma kasan munada dangantaka da kai?" ya cire hular kanshi ya yar akan kujera ya share gumin fuskar shi da hankechief sanan yace "saboda wanan zoben nawane, na gidan mune dukkanmu munada shi" ya riko yatsar hajara nahagu na hudun ya nuna mata irinshi sak saidai banbancin design din harrufan ta "kinga na autarmu itama tana dashi, tahir da kika zauna a gidanshi da kin lura da yatsar shi shima da kin gani. Nawa ne kadai baya nan sanadiyyar sanar da iyayena da nayi cewa nawa ya bata bayan ba haka bane, budurwata wacce nake mutukar kauna na bawa a kauye a lokacin dana je nysc a gombe" mikewa tayi saurin yi kamar mai iskokai tace "kaga malam dakata kaji, kai baka ma ji kunya ba kama ce ni yarka ce, menene nawa ka sani ci ko sha ko sutura? Wani hakkina ka sauke wanda Allah ya rataya maka a wuya har kanada guts din da zaka ce ni yarka ce?" ya hada hannayen shi biyu alamar roko ganin yanda a lokaci daya ta birkice kyakyawar murmushin fuskarta ya bace yanzu ya hadu tamkar hadarin gabas alamun babu sasauci "ki tsaya ki fahimce ni zaleeha, u have evry right to be angry amma kamata yayi ki saurareni kiji uzurina wlh zaki gane cewa duk abunda ya faru ba laifina bane ......" tayi saurin katse shi "idan ba laifin ka bane laifin uban waye? Kaga malam saurara ka natsu ka kama girmanka tun muna shaidan juna da kai, ina mutukar ganin darajar familyn ku saboda dan uwanka ya taka rawar gani a kundin tarihin rayuwata saboda haka ka rike girmanka kada na sake jin ka ambaci kaine mahaifina idan ba haka ba zan shayar da dukanku mamaki" ta laluba gyale da jakanta tace " yamma ya doso zan wuce gida saboda nike wa mahaifiyata girki, ku huta lafiya" tayi waje abunta. Dukkansu jikinsu yayi sanyi a falon harda mutumin domin fashewa yayi da kuka kaman karamin yaro (sharar hawaye) yafa ban tausayi. Umar yayi sauri ya mike ya bi bayanta da sauri ya tarar harta fita gate, ya buga mota ya biyota a baya ya tarar tanata buga uban sauri ta kusa karasa bakin layi yayi saurin shan gabanta gamida bude mata kofar, batayi musu ba ta shiga yanayin fuskarta ya tabbatar mishi da lallai an fama mata babban miki a zuciyarta shiyasa baice komi ba har suka isa ta sauka ko sai anjima baiji ba ballantana kallaman bankwana data saba mishi a duk lokacin da zasu rabu, lallai yau an tabo mun gimbiyata yace a ranshi sanan ya juya motar shi ya koma gidan habiba ya tarar habib nata yiwa matarshi da yayanta jerin tambayoyi shigowar umar yasa ya tsaigaita domin an saka shi a duhu, mutumin yace "umar dama kai nake jira saboda kai kafi kusanci da ita shin mamanta na raye?" umar ya gyada kai sai yace "to inaso ka recording duk abunda zan fada yanzu bansan ko zan kai wani lokaci ba saboda bakincikin dake cikin zuciyata nata karuwa" umar yayi saurin danna record a wayanshi sanan ya soma "asalin sunana Abubakar Yusuf Moddibo, familyn mu sananne ne a garin adamawa saboda mun hada dangantaka da sarauta, mahaifina Alh yusuf shararren mai kudi saboda bamu tashi mun tsinci kawunan mu a babu ba, mu bakwai mahaifiyata ta haifa, Al'amin,sai ni sai Abdullahi, Buhari, Tahir sanan Abdulsamad da Hajara. Akwai tazara a tsakanin mu ssai domin saida na gama sec schl aka haifi hajara. Dukda ba nine dan fari a gidan ba amma sai na kasance mafi soyuwa a garesu saboda sassanyar halina, banida hayaniyya ko kadan sanan iyayena su ne abokanan shawara na, bana taba daukan mataki ba tare dana shawarce su ba mussaman ma mahaifiyata, akwai shakuwa da sabo ssai a tsakanimu shiyasa ma duka yangidan mu boardin sukayi amma ni day nayi sanan ko a lokacin da al'amin ke dubai mahaifiyata ta hanani zuwa ta zabar mun abti domin kwata kwata abunda zaiyi nesa danine bata so. Ina kammala karatuna aka turani gombe state nayi service dina, mahaifiyata ta tayar da hankalinta ko mutuwa albarka da kyar da lallami aka kallameta aka fahimtar da ita akancewa da mace takewa wanan kullen da da sauki amma namiji ana bukatar shi a wajaje da dama waya san a inda cin abincina yake? Idan bata barni ba ta yaya zanyi socializing da sauran mutane. Da kyar da ta yarda na tafi gombe state a garin dikko.
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.