Kakkarfar Alaka Part 18

164 11 0
                                    


               🎆🎆🎆🎆🎆🎆 18 🎆🎆🎆🎆🎆🎆


Ya bude drawer din gadonsa ya tura takardan ciki sanan ya diro ya wuce ban daki ya dauro alwala. Yayi yan nafifili sanan ya hau gado yana mai tunanin zalihan sa. Washe gari yaje wajen aiki da niyyar yana dawowa yaje ya kai mata littafinta tafiyan gaggawa ya kamashi oganshi ya aike shi enugu wani aiki da zumar bayan kwana uku zai dawo. Wasa wasa tafiyan kwana uku ta koma sati daya, ya dawo a gajiye amma kasancewar ya dau wa ranshi rikicin ala dole yaje ya nemota haka ya kicking din mota ya dauki hanyar cafe din a hanya motarshi ta soma hayaki motar ta taya cak alamun ta lalace. Ya bugawa habib kira "kana ina ne?" "ina gida amma ina shirin fita, zan kai matata asibiti karban result dinta" "gani nan a kwanan masu gwangwani kazo ka daukeni, zaka ajiyeni ne a wani waje" ya kashe wayar. Bai dade ba sai gashi a lokacin mai gyara har ya iso ya soma aiki, ya mika mishi mukulli ya sallameshi akan idan ya gama ya mayar mishi motar gida domin bakanikin gidan su ne. Suka gaisa habib ya ja su sai asibiti tana kokarin sauka yace "kinsan Allah yanda nasan layin da ake tarar wa a asibiti dinnan ballantana ma mata muddin kuka samu abokin hira kuna manta lokaci to muddin kikaje kika dade saidai ki tara mashin ko adaidaita sahu domin zaki dawo ki tarar babu mu. Minti goma kawai na baki, ehe" hannunta a kunne tana dariya tace "to naji kuma in shaa Allah bazan dade ba" habib ya rike haba "ikon Allah, ji mun wani karfin hali a nan. Mata da motan mijinta amma ana neman yi mata fin karfi? To kaima saurara kaji, bazan taba barin wanan asibitin ba muddin bada matata ba, kaji mun mutum" asmau yarsu mai kimamin shekaru bakwai sai faman dariyan su take dama aikin kenan muddin sun hadu. Suna kan chachar bakin sai gata ta dawo da results din wanda ya nuna alamun tanada shigan ciki. Saida suka gama murnan sanan ya tambaye shi "man ina zan kaika ne" "cafe din murtala muhammad way" "yanzu cafe ne dama zaka ka wani daga mun hankali, ya baka tambayeni ba? Laptop dina na bayan seat a wajen ka dauka mana kayi duk abunda kake bukata zaka wani wahala kanka" "to malam ai nima inada laptop din idan ina bukata ne da ko na ahmad na ara nayi abunda zanyi. Ba wanan bane matsalata akwai wanda ke jirana ne" sula dau hanya. Yana isa yayi parking a wajen ajiye motoci "to dazu kana ta aukin yi wa matata kashedi to yanzu kaima saurara naka, nasan layin cikin cafe don ni ba bakonsa bane so kaima yanzu ka jini da kyau, muddin ka dade yanda muke jin yunwan nan to ka tabbata zaka dawo ka tarar da wayam" ya kulle motan "inda kuwa kayi kadan kenan, ka kuskura ka gani garin nan sai yayi mana kadan" "ahap! Nidai na gaya maka" yana dariya yayi cikin harabar cafe. Daga nesa ya hangota tallafe da kuncinta da hannayenta duka biyu, sai da ya matso kusa sanan ya gane ita ce amma compared to ranar yau fuskarta very dull alamun tana cikin rashin natsuwa. Ya karaso karkashin leman roba na mtn da take zaune ya janyo kujera ya zauna amma duk da haka idanunta ko kiftawa batayi alamun tayi nisa a tunani, saida ya kwankwasa tebur din sanan ta dan firgita ta kalleshi, yayi mata sallama sanan ya tambayeta me takeyi a nan ta zauna ita daya ta buga uban tagumi ko lafiya, ta cire tagumin ba tare da ta kalleshi ba tace "bawan Allah dama ka tashi ka tafi yin aikin dake gabanka daya fi maka, a yanzu the last thing i realy want 2 do is talk" yayi murmushi sanan yace "nayi sallama baki amsa ba na miki tambayan meke damunki baki ban amsa ba a maimakon haka ma sai kike nufin korata, daga son jin matsalarki shine nayi laifi?" sai a lokacin ta dubeshi tana mai kallo a tsanake ya gyada mata kai alamun yana sauraran ta, tace "naga alamun natsuwa a tattare da kai idan aka auna da sauran da suka dinga tambayana babu wanda yazo da sallam daga baya ma idan na fada musu matsalata sai suta mun dariya to ni abunda bana kauna kenan, idan ka tabbatar bazaka mun dariya ba zan fada maka abunda ke damuna" yace "nayi alqawari" "shikenan, takarda ta mai muhimmanci na batar shine nake nema almost a week ban sameshi ba" ...........

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now