Kakkarfar Alaka Part 6

161 11 0
                                    


                       🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 06 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆

Haka ya buwayi rayuwata ban isa na zauna a kitchen ko tsakar gida ba haka zai yayameni ya takuran, danaga matsawar tashi ta isheni sai nace mishi to yayi hakuri tunda sona yake ya bari na kammala karatuna sai yaje kauyenmu ya aureni ya gina mun gida koda daki dayane na zauna don bazan taba hada kishi da uwargida na ba, ni a tawa shirmen sai na gama karatuna takarduna a hannu idan na koma dikku nida katsina hatta nana. Muna shirin fara waec baban Aliyu ya rasu wato mahaifin auty rukkaiya duk muka garzaya gombe bayan sadaqan uku sai baban amiir ya soma shirye shiryen komawa bakin aiki nima washe gari zamu soma zanar paper sai ta hadamu muka koma tare da niyyar bayan sadaqan bakwai zata dawo itama ta koma bakin aikinta. Bazan taba manta da wanan bakin lokacin ba don da nasan abunda komawata zata haifa dana sha zamana na hakura da wanan paper din har lokacin da maman amiir zata gama mu koma tare, a daren ranar bama washe gari ba mara imanin nan ya mun fyade(kuka). Ya lalata mun rayuwa ya yagalgala mun sirrina ni zaliiha na rantse da Allah bazan taba yafe maka ba baban amiir, nayi kuka har na gode Allah, barci ranar nemansa nayi na rasa saboda duniya duk tayi mun kunci tayi bakikirin ba abunda nake tunowa sai mamana itama haka ta gama rayuwarta saboda rashin budurci ta zabi ta gama rayuwarta a bauta akan taje ta auri wani ya tarar da ita a mace kunyar duniya ta ishe ta yanzu nima haka rayuwata zata kare? Shin ina imanin mutane ne?. Allah ya isa baban amiir....... A dai dai nan wajen umar ya ja wani gauron numfashi, idanun shi duk sun sauya launi sun koma ja kamar gauta yayi saurin rufe littafin ya rintse idanunshi yana karanto kalmar innalillahi wa inna ilaihirr rajiun.!!!

Ji yayi zufa nata keketo mishi ta koiina, bacin rai yayi saurin yi wa zuciyarsa dirar mikiya , ya dunkulle hannunshi na hagu ya kai wa tafin na dama naushi "wanan wani irin shegen mutum ne haka? An ba kai da matarka amanar yarinya amma ka rasa wacce zaka keta wa haddi sai ita? Jikin matarka bai ishe ka ba sai ka hada dana inocent girl wacce bata san komi ba" ya buga wani uban tsaki, mita yake tamkar shi baban amir dinne a gaban shi. Yana kan maganganunshi yaji an kira sunanshi da karfi yayi saurin waigowa ta inda yaji kiran, habib ya gani tsaye ya harde hannu a kirji ya mishi kuri da ido, sai a lokacin natsuwa ta soma ziyartar shi, kalan idanunshi suka soma washewa yana neman daidaita kanshi sanan yace "yaushe ka shigo, banji sallamarka ba" ya karaso gaban shi da kyau ya tsaya yana leken fuskar shi "umar lafiyanka lau kuwa? Tun dazu fa nake ta faman kwankwasar kofa naji shiru da ba don mami ce da kanta ta fada mun kana nan ba da sai na karyata, hargowarka cefa tasa nayi shigowar ba shiri na tarar kanata mita nama zata a waya ne sai dana kara lekawa naganka kai kadai. Anya bakayi gamo da aljanu ba kuwa?" ya kirkiro murmushin dole sanan yace "abokina yi hakuri, duk tension ne amma wait! Neman me kake mun ne wai inji farida?" ya jinjina kai don yasan halin umar tamkar yunwar cikinsa, muddin baya son magana to sai ya dinga kwana kwana yana basar da zancen "anyway kai ta shafa koma menene tunda kaki fada mun, kayyakin da nayo odar su ne abokan aikinka suka amshe mun shine nakeso ka dubo mun kada nayi asarar su" "shikenan jirani na dan watsa ruwa sai muje,i'll see what i can do about it" ya tura takardan a cikin bedside drawer dinshi na chan lungu sanan ya sake watsa ruwa ya chanja sabbin kaya suka fice tare da shi........ 

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now