🎆🎆🎆🎆🎆🎆. 26. 🎆🎆🎆🎆🎆🎆
A hankali a hankali na dinga tanadin kayan aurena ba tare da sanin kowa ba saboda nasan ko sama da kasa zasu taru su hadu alhaji bazai taba barina nayi aure ba yanda yaci buri da karatuna sanan ko ya Al'amin bai soma kirgen zancen aure ba bare ni da ko masters dina ban soma ba. Ana cikin wata hudu da gama service dina naji kiran maryam a wayata abunda ya mutukar bani mamaki saboda kusan a kowanne lokaci ni nake kiranta, tana amsawa naji muryarta cikin tashin hankali nayi saurin tambayanta me ya faru a lokacin ta sanar dani wani labari mai kidimarwa na bata hakuri akan zancen aurena da ita babu babu ja da baya saboda haka ta kwantar da hankalinta zan sanar wa da mahaifina abunda ke faruwa. Dana sanar wa mahaifina abunda yake faruwa sai a nan nayi baban kuskure saboda ban fada mishi batun cikin ba gudun rikici naso sai sun amince har an soma shirye shiryen sanan nasan nayi. Mahaifina ya kekashe kasa yaki amincewa dana cigaba da magiya ma marina yayi yace na fice mishi daga gani, da daren ranar na kirata nace ta kwantar da hankalinta a cikin sati mai zuwa zan zo kauyen mu san shawarar da za'a yanke abunda ban sani ba shine mahaifina ganin zagewata akan maganar auren ya bashi tsoro shiyasa yayi saurin hada mun visan canada cikin satin. Ina zaune kawai sai cewa yayi zan raka shi turai wani business trip, da farko nayita basarwa saida mama ta sanya baki na amince saida muka isa ya kwace visa dina da duk abunda zai iya sadani da 9ja sanan ya baro ni chan tare da wanda ya ajiye gadina koda zan yi yunkurin guduwa. Na gwada hanyoyi na dawowa amma babu wanda nayi nasara a ciki haka na hakura na rungumi karatuna badon naso ba saidai domin nayi na bar garin zan koma wajen abar so na. Ban taba manta da son da muke wa juna da maryam ba a wasu lokacin idan na tuna da halin da take ciki da kuma ajiyata dake cikinta sai nayita kuka ina nadamar abunda muka aikata sanan babu abunda ke kara daga mun hankali kaman ganin da za tayi guduwa nayi dama bana son aurenta shiyasa nayi guduwa abuna. 1st semester ya kare na zata alhj zai taho ne kokuma ya aiko da al'amin da takarduna amma sai naga mutumin da aka bari yayi gadina yazo ya daukeni ya kaine wani dankareren gida yace ga gidan da alh yace a siya mun da kuma credit card na bukatun yau da kullum a lokacin nasan eh lallai alh dagaske yake ya rabani da 9ja. Ina shekarata na biyu na hadu da wata kaska mai bin jiki wai ita kubra, tunda ta ganni ta nanike mun a wajen duk inda na cire kafa muddin tana wajen to a wajen zata saka nata. Tun ina shareta har muka soma dan shiri saboda tanada rayuwa mai sauki sanan gata da abun ban dariya kuma gwana ta fannin shagwaba, mukanyi karatu tare amma a matsayin kanwa na dauketa babu komi sai shi. Ashe duk abunda ke faruwa wani saurayinta mai tsananin sonta amma tana gwasaleshi dan jamaica na biye dani yana fakona, ranar ya tareni a wani layi mara hayaniya bayan na fito mike kafafuna shida abokanshi suka nada mun duka sanan suka shakar mun da cocain mara iyaka suka barni a wajen. Bansan yanda kubra tasan ina wajen ba amma ita ta kira gida ta sanar dasu abunda ya faru, a takaice dai daga ranar na rasa hankalina na zama lafiya lau ba lau ba. Anyi maganin asibiti anyi na gargajiya duk a banza domin al'amarina yaki kyau shiyasa kawai aka dawo dani gida aka cigaba da jinyana nafi shekara ishirin ina jinya kowanne mai magani yazo ya gama gwanintan shi ya gama sai daga baya wata karamar yarinya mai bada magani a bauchi ta bani shikenan na warke murus. Tunda na dawo hankalina babu wacce nake ambata sai maryam maryam daga baya ma dana tuna da cikina a jikinta wanda idan ba wani kaddara ba nasan ta haife sai na cigaba da maryam da da'na. Inata jinyar lafiyata har na warke ssai sanan na buga mota sai gombe babu wanda na fada wa, ban sha wahala ba wajen samun gidansu ba saboda tundama na sani amma sai na tarar wai sun bar garin kuma ba'a san inda suka koma ba nace ita maryam din ta taba haihuwa sai tace eh wani dan bautar kasa ya mata ciki ya gudu ta haifi ya' mace aka saka mata zaliha, anan nayi hamdala tunda naji ta haihu kuma naji jinsin harda sunanta. Na dawo gida cikin tashin hankali na tarar har an soma cigiyata, na birkice musu a gidan babu wanda ya gane kaina sai da alh ya dawo ya tarar dani a haka yake tambayana me nake so nace ai shi ya jamun duk halin da yake ciki da ya barni na aure yarinya da lafiya lau nake amma yaki ya turani turai wani dan iska ya illatani a banza da wofi babu ilimin banu takardun gashi na dura wa yarinya ciki. Daga jin kalmar ciki duk kowa ya dafe kirji da ambaton ciki? Cikin karaji nima nace "eh ciki har na wata hudu ma kuwa kuma nawane a da nayi dana sanin aikata abunda nayi amma yanzu wlh murna nake saboda an hanani aurenta amma gashi harda ya' a tsakanin mu" salati suka dauka a dakin al'amin ya mike cikin fushi yace mun "kana hauka ne zaka dube fuskar mu duka cikin bagu ka fada mana kanada ya' kuma bata sunna ba" nayi murmushi nace "abunka da wanda ya warke kwanannan daga ciwon hauka watakila ma ban gama warkewa ba a mayar dani asibiti a chaining dina a dakin mahaukata sanan na dawo hankalina" ya daukeni da mari amma ko gezau banyi ba hasalima cigabawa nayi da fadin abunda nayi niyya "babu wanda ya ja mun halin da nake ciki sai alhj saboda haka yau zan fada a gabanku kowa ya shaida muddin baza'a nemo mun ita ba to zan tattara duk komatsaina na bazama duniya ni kadai. Nayi shekaru fiye da ashirin a matsayin mai tabin hankali so i knw no one wuld miss me saboda haka ma nasan babu hankalin kowa da zai tashi amma ko nan gaba babu ni babu kowa a zuri'ar gidan nan banida jini ko daya a zuri'ar nan" na fice daga palon na hada yan kayyakina da sharadin bayan kwana biyu idan ba'a dau kwakwarar mataki ba zan bazama nemanta da ya'ta. Koya suka kare oho a washe garin suka yanke shawarar zuwa neman su a lokacin ne labarin ya kai kunen hajara a nan garin tace akwai wata zaleeha data zauna gidan tahir amma a bincike zuhuriyya domin batasan ko ita bace. Kan tahir ya kulle domin ko shi baisan tarihin rayuwarta ba, sirrin tsakanin su suka barshi, saida zuhuriyya tazo tabada tarihin labarinta akaga sun rythming. Tayita kuka tana dana sanin korarki da tayi amma aikin gama ya riga ya gama kawai sai na dawo gida na rungumi kaddarata domin nasan kun mun nisaa kwatsam dazu sai ga hajara hankali tashe wai kunshin da akayi jiya asma'u ta batar da zobenta gata chan ta daga musu hankali suka bazama neman shi da kyar suka sameshi a wajen flower. Kallo daya nayi wa zoben na gane cewa tawa ce don ga rarrufan sunana akai na tambayeta waya ba asma'u wai bakuwa ce nace mata dan Allah duk ranar da suka hadu da bakuwar a sanar dani akwai yan tambayoyin da zan mata sai gashi ta kirani wai tana nan a cikin gidanta nayi saurin garzayowa na duba ko zan dace ashe ya'tace ma zan gani" yayi ajiyar zuciya "dole ta tsane ni tsana mai tsanani domin kowa ma yana zargin nayi wa mamanta ciki na gudu ballanta ita da abun ya shafa, nidai fatana su fahimceni dukkansu su san ba'a son raina komi ya kasance ba na nema gafarar su ko zan dace ya'ta ta kaunace ni".
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.