🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 28 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Washe gari da safe bayan ta fito daga wajen meeting kawai sai ta wuce gidan habib domin ta cika alqwarin data dauka, ta tarar ma har baban ta ya so yana jiranta, hajara tace''ni har na soma cire tsammanin ma zaki zo '' tayi murushi kawai sanan baban yace ''muje ko'' suka wuce. A ranar zalleha ta tabbatar da cewa ita yar dangi ce gaba da baya saboda kowa sai faman nan da nan yake da ita bare kakanta da akace za'a rabu dashi muddin ba'a ganta ba ai dole yayi murna da ganinta, kwatsam kawai sai gata a gaban zuhuriyya, cikin murna ta rungumo ta zuhura na hawaye tace ''zaleeha ki gafarceni korarki danayi na so kaina dayawa zaleeha ashe ke ya'ce ma a gareni ban sani ba tana share mata hawaye tace ''babu komi aunty, ni baki ma mun komi ba idan har akwai abunda kika mun to shine taimakon rayuwata da kikayi kika inganta munshi har nayi degree shin aunty wacce gata tafi wanan? babu saboda hala ki bar damuwar kanki wlh ban rike ki a zuciyata ba tunda kafin na tafi kinban chance kuma na zaba kuma kika hadani da makudan kudade ba wai korata kikayi haka nan ba sanan abu mafi muhimmanci kika hanani auren kawu na shin me yafi haka'' ta jinjina kanta ''hakane amma duk da haka ki dai yafe mun saboda consience dina wuld neva be cleared idan ba wai hakan ba'' ''shikenan aunty na yafe miki yanzu dai ina kanne na suke?'' '' karatu ya hanani zuwa dasu amma ai zaki zo gidan mu kiyi mana hutu koh?'' ayi murmushi ''karki damu aunty zan zo da yardan Allah'', wuni tayi curr ana zagawa da ita dangi kowa naso yaga kwan abubakar tillo kwaya daya a rayuwar shi, kyaututukan data samu kam sai sambarka ala bisa dole ta amince ya kaita gida akan washe gari ta bawa umar mukullin ya kawo mata,tunda zaleeha ta fada ma mamanta tare suke da babanta taji duk ta brkice ta kasa zaune ta kasa tsaye, sallamarsu yayidaidai da faduwar gabanta na bakwai. Ya kura mata ido na tsawon lokaci yana aiyyano kammaninta kamar yanda itama take aiyyano nashi, zaliiha data lura hankalinsu yayi nisa sai ta jijiga kanta ta sulale ta barsu a wajen dama da walakin ya nace akan shi zai kawota gida daman domin su dinke ne da tsohuwar budurwarsa kuma masoyiyarsa. ita ta soma samo natsuwarta tace ''abubakar zauna mana ka tsaya'' ya ja gauron numfashi ya dawo a hayyacinshi sanan ya samu waje ya zauna suka soma gaisuwa a lokacin zaleeha dake makale a bayan labule tana ta faman leken su ta gintse dariyan dake makale a makoshinta ta shigo ta jera mishi abun sha akan table din gefen kujerar da yake zaune sanan ta koma shashin ta tana duba abubuwan data taho dasu. Shiru ne ya ziyarce cikin falon sanan yace ''maryama nawa kenan har yanzu na kasa gasganta cewa kece a gabana, sai yana mun kaman mafarkin dana saba yi ne sai na farka naga wayam babu ke, nayi kuka nayi kewa nayi dana sanin abubuwan daya faru a tsakanin mu da kuma guduwan da kikayi tunanin nayi wlh ba hakan bane'' tayi saurin dakatar dashi tace'' ni tun asali banga laifin ka ba akan abunda ya faru saboda ni na kai kaina ga halaka na daya kenan na biyu shine nayi dana sanin aikata zunubi kwarai da gaske amma bana dana sanin cetonka danayi sanan kuma bana dana sanin samun zaleeha ko ba komi takan deba mun kewar rashinka kaga sai ka cire wanan tunanin a cikin ranka'' ''shikenan na cire amma nazo nan neman wani alfarma dan Allah zaki iya mun?'' ta daga kafadunta alamar ko oho sanan tace ''ya danganta da koma menene'' saukowa yayi daga kan kujerar ya durkusa mata gwiwa biyu yace'' so nike ki bani dama bayan auren yarinyar nan a daura mana namu, wlh nakasa rayuwa da wata ya' mace banda ke shiyasa kikaga har yanzu ina gauro na kuma kema ga alamu dukda bansan ko kin sake wani auren ba mijinki ya mutu kokuma kuka rabu amma as for me naki yi ne saboda bana ra'ayin kowacce banda ke ki taimaka mun'' tayi ajiyar zuciya domin ya sosa mata inda ke mata kaikayi tace ''shikenan zanyi shawara sai ka surari amsata'' ''Allah yasa muji alkhairi'' '' amiin!''. Gadan gadan aka soma shirye shiryen auren zaleeha da umar dinta, amarya ta sha gyara ba laifi dukda kasancwarta ba budurwa ba amma haka ango ya gani yakeso. An daura auren su a wata safiyar asabar wanda dumbin jama'a suka shaida cewa sun zama mallakar junansu a bisa shari'ar musulunci. sun gina rayuwar aurensu cike da so,kulawa aminci da kuma yarda a tsakanin su saidai muce Allah ya kara musu zaman lafiya, amiin.Bayan watanni biyu aka sake dura auren masu tsohon soyayya wato maryama da kuma abubakar amma akan sharadin bazata bar gidan da take ba saidai ya bita saboda tana zaune da ja'afar kuma bata son rabuwar su kuma ya amince suma din saidai na musu fatan alkhairi Allah ya bada zaman lafiya mai dorewa.
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.