Kakkarfar Alaka Part 12

127 8 0
                                    


                  🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 12 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆


 Ya mugun ban tausayi don nima karan kaina naga yanayinshi daban dana ranar dana soma ganinshi, kalamanshi masu taushi ba irin na baban amiir ba da a kodayashe bashi da kalma data wuce ta jikina amma ya zanyi? Bazan iya cin amanar uwargida na ba don ta mun hallacci ssai,"kayi hakuri Alhj ba wai ina kinka bane wlh baka da makusa a ratuwarka, aurenka ne dai bazan iya ba saboda hajiya ta nuna mun matarka nada muhimmanci a rayuwarta, ina tsoron a kira ni da kalmar munafuka ko mayaudariya bayan an mun rana ni kuma nayi mata dare sanan an sha fada mun kiyayyar dake tsakaninta da kishiya. Bana fatan nayi auren da za'a hanani zaman lafiya karshenta ma na fita" "ki daina ma wanan zantutukan don basu ma kamaxe ki ba, ni namiji ne ba mijin tace ba, na isa da gidana so zan iya auran duk wacce nake so how i like it kuma when i like, babu wacce ta isa ta sakani kokuma ta hanani sai mahaifiyata kuma na san ita mai son duk abunda nake so ne so ki fidda wanan tunanin a ranki. Zan aure ki bazan ma hadaku gida daya ba, idan kina ma so ko gari daya bazaku zauna ba don farincikinki nake so ba wani abu ba pls ki amsa wa bukatata idan ma kinaso zan iya baki lokaci kiyi nazari akai" na durkusa mishi gwiwowina akasa nace "kayi hakuri ka rufa mun asiri,babu sauran tunanin da nake bukata, aikatawa ne kawai bazan............" sauran kalaman suka makale a makoshina a sanadiyyar bankado labulen da akayi, hadiyan yawu nayi da kyar wanda yazo daidai da birgewan da cikina yayi saboda firgitan da nayi. Hajiya ce da wata mata, sai haki take ita kadai sai kace wacce tayi guduwan fanfalaki tace "ai dama nasan da wata makarkashiya a kasa tunda ka daina cin abincina kwana biyu idan ka dawo ma kace ka gaji ashe nan kake zuwa ko, sanan naji tana wani babatun a rufa mata asiri wani abun tayi da takeso a rufa mata?" babu shakka bare tsoro yace "son ta nake, a takaice ma aurenta nake sonyi ko da wata matsala ne?" da sauri na kalleshi saboda ban zaci wanan amaan daga garrshi ba, amma lallai mutumin nan da karfin hali yake. Ta wani lailayo wata uban ashar,ta sunce gyalenta ta ci damara dashi saboda tsaban bala'i ko cikin jikinta bata ji dashi ba ta soma dure duren ashar akan idan ta yarda Allah ya tsine mata mai ya mutu ya dawo. Nidai ina durkushe a kasa har a lokacin babu abunda nake sai kuka, abunda na dade ina tsoron zuwan shi yau gashi ya auku ko ina mafita?. Ganin hargaginta na neman janyo mishi jama'a abunka da gidan abinci saurin taro ba wani abu bane mai wuya sai ya dubeni yace "kiyi hakuri zalii zanje na dawo, karki damu babu mai raba mu" ya dubeta babu ko alamar fargaba a fuskar shi yace " bawai kinzo nan kina neman tara mun mutane ba zaki fuskanci hukunci mai tsanani, kuma da izinin uban wa kika fito daga gida bayan nayi nayi ki zo muje gaishe da innata kika ki wai bazaki iya tafiya ba amma a nan kinada karfin masifa ko? Ba wai kin sha damara bako? to bari kiji, wlh wlh wlh, tunda kika wulakanta mun mahaifiya kema saikin ji a jikinki kuma muddin kika kuskura kika yarda na isa gida kafin ke to a bakin igiyarki daya rass, gobe ma ki fita bada sanina ba ki gani, haka zandinga tsinke su one by one har sai sun kai karshe ki kara gaba na gaji da halin fitsara irin naki aina'u, baki faranta mun so babu yanda zaki hana wata ta faranta mun tunda ba ke kike aure na ba nina dama dake saboda haka dole na fada kiji" ya juya ya fice ya barta a tsaye nan gumi ya gama wanketa wanan bakin masifar ji kake kuss ba laka. Babu mafita haka ta juya tabi bayanshi a motarta ko ya suka kare oho don ban sake haduwa dasu ba har yau suma din. Hajiya ta shiga kwaso kayana a daki tana kutubal dasu a waje wai ta dauko wa kanta alakakai wace take niyyar kwace wa kawarta miji gata da shegen kyau kamar na yar sarkin aljanu wahala baya rage shi koda kadan ne. Nayi kukan, nayi magiyar, nayi rantsuwar rashin sanin, nayi rokar amma duk a banza hadani tayi da kartinta masu mata aikatau manya suka tarkata keyata dana da'na zuwa karshen layi sukace koda wasa na kara bin koda hanyar ne sai su tsireni da rai............

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now