Kakkarfar Alaka Part 11

137 11 0
                                    


              🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 11 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆


 Tafiya nake ina faman waige waige na wanda har yau na kasa gane dalilinta, wani corola S yazo ya giftani sai naga yayi ribas, sai na daga kaimi wajen sauri don a yanzu ba tsayawa da mutane bane a gabana. Yayi saurin kiran sunana da akasarin yan gidan abinci suka sanni dashi wato "maman jj" shiyasa na tsaya gami da lekawa naga ko waye. Alhj mubarak ne wato mutumin ranar, na fadada murmushin fuskata na gaishe shi ya amsa hadi da tambayana "dama a nan unguwar kuke da zama kike zuwa har chan aiki" na girgiza kai "na kawo ma wata kawata ce ziyara" ya gyada kai,ya bude mun kofa yace "shiga muje na dropping dinki a shago don chan nake da nufin bi sanan naje inda nayi niyya" gabana ya fadi, a ganni a motarshi nace mene? nayi saurin kakalo karyar karfi da yaji "ah ah ba wajen na nufa ba cikin gari zani dama ka mayi tafiyarki" ya hada gira "i insist! ki shigo na ajiyeki koda a ina ne don nasan unguwar mu da wahalar samun abun hawa so shigo muje" naja shima ya ja, ganin har ranshi ya soma baci kada ya kaini kara wajen uwargida na shiyasa nayi shahada na shiga ciki muka wuce, tafiyan kurame muka soma yi daga baya idan ya mun tambaya saidai na amsa da eh ko ah ah don kwata kwata a tsure nake a motar. Muna fakin hajiya na lekowa da fara'a a fuskarta kasancewar ta san motarsa amma saukowata daga gefen seat dinshi tuni annurin fuskarta ya gushe, na gaisheta kawai nayi wucewata ciki, da dare tazo tana tambayana ta yaya akayi haka? Nikuma na mata bayani tsakani da Allah, ta nuna ta amince amma daga ganin yanayin fuskarta nasan akwai boyayen al'amari a kunshe a ciki daga baya ta karasa da "wanan mutumin mijin kawata ce kut da kut, ni bazan lizamci cin amana ba gaskiya saboda aina'u tayi mun halacci ssai a rayuwata", nidai bance komi ba don koda na fada bazai chanja mata kallon da take mun ba Allah dai yasan gaskiyan abunda ya wakana. Alh kuwa tun daga ranar sai ya mayar da shagon mu wurin cin abincin shi, tun ban hango ba har na hango kuma na gamsu wato dai shima sona yake yana neman tada mun rigima tana barcinta lami kalau. Ganin yawan zuwansa sai hajiya ta soma chanja mun fuska, faram faram din da take mun ya ragu, nima sai na chanja taku duk ranar daya zo shago sai na nema excuse din da ba nice zan serving dinshi ba, ya karaci hange hangenshi ya kara gaba. Ranar dai kaddara ta data saba faruwa ta auku a kaina. Ina cikin aikina naji sallamar shi saida gabana ya fadi kasancewar ranar sunday ne kuma sauran abokan aikina christians ne basu zuwa so duk ranar sunday ni nake koman shagon don hajiya bata cika zama ba a ranakin weekends. Haka dai na daure na fito na gaishe shi gami da tambayar shi me yake so, ya mun kuri da idanunsa masu matukar kyau har na soma tsarguwa. Na sake maimaita tambayar yace "ya kamata ace kin san abunda nafi so don a kodayaushe nazo nan shi nake siya" har zance "ban sani ba" sai na tuna neman hira yake nikuma am not in d mood kawai sai naje na sako mishi tuwon alabo da miyan wake ya sha kifi masha Allah nazo na dire mishi na dauko ruwa da kofi na ajiye mishi, na koma bakin aikina sai ga jafar ya shigo daga islamiyyanshi, ya wani yafito shi ya zaunar dashi kan cinyar shi to tare suka cinye nidai bai shafeni ba. Yana gamawa ya kirani, na fada mishi kudin ya ajiye akan tebur na kwashe,yace "wato ke zaliha naga baki da matsalar komi ko? Kinata wahalar da bawan Allah ko tausayinshi bakya ji" na ko hada rai saboda ma kada yaga fuskan ambatan abunda na dade ina gudu "ban fahimce me kake nufi ba" yayi murmushi "zali na dade da sanin kin fahimce ni, kawai kwana kwana kike sonyi mun amma tunda hakanne bari na furta, na dade a cikin mayen sonki, Wallahil Azeem na fara sonki tun ranar dana soma ido biyu dake, tun a ranar na nema sukuni na na rasa,banida buri saidai na ganki a matsayin matata. Ki taimaka wa rayuwata ki amsa tayina,na miki alqawarin bazakiyi dana sani ba".

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now