Kakkarfar Alaka Part 29

97 7 0
                                    


                             🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆. 29. 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆

Cikin jikin zaleeha nada wata bakwai ranar ta kai ziyara gidan su domin bata cika sati basu je lekasu ba dukda gidansu akwai dan tazara amma gidan iyaye baya taba nisa koda a nesa kake ballantana ma gari daya, sallamar da zatayi tayi ido hudu da baban amiir,wani tukukin bakin ciki ya tokareta a wuya ganin ya wurga mata murmushi, shiru tayi bata ce komi ba ta wuce cikin kitchen da tulelen cikin jikinta, ta nemi gatari a backyard din sama da kasa ta rasa tasan aikin mamanta ne saboda cewa da tayi sai ta sare kafafun babanta muddin ya tako kafa gidan, ganin babu mafita kawai ta rarumo tabarya da karfinta ta nufeshi gadan gadan suka soma zagayen falon yana dingisa kafafu tana cewa ''yau sai na rabaka da numfashinka domin muddin ba haka nayi ba hankalina ba zai kwanta ba'' mama kam ta ma rasa abun fada sai rusa ihu take akan a kawo mata agaji zaleeha zatayi kisan kai cikin saurimai gadi da direba suka kawo dauki suka kwace tabaryar a hanunta tanata faman haki dukkansu sun hada uban zufa a lokacin ta fashe da wani kuka mai ciwo ''Wlh Allah ya isa tsakanina da kai duniya da lahira akan abunda ka aikata mun a rayuwa wai shin meyasa baku da imani ne? sai bayan kunga mutum ya tsince kan shi a farinciki sanan ku dawo har kun isa ma ku kira mutum da danku ? toh dan ubanka baka isa ba wlh kayi kadan sanan albishirinka kasan wani makaranta na kai jj kuwa? to NMS Zaria na kaishi wanda daga nan zai ta cigabawa a rayuwarshi har ya zama ingarman soja wanda kuma kasan menene dalilina na aikata hakan? to saboda kaine ya girma ya harbe mun kai ya huce mun takaicin abunda ka aikata mun a rayuwarta wanda kaida samin natsuwa sai a darul salam shima din idan ka aikata mai kyau kenan amma with the look of things tun daga hakkina daka danna kai.........'' mama ce tayi saurin dauketa da marruka uku masu ji da rai har saida taga walkiya itama tana kuka tace ''haba yar nan. akan wani dalili kika bari wadanan kalamun suke fitowa daga bakin ki haka. shin ke a rayuwarki baki san yafiya bane ko mene? Wai meyasa ke a kullum sai an dauka ba dadi dake sanan ki saurara wa mutum eh?'' '' Ai dole kice mun haka mama, nifa suka sabamawa dukkansu na baba na mishi uzuri amma wanan fa uzirin mene zan mishi akan abunda ya aikata?'' ta juya gareshi ganin bacin ran fuskanta saida ya sakashi ya tsorata gamida jan baya incase zata sake son kasheshi, tace'' yafiya koh to kai da jin wanan kalmar har abada sanan duk ranar dana kuskura na kama kafafun nan naka a gidana to kasan cewa ka zama obituary'' ta fice daga gidan a guje ko kallon mijinta dake kokarin parking batayi ba tayi wajen gate. 

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now