Kakkarfar Alaka Part 10

154 9 0
                                    


                        🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 10 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆


 JJ nada sati uku itama ta sauka shima namiji, aka dinga nan da nan da ita wanda ya saka zuciyata ciwo, dama nice. Ranar suna rufe shi nayi a dakina na dinga yawo da mukulli dama bashi da kukan banza, tym to tym nakan zo na leka shi na bashi nono gudun kada na shiga hakkin shi, aka rada wa jinjiri "JUNAID". Muka cigaba da renon yayan mu tamkar kishiyoyi masu miji daya, kodashike ai dan nashi ne, duniyace kawai basu sani ba. Da'na nada wata shida ranar ta tattara nida komatsaina muka fice daga gidan, gidan abincin wata hajiya ta kaini tace mijina ne ya rasu shine nake neman yanda zanyi na tallafa rayuwar mu saboda nace mata bazan koma kauye ba kawai ta nemar mun aiki a wani wuri. Ta cigaba da fada mata am very hardworking banida son jiki ko kadan, matar ta amince da cewa zata daukeni harda daki daya da zamu dinga kwana. Maman amiir ta fito dani waje mukayi sallam tare da jajjanta mun cewa kada na kuskura na kara dawowa gidanta don tana tsoron maganar mutane, ta bani wasu yan kudade sanan ta fice, itama wanan shine ganina da ita na karshe don ban nemeta ba kuma itama bamu kara haduwa ba. Na soma aiki da hajiya salin alin, aikin gidan abinci dana gidan cikin da basu wuce hudu ba akwai bambanci amma haka na zage damtse na na soma mata bauta domin neman tsira da cikina dana dana. JJ nada shekara daya da rabi ya soma ja mun magana saboda iyayin shi, idan ya shiga cikin shago mutane sun dinga kiran shi kenan suna "hajiya ina kika samu kyakyawan yaro haka, daga gani mamanshi ma zatayi kyau" hajiya kuma sai tace "wlh maraya ne mamanshi yar aikina ne" sai su ce "ai ina ciki a dan mun hanya mana ko zan dace" idan ya tashi shigowa sai ya shigo mun da uban kudi wai inji su,na hana shi har na gaji abunka da yaro. A lokacin da mukayi shekaru biyu a wajen ranar da abun ya isheni na zazzare mishi idanu hannu na rike da kunnen shi domin maganar da nake ta shiga da kyau nace "kasan Allah muddin ka cigaba da karban kudin mutane bada sani na ba zan tafi na barka ko, zan tafi duniya daban kai kuma na barka a nan koda yanka ka za'ayi bazan waiwaye ka ba, kana jina ko" kasancewar a lokacin ya soma wayo kuma yasan koda kasuwa naje ban dawo da sauri ba har ya tashi daga barci ya dinga ihun maman shi kenan har sai na dawo tuni ya fashe da kuka yace ba zai kara ba, na zake jan kunen da kyau "kama kara mana ka gani sai ka bude ido kaga babu ni sanan ka gasganta abunda nake fada" na tura shi daga jikina ya fadi gefe na juya mishi baya na cigaba da abunda nake. Ranar dai wuni yayi a daki ko wasa bai je ba gani yake kamar guduwan zanyi dagaske na barshi, daga ranar bai sake ba koda an matsa mishi saidai ya saka musu kuka dole suka rabu dashi sanan na samu sukuni a raina. Ranar na dawo daga kasuwa ina nufin shiga shago na lura da wani jeep lexus 300 an parker shi a gefe, banyi karambanin lekawa ba nayi nufin kutsawa cikin shagon sai naji ance "baiwar Allah ji mana" na juyo gareshi bai sauko ba windown ya saukar ina iya hango shi, a shekaru dai zaiyi arbain kokuma da daya, wankan tarwada amma mai haske, saje ta mai rumfa a fuska, irin su ne da suke gangariyar samartakan su yan mata sunyi rububin su, a yanzun ma dai nasan baza'a rasa ba, na kawar da tunanin da nake nace "ni?" ya gyada kai "a cikin nan kike aiki?" saida na juya na kalla shagon sanan na waigo nace "eh, kaima kazo siyan abinci ne?" "eh, amma zanfi so ki kira mun hajiya don ita nafiso ta serving dina" na gyada kai naje na isar da sakon shi bayan na ajiye kayan dana siyo naje na kama aikin wanke wanke, sai da dare naji hajiyan tana fada mun wai matar shi abokiyar ta ne kut da kut,ana kiranta haj Ai'nau yanada arziki ssai sanan ita matar yar hutu ce gashi Allah kasheta a mata kishiya, ta tsaneta kamar yanda ta tsana mutuwarta. Yanada kyankyami ssai gashi matar nada juna biyu laulayi na hanata ciki shiyasa yake daurewa yake zuwa siyan abinci don aiki baya barinshi ya girka da kanshi, na dai gyada kai na cigaba da tsintar agushi, babu ruwana da harkarsu wanan su ta shafa. Ranar wara lahadi naje kasuwa na yanka wa JJ uniform don inaso ya shiga islamiyya kada ya zauna dukkansu biyu babu ina dawowa nace wa maimashin ya kaini tsohon layin mu, bayan ya ajiyeni yayi gaba sai na soma takawa. Nayi kewar unguwar ne ssai shiyasa naje, yanayin unguwar na mun dadi, very quiet, peaceful n serene, ba hayaniya ko kadan amma dana san kaddarar da zata gifta mun da ko kasuwan banje ba ranar.

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now