🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 19 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Yayi murmushi "banda abinki, ai akwai wuraren sayar da takardu kala kala a garin nan, ai abune mai sauki ki siya sabo wanda ya fishi kyau bayan kullum cikin buga sabon yayi ake" ta girgiza kai "bazaka fahimta ba, wanan takardan daban ne, tarihin rayuwata daki daki na rubuta a ciki, its special saboda haka dole ne hankalina ya tashi. Yau kusan sati kenan ina zuwa nan ko zanyi sa'a na dace wani ya gani amma shiru" yanda take magana ta bashi dariya daba don ya karanta labarinta ba da sai yace wata asalin shagwababbiya ce katuwa da ita. Yace "to shikenan naji matsalarki,dukda ina sauri amma zan iya baki abu daya wanda nasan zai taimaka miki" ya daga hannaye sama alamun adu'a "ya Ubangiji mahaliccin sammai da kassai, ya Allah muna mai kaskantar da kanmu a gareka, ga baiwarka nan ta batar da takardar ta mai muhimmanci ya Allah idan da rabon ta gani ka baiyyanar mata dashi don darajar fiyayyen halitta" ai tuni ta amsa amiin da baban murya ta shafa a jikinta tana fara'a. Ya mike yana duban agogo,"ya kamata na wuce, a nan zan ce miki sai anjima" ta watsa mishi wani sassanyar murmushi har saida hakoranta suka bayyana tace "nagode bawan Allah adu'ar da ka mun dinnan sai naji dadi a raina kaman har na ganshi, nagode ssai" "babu damuwa, ai taimako nayi, waya san ko wata rana nima na nema taimako a wajenki" "hakane", ji yayi an chakumo shi ta baya yayi saurin janyo ta gabanshi tana dariya "uncle wai kazo inji dadi kokuma ya tafi ya barka" ya ja hancinta yace "ta yaya zai tafi ya barni bayan ga angel dinshi a nan" sai a lokacin ta hango zaliiha, ta kura mata ido sanan tace "uncle ina ka samo mai kama da mummy" "haka ake gaisuwa a garinku? Ko so kike mu bata " tayi saurin rike kunnenta ''sorry uncle'' ta gaishe ta cikin natsuwa, ta amsa tana tambayanta ya sunanta tace Asma'u tace nice name asma'u tace "aunty zoben hanunki mai kyau kuma ya miki karami zaki bani?" umar ya bude baki "angel haka akeyi, daga ganinta sai roko" ta rike kunenta ta sake cewa "sorry uncle" zalihan ta janyo ta kusa da ita "zan miki tambaya daya idan kika amsa mun i promise zan baki kin yarda?" tace "eh" Zaleeha tace "ya sunan uncle dinnan naki?" "sunanshi uncle umar" ta gyada kai "tunda kin fada mun zan cika miki alqawarin dana dauka amma kema sai kin mun alqawarin babu abunda zai sameshi, zaki daukeshi da daraja domin mamana ne ta bani" tana murna itama tace "na yarda aunty" da kyar ta cire daga dan karamin yatsan ta ta sakala mata shi a yatsan tsakiyar hanunta. Umar yace "to tunda kin mun wayo kin tambayi sunanana yanzu kema ya kamata na tambayi naki, ko zaki taimaka ki fada mun" "zaleeha" "nice name" "urs too" ya riko hanun asmau "anan nake mai ce miki sai anjima kokuma ince sai watarana. Allah ya hada fuskokin mu da alkhairi" tayi murmushi hadi da fadin "amiin", suka fice zuwa wajen mota. Asmau ta shigo sai murna take taga mai kama da mommy har zobe ta bata, habib yace "haba man, yanzu dama budurwa kaje gani ka zauna hira ka shanya mu a nan cikin mota saida na sauka na nemo mana yan abun motsa baki sanan muka gane hankalin mu. Ka kyauta kenan?" matar shi ta amsa "bai kyauta ba kuwa, rowanta yake shiyasa ma yaki kawota mu gaisa da ita" saida ya dauko littafin ya rufe kofan bayan sanan yace "ba budurwata bace, takardarta ta batar shine zan mayar mata dashi. Ka jirani bari na bata ko minti goma bazanyi ba" "a gaskiya kayi sauri domin kasan nikam banida juriyar yunwa, ehe" ya wuce ciki, ta parking lot ya dinga rabewa saboda bayaso ta ganshi har ya shiga ciki. Ya samu mai cafe din ya mishi bayanin ga littafin amma pls kada yace shine ya kawo, ya ce a shara kokuma a wani waje aka tsinto sanan ya fito ya fada mota suka wuce gida. Ya tarar mai gyara har ya kawo mishi motar gida, yana fadawa falo basma ta taho a guje ta mishi oyoyo ya cillata sama yana dariya labiba ma haka tazo ta dale shi itama, saida ya gama tsokanarsu sanan ya zauna suka gaisa da rumaisa babbar yayar su, suka taba hira ya haura yayi wanka yabi lafiyar gado. Bayan kwana biyu ya hadasu su biyu da ahmad ya wuce dasu yawo a zoo, suna kan doki kaman ance ya dago kanshi ya hangota ita da wadansu yara kanana su uku sai wata wacce bazata wuce shekaru sha hudu zuwa biyar ba zaune akan darduma suna shan ice cream sun zagaya ta cimaki kala kala a gabansu,sunata hira suna dariya daga gani tana cikin very gud mood. Kura mata ido yayi kawai yana kallonta, a kodayaushe yayi arba da ita yakan shagala da kallonta, yaji wani anuri da farinciki suna mishi marhaba a zuciya ga kaunarta ya darsu daram a ranshi. Kallonta da yakeyi watakila shi yasa ta sha jinin jikinta ta soma waige waige karaf suka hada ido yayi saurin juyawa kaman bai gane ko wacece bace, ta kawalla mishi kira da karfi ya juyo ta daga mishi hannu alamun hi shima yayi mata haka tayi saurin mikewa ta doso shi, ba murmushi kadai ta iya ba domin hatta takun da take yi cikin natsuwa abun kallo ne.
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.