Kakkarfar Alaka Part 9

141 10 1
                                    


              🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 09 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆


Kai! Naga tsangwama kala kala amma babu damuwa ba laifin shi bane, muka soma neco a lokacin manya manyan kaya nake sawa Allah ya soni banida girman ciki gashi ko laulayi daya banayi, da ba don motsin da nake ji a marata ba da sai na ma karyata inada juna biyu. A lokacin da muka gama neco cikina nada wata biyar a lokacin duk boyon da nake girma kawai yake kara yi, a ranar da muka gama teachers nata yabona da good characters dina, i was just wondering da sun san akwai cikin shegen dake neman wata shida a mahaifata bansan ko zasu cigaba da mun kallon girl din ba. A washe garin dana gama jarrabawa muka je kauye muyi hutun sati biyu, kallon farkon da kakata ta mun ta fahimce halin da nake ciki amma bata nuna a fuska ba saida kowa ya kwanta sanan ta taso ni "zaliha fada mun waya miki wanan ta'adin" na mutsisika idanuna da kyau nace "mene kenan inna?" "gaya mun waya miki ciki" gabana ya fadi rass! "ciki inna? Ni banida kome " "dubeni da kyau ni dinnan na kwan biyu a duniya ballantana ace zaki boye mun abunda nake gani a zahiri. Gaya mun gaskiya, wanchan munafukin neko?" na gyada kai "garin yaya zaliha? Bayan duk kashedin da na miki? Yanzu so kike abuda ya faru da mahaifiyar ki a kauyen nan ya faru dake?" ina kuka na shaida mata abunda ya faru. Ta gyada kai bayan na gama "shikenan, wanan kaddarar muce Allah ya bamu ikon cinyewa, yanzu inaso in sanar dake wani abu kada ki kuskura kice zaki zubar da wanan ciki domin babu laifin shi a abunda ya faru ki tabbatar kin haifo shi. Muddin kika bar kauyen nan kada ki sake dawowa sai kin tabbatar da kin rabu da shi ko ita lafiya har sunyi wayo sanan koda adoption ki kai dan wajen, ina gudun abunda ya faru bara ya sake maimaituwa. Akwai wasu kudade a wajena zan baki idan zaki tafi, koda ta kore ki a gidanta ki nema wani ki koma, Allah na tare dake in shaa Allah bazaki taba tabewa ba kada ki kuskura ki karaya kinji" ina kuka na gyada kai "abu na karshe, kome tsananin halin da zaki shiga kada ki kuskura kiyi karuwanci kokuma ki aikata wani abun daya kuskura ya savawa addinin ki kinji", har yanzu ina kallon wanan wasiyar a idanuna saboda wanan shina ganin karshe dana mata. Da muka dawo bayan kwana biyu na tarar da maman amiir a palor tana kallo kasancewar weekend shikuma gwaskan baya nan na durkusa gwiwa biyu a kasa na soma kuka, galala take kallona "zali menene haka kuma?" "aunty ki yafe mun, kiyi wa Allah kada ki gujeni" ta rikoni "me kika mun zaliha?" na daga mata bujejen dogon rigan mai hanun dana saka na nuna mata tulelen cikina, mikewa tayi a razane har tana neman dungurawa "ni rukkaiya me zan gani, zaliha kardai ki fada mun ciki ne dake" kuka kawai na fasa don ba amsa "ta saka hannu a kai "na shiga uku, zaliha abunda zaki mun kenan? Nayi kokarin sauke hakkinki dake kaina ci da sha da sutura amma all u can pay me up with is dis? So kike a ji a gari aikin karuwanci nake turaki shiyasa na daukoki daga kauye" hannu a kai ta soma sintiri a falo itama da tulelen cikinta domin ta fini girman ciki, na rike kafafunta ina kuka "aunty kiyi mun rai nima ba laifina bane wallahi fyade aka mun" ta tunkudeni "don ubanki wa zai yarda da hakan, kowafa ni zai zarga ban san hawa ba bansan sauka ba, oh ni ya'su. Yanzu inaso tun ban nada miki dukan da zai illata ki ba ki wuce ciki ki tattara komatsanki ki wuce garin ku zan baki kudin mota dana amfani nidai burina ki fice tunkan zancennan ya kai kunnen mijina". Na soma rokonta da Allah da annabi ta yi mun rai kar ta koreni kauye da cikin shege, da kyar ta hakura da sharadin bayan na haihu zata nemar mun wani wajen aiki daban saboda kada wata rana a zo daga kauye a tarar da ni, na amince. A lokacin da ta tambayeni uban wa ya mun ciki nace wani yaro ne a kauye, na fada mata hakan ne ganin ta hakura kada na fada mata mijin nata da take wa kallon salihi ne ya zurkuta mun ciki taki amincewa karshe ma ta koreni tace sharri nake neman mashi. Ko ta ya tayi ta sanar wa salihin maigidanta gaskiya oho, nidai kallonshi kawai na cigaba dayi na barshi da Allah ya mun sakayya. Ta cigaba da kula dani itama da nata juna biyu, idan ta siyo kaya nima ta siyo mun don daga baya na soma bata tausayi don bata manta abunda mahaifiyata itama ta fuskanta ba, haifan da' bata hanyar sunnah ba akwai tashin hankali, ranar nakuda ta kamani ta kaini asibiti da kanta don mijinta ya tafi turai yin wani course na shekara biyu. Na haifi dana mai girma tubarkallah, kyakkyawa kamar ubanshi, fuskar maciji domin nima haka akace mun wai fuskar ubana na dauka ko haka dukkansu suke oho?. Lafiyata na lau na haihu kamar yanda nayi renon cikinshi lau lau, ba wani complications Allah ya dauke mun shi. Ta cigaba da lura dani ina cin abinci me kyau, a ranar suna ta tambayeni wani suna nake so nace "JA'AFAR" mai lakabin JJ.....

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now