🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 14 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Sa'a tayi saurin shiga tsakanin mu tace "haba yar'uwa me ya faru haka? Me yayi zafi da har zaki marar mun masoyina ko kin mance yanda nake ji dashi ne" Abdul yayi charaf yace "ta ko mance saboda da kinji ababen da suka faru anan da bazaki ma yarda ba. Wato kawarki wai ta rasa wanda zata ce tana so sai ni, tafa nace mun wai dolen dolen sai na sota, ni kuma naki na amince nace nasan irin son da kike mun bazaki iya rayuwa ba idan bada ni ba kuma soyayya bai ce haka ba, wai abun bakin ciki wai sai me idan na yudareki? ki mutu din mana ga ki wata cus dake ko rabin kyawonta baki kai ba, shine fa don naki amincewa nace naji na gani a hakan nake sonki shine ta daukeni da wanan lafiyayen marin". Wayyo! zo kuga idanun ta saboda bacin rai, nikuwa mutuwar tsaye nayi ina sauraran wanan iblis din yana korar bayani, yayi kudina har ya sayar dani ina tsaye ina kallon ikon Allah wato Allah ya rabaka da mutum munafuki, amin. Idanun sa'a suka soma zubar hawaye ta nuno ni da yatsa "sis ke? Kece kika fada haka? Da ba don da idanuna na gano marin da kika mishi ba da ban gasganta ba. Sis sakayyar son dana miki kenan ko? Ashe so kan koma kiyayya? Sis kin bani kunya, ban taba tsammani haka daga gareki ba" maman sa'a kuwa cewa tayi "nagode zaliha, dama ance dan adam kenan ayi mishi rana yayi wa mutane dare. Nagode ssai kuma Allah saka da alkhairi, yanzu inaso ki shiga ciki ba duka ba zagi ki tattar dukanin abunda suke a mazaunin naki dana danki kizo ki fice mana daga gida. Zakiga sakayya nan bada jimawa ba",yawun bakina kafewa yayi na kasa harhada kalamai kwata kwata kaina ya cushe.. Da na karanci alamun fuskan su sai na gane babu bayani da ranstuwar da zanyi da zaiyi tasiri a zukatansu shiyasa kawai na juya na koma ciki, dama ba wani uban suturori ne damu ba jaka dayane da ghana must go na tattara dukkanin abunda nasan nawane na tasar da jafar daga barci na goya shi a baya kasancewar komi girmanshi bana gani a kodayaushe gani nake kaman jaririn jiya ne sanan ga barci kar ya dinga tafiya yana tangadi mun a hanya na fito na tarar babu su ba motar abdul wato alamu kenan na tare suka fita. Na kulle kofar na tura mukullin a inda aka saba ajiyewa na sunkuci jakukunan mu sai gareji, garin kt ya fita mun a raina kwata kwata, sau uku kenan ina zaman zamana maza na jaza mun jidali babu laifin zaune bare na tsaye shiyasa na yanke shawarar barin garin wata kila banida sanadin cin arziki ne a garin, haka muka wuce tasha motar abuja na hau domin nasan garin masu kudi ne, zan cigaba da wankau dina na ciyar da nida dana amma nida aikin gidan abinci kuma munyi hanun riga har abada. Mun iso da yamma kasancewar mun bar kt da rana sakaliya sanan ga zaman jiran fasinja, muna isowa na sauko nida dana daketa faman hamma domin ko abincin rana bamu ci ba hango wani gidan abinci shiyasa na janyo shi gefen titi na zaunar dashi akan jakar mu nace ya zauna bari naje chan na tsallaka titi siya mana abinci na dawo. Ya zauna nikuwa na tsallaka,har an miko mun shi a takeaway ina kiciniyar karban chanji kawai naji kiiiiii.......... Wato mota ya taka burki juyowar da zanyi naga jj a yashe a titi na saki kara nayi fillo da abincin nayo kanshi ina jijjiga shi, driver din motan ya sauko yana salati wata mata ta biyo bayan shi itama haka hankalinsu duk a tashe, tace ma driver yayi maza ya saka shi a mota a wuce dashi asibiti ai saboda kidima a wajen na bar jakukunan kayan mu don gani nake idan naje dauko kan na dawo har sun bace muka dukufa hanyar asibiti. Aka wuce dashi emergency na zauna akan waiting chair a waje nida ita idan banda kuka babu abunda nake saida naga an fito dashi an shiga dashi wani daki sanan hawayena ya tsaigaita matar kuma ta bi doctor office dinshi sanan ta dawo inda nake, tace "kiyi hakuri kinji, wlh tsautsayine don wanan shine first time a rayuwata da na taba kade abu ma mai rai a mota, in shaa Allah ba zai sake faruwa ba" na share hawayena "babu damuwa ai, kaddara bata bar kowa ba kuma ubangiji baya jarrabtar ka sai don son da yake maka, nidai fatana Allah ya tashi kafadar shi kada wani mummunan abu ya sameshi" ta cigaba da ban hakuri har na bar kuka sanan ta mike tace "bari naje na taho muku da abinci nasan watakila a lokacin daya farfado zai bukaci abinci" na gyada kai "nagoda hajiya Allah ya saka da alkhairi" murmushi tayi tace "baki fada mun sunan naki ba " nace "zaliha" "shikuma fa ko shima sai na roka?" murmushin dole ta sakani nace "haba dai! Wace ni? Sunan shi Ja'afar" dukkanku sunayenku masu dadi bar naje na dawo" har ta kai kofa ta juyo tace "ji mana" na dago da kaina "yanzu da baki tambayeni sunana ba ta yaya zaki gane file din bayan na family na ne" a lokacin na farga da wauta na "kiyi hakuri dan Allah kidima ce kawai ke dawainiya dani ya sunan ki" "Zuhuriyya, amma kina iya kira na da aunty Zuhrah" na gyada kai alamun gamsuwa sanan ta fice. Chan sai gata ta dawo tare da wasu yara hudu kowane rike da abu a hanun shi............
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.