Kakkarfar Alaka Part 23

102 8 0
                                    


             🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆. 23. 🎆🎆🎆🎆🎆🎆

Habib ya takura mishi akan yana musu rowar amarya saboda haka sai ya tsai da ranar da zasu je gaishe su, ta so tirjewa da farko amma ganin ranshi zai baci shiyasa ta yarda. Ranar ta shirya yazo ya dauketa basu tsaya koi'ina ba sai a gidan habib, yayi horn maigadi ya bude yana turo hancin motar ya hango asma'a zaune akan blocks din flower bed sai sharban kuka take kamar ranta zai fita. Zaleeha ta budo kofar ta fito tayi wajenta da sauri tana kiran sunanta, ta dago taga zaleeha ta waro mata hannu tazo dagudu ta dale jikinta har a lokacin tana kan kuka. Ta soma jijjigata tana dan bubuga mata baya alamar tayi shiru kuma me ya sameta, buden bakinta tsakanin kuka tace "aunty ya bata. Zoben da kika bani ya bata a gidan lalle na nema na rasa ban gani ba. Aunty kiyi hakuri wlh ba dagangan na batar dashi ba laifin mummy ne" sai ta sake saka wani kuka, zaleeha tace "shh....... Yi shiru abunki na yafe miki kinji idan ma kinaso irinshi sai muje shagon mai azurfa nasa shi yayi miki irinshi, yanzu daman akan zobe kika diga mun asarar tsadaddun hawayenki? Kin mance big girls dont cry" a hankali ta soma shiru har ta koma ajiyan zuciya . Tare suka kutsa kai cikin falon suka tarar habib ya buga tagumi kawai yana karantar wasikar jaki, umar ya doke tagumin dayayi yace "haba! Yanzu saboda Allah dama kana cikin gidanan ka bar asma'u a waje tanata faman kuka sai kace ta rasa iyayenta?" yayi ajiyar zuciya "to umar me kakeso nayi mata? Sunje kunshi gidan su ne ta cire zoben da wai aka bata akayi mata to ta mance dashi a chan harfa aka kwana dazu ta tashi daga barci a firgice tana lalube tana kiran zobenta ita a samo mata zobenta, kamar wasa amma ta daga mana hankali shine mamanta taje gida ko zata gani ta barni da ita babu lallashin duniyar da banyi ba akan tayi shiru amma ta ki shine na korata waje saboda gudun kada zuciya ya debeni nayi mata dan banzan duka" a nan suka gaisa da zaliiha ya shiga ya samo musu abun motsa baki ganin asma'u tayi shiru shiyasa hankalinshi ya kwanta har suka soma labari a tsakaninsu. Yana tsokanar zaleeha motarta yayi fakin ta sauko suna ji ta kulle kofar asma'u ta mike ta nufi kofa a wajen suka hadu tana fadin "mummy kinga zoben?" ta riko hanunta ta saka mata shi a tafin hanun sanan tace "na huta ko asma'u" ta karaso falon tana faman fadin "yaudai umar ya daure ya kawo mana amarsu ......" sukayi ido hudu da zaleeha ta wangale ido da baki alamar mamaki tana nunata da yatsa "zaleeha? Zaleeha kece?" cikin mamaki itama tace "aunty hajara, kardai kece matar habib" "kwarai kuwa nice, ashe da rabon zamu sake ganin ki? Kin guje mu babu neman duniyar da bamuyi ba dani da maman aziza amma bamu ganki ba har gombe mukaje neman ki amma wai kun dade da barin garin" murmushi kawai tayi ta basar da wadanan jerin tambayoyin ta hanyar tambayan ya yaran suke, ta amsa da lau lau dinsu ta wuce kitchen hada musu abinci. Cikin lokaci kankani ta hado musu dafadukan cous cous da miyan ganye kasancewar tun dama ta tanadi miyanta zaleeha ma ta gagara zaman falon taje ta saka mata hannu suka kammala tare, suna kan jerawa akan center carpet din sukaji dirar mota a gidan. Haka kawai taji zuciyarta yayi saurin harbawa, bata san dalilin faduwar gabanta ba a zuciyarta tanata Allah yasa ba tahir bane. Yayi sallama ya shigo cikin falon, kowanne a cikinsu ya amsa, yana yanayi da Alh tahir saidai shi wanan yafi shi manyanta sanan yafishi haske amma wanan yafishi tsawo da faffadar fuska, ya dinga binsu da ido daya bayan daya har ya sauke kwayar idanunshi akan zaleeha. Ya dade yana kallonta harta tsargu sanan ya natsu, hajara tace "to yaya tunda ma ka zo to ka iso a sa'a, ku taho kawai muci tare" dukkansu suka hallaro kan table din hajara da kanta tayi serving dinsu sanan ta zauna kowa ya soma ci, duk irin rashin jin kunyar cin abincin zaleeha a gaban kowa sai taji tana kunyar mutumin nan shiyasa ta tsakuta kadan ta ajiye chokali tayita faman kurban juice har suka kammala suka dawo falon, ta tayata wanke wanke dukda hajara nata faman cewa ta barwa mai aiki amma taki ji tana mai aiyyana "gwara zaman kitchen akan na falo idon mutumin chan na bina" a ranta. Ta gama sanan tazo ta samesu a falo sunata faman hira tana zama hajara tace "yaya ga zaleehan nan da fatan idanunka sun gasganta maka abubuwan da kunanka suka jiye maka" dukda zaleeha bata san ko me da me aka fada akanta ba amma sai ta soma sha'awar jin menene abun da ake bukatar gasgantawar shi yace "na amince auta domin tun shigowata zuciyata ya bani" yana magana idanunshi akan zaleehan yace "malama zaleeha na dan tambayeki mana" duk tabi ta takura mutuka domin dama ita ba mace mai yawan mingling da mutane bane ta daure tace "ina jinka Allah yasa na sani" "kinma sani domin ba tambaya me wuya bane, dama akan zoben hanun asma'u ne shin ke kika bata?" ta gyada kai" eh nina bata, mahaifiyata ce ta bani shi" ya sake gyara zama "ita din bata fada miki wanda ya bata ba" "ehto, tace mahaifina ne ya bata amma gaskiya rabonmu dashi munyi shekaru ko yana raye oho" hawaye ne ya soma yi mishi zarya a fuskar shi kowa a falon kallo ya dawo kanshi,"lafiya baba?" ya nuna kirjinshi "nine mahaifinki...

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now